NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 96 of 172

nar tana kallan kwandon nasu da bakomai a ciki sai atamfa kwaya daya. Kiran Hassan ne yasa ta kalli Jalila tace "Yaya!" Jalila ta kalleta bayan ta amsa kiran, Ameera tace "Yaya...." Yace "me kukeyi haryanzu? Badai shirme kuka tsaya yi ba?" Tace "a'a Yaya, ni narasa me zamu siya ne, duk abinda na dauko sai Yaya Jalila tace wai yayi tsada sai ta maida." Hassan ya kashe wayarsa baijira ya gama jin abinda zatace ba. Tahowa yai ya shiga ciki, security din ya bishi da kallo yana yan kunkuni, inkasan shigowa zakai gulmar ta menene? Tun dazu ka tsaya kamar mai jira. Hassan na shiga ya sake kiran Ameera ya tambayeta inda suke, ta sanar dashi. Yana isowa ya bugama Jalila kallan harara sannan ya kalli Ameera yace "ina kayan da kika zaba?" Nan ta shiga daukowa tana sawa a cart din, mamaki na kara ratsata, bata dade a gidansu Aina'u ba yaushe har yayanta ya koma haka? Jalila na tsaye tana kallansu sai zuba kaya sukeyi a cart din har sai da ya cika sannan suka nufi gun biyan kudi. Tana can gefe suka biya kudin sannan ya kalleta ya nuna mata ledoji, matsowa tai ta dau leda biyu manya itama Ameera tadau biyu suka nufi kofar fita. Yana kallanta da yanda ledojin suka mata nauyi dan kamar ma janta sukeyi, kallanta ya sakeyi sannan ya kalli ledar ji yake kamar yaje ya amsa sai dai inaaa bayaji zai iya yin hakan, balle agaban Ameera. Taje kusa da motar bata kula da saman interlocks din daya dago ba, jitai tayi tintibe da sauri yasa hannu ya riko cikinta. Ajiyar zuciya tai dan ta tsorata ga kayan da suka kara rinjayarta. Juyowa tai ta kalleshi kawai sai tai dariya tace "yaya wlh na tsorata, har na hango kaina ya bugu da jikin motar." Jawota yai ta mike daidai sannan ya kalli gun datai tuntube, lalai mutanen nan basuda hankali tayaya bazasu gyara gun ba? Fuska a daure ya kalleta yace "meyasa bakya kallan kasa in kina tafiya? Da bana kusa ko da banyi hanzarin kamoki ba me kike tunanin zai faru?" Ta kalleshi jikinta yai sanyi tace "wlh ban......" Gani tai ya wuceta rai a bace, ledar hannunta ya amsa ya sa a boot din motar sannan ya bude ciki ya shiga. Ameera ta ajiye nata itama ta shiga baya sum sum. Jalila ma jiki a sanyaye ta shiga, to laifinta ne? Itama ai da saninta bazata bari ta fadi haka ba. Harya tada motar ya fito daga ciki ya nufi gun secuydin. Kallansa yai fuskar nan a daure, security din ya kalleshi yace "Yallabai da wani abun ne?" Shiru yai yana tunani, menene damuwarka da har kazo nan zakai fada akan su gyara gun da yarinyarcan zata fadi? Menene damuwarka Hassan. Bai tanka mai ba ya juya, security din ya bishi da kallo yace "yau ni kuma ina na samo wannan?"Hassan ya bude motar ya shiga dya rufota da karfi yaja motar da gudu suka bar gun. Shiru motar tai ba wanda yake magana, sai sanyin Ac dake ratsa cikin motar. Jalila ta kalleshi taga ba alamar wargi, tai gum. Can ta sake kallansa nan ma taga ba alama tai gum. Sunyi nisa sosai sai tace "Yaya kashanye yoghurt dinka?" Bai tanka mata ba sai dai yasa hannu ya miko mata ledar, ba haka taso ba, ta daure ta sake cewa "kasan yaya sai da muka shiga cikin store din nan naji cikina yana wani kara?" Nan ma baiko tanka mata ba, ta amshi ledar ta ajiye a kusa da ita sannan ta kalli Ameera datai shiru tana danna wayarta. Itama jan bakinta tai bata sake cewa komai ba. Suna isa gida Ameera ta fito da sauri saboda tsoron kar reshe ya juye da ita. Jalila ta zauna ba alamar fita, kallanta yai yace "me kikeyi?" Tace "Yaya kaima kasan ba kaifina bane, tuntube nai sannan wlh bawai kula bane banayi" Yace "kinji nace wani abun?" Tace "bakace ba amma......" Ya katseta "sauka inkuma bazaki shiga ciki ba sai ki kulle motar inkin gama zaman." Kallansa tai ranta yadan sosu ta fito daga ciki ta duba boot ta dauko ragowar ledojin sannan tai ciki. Kallanta yai harta shiga ciki sannan ya dan saki huci yace " ba saboda ke raina ya baci ba saboda kaina ne." Idanunsa yadan rufe da hannunsa kafin ya fito daga motar. Ummy najin motsin shigowarsu ta fito daga dakinta tana cewa "Jalila kun dawo?" Ameera ce ta taho da gudu ta rungumeta, Ummy tai dariya tace "Auta saukar yaushe?" Ameera ta kalli Jalila tace "tare muke dasu Yaya Jalilah." Ummy ta kalli Jalila wacce ta karaso tana cewa "da ita muka je ai Ummy." Ameera ta kalli Ummy cikin zumudi tace "Ummy kinsan waye ya kaimu?" Ummy ta kalleta, Ameera ta kara matsowa tace "Ummy karkiyi mamaki........." "Hassan kun dawo?" Abinda Ummy tace ne yasa Ameera saurin boyewa abayanta, Hassan yace "eh Ummy." sannan yace "Abba fa?" Ta nunamai falo tana kallan Jalila wacce tana tsaye yazo ya wuce kamar baiganta ba. Hassan ya wuce falo, Ameera ta kalli Ummy da sauri tace "Ummy kingani? Ummy yaya ne yake magana haka." Ummy ta kalleta tace "naji hajiyar magana, akwai baki a dakinki kije ku gaisa." Ameera tace "baki? Su waye?" Ummy bata tanka mata ba ta matso kusa da Jalila tace "Jalila wani abun ya faru ne?" Jalila tai yake tace "bakomai Ummy, Kinga kayan da Yaya ya sai mata." Ummy ta kalli ledar tace "basai kin ciro ba, a
🏠