da hadi da ita?"
Jalila tai murmushi tace "ya kake gani?"
Yace "yanzu muje ki siyo mata kaya, da abinda zata bukata sannan sai ki mata magana akan gidan da zata zauna kiji."
Jalila tai shiru tana kallansa, juyowa yai ya kalleta yace "kallanfa?"
Tace "wani sa'in rasa abin cewa nakeyi."
Yace "kin huce kenan?"
Tace "ai ba fishi nai ba, kaine fa kacemin wai bazakaci ba."
Yace "bazanci ba so kike nace zanci?"
Tace "ba haka nake nufi ba.
"To me kike san ji?"
Shiru tai tare da tambayar kanta, me nake sanji?
Hassan bai kalleta ba ya cigaba da tukinsa.
Can Jalila tace "Yaya nagode sosai harma bansan ta ya zan yi godiya ba, yaushe Ameera zata dawo ne?"
Yace "Ameera batanan?"
Kallan mamaki tamai tace "bangane ba?"
Bai tanka mata ba, ta cigaba "dan Allah bakasan bata gida ba? Ta dade fa batanan."
Nan ma baice komai ba.
Haka suka isa ya zauna a mota yace ta shiga ta siyo kayan, ya mika mata Atm dinsa.
Kallan mamaki tai tace "wai ni kadai zani?"
Yace " badai kina tunanin dani zaki shiga ciki ba?"
Jalila cikin mamaki ta kalleshi tace "Yaya ni wlh tunda nake bantaba zuwa irin wannan gurin ba, sannan bantaba siyo abu ma da Atm ba bare nasan ya akeyi."
Kallanta yai kamar zaiyi magana sai ya fasa.
Kallansa itama tai tadan shagwabe fuska tace "Yaya Please!"
Shiru yai yana kallanta kafin ya bude kofar ya fito, yana fitowa itama ta fito da sauri ta matso inda yake.
Can gefe yaje ya tsaya yana kallanta wai ta gama zaba, tsayawa tai a gun atamfofi tana tunanin wanda zata dauka tare da duba kudin da aka rubuta a jiki.
"Bakya tunanin wannan yafi kyau?" Abinda taji an fada kenan, muryar daga bayanta ta fito.
Da sauri ta juyo, baya tadanyi kadan ganin mutum a bayanta.
Murmushi ya sakar mata yace "Sunana Al-Ameen Abbah."
Dan baya ta sakeyi tace "Malam......."
Ganin Hassan tai a bayanshi, hannu yasa ya dan bugi kafadarsa, mutumin ya juyo rai a bace yace "Malam meye hakan?"
Hassan yace "zaka tafi abinda ya kawoka ne ko kuwa?"
Yace "mene? Kai."
Wani kallo daya bugama Jalila ne yasa tai saurin matsowa kusa dashi, kallanta yai yace "wuce muje." Gani tai ya nufi kofar fita tace "bamusai kayan ba."
Yace "banasan shagon."
Jalila ta bishi fa kallo, tare da binshi mota.
Waya ya dauko ya kira Ameerah.
Yauce rana ta farko data fara ganin kiran yayanta a wayarta, cikin mamaki ta daga tace "Hello."
"Kina ina?"
Tace "Yaya? Ina gidan Aunty Nana."
Yace ki shirya zanzo in daukeki." Mamaki ya kamata bayan ya kashe wayar tabi wayar da kallon mamaki.
Da sauri ta mike ta hau shirya kayanta.
Aina'u tace "Ameera tafiya?"
Tace "eh yaya ne zaizo ya daukeni yanzu."
Aina'u tace "Kice yau akwai zolaya gun Yaya Sageer?"
Tace "Yaya fa ba yaya Sageer ba."
Mamaki ne ya kama Aina'u bata dade da shiryawa ba ya kira wayarta yace ta fito yana waje."
Aina'u tace "Ameera tafiya zakiyi ga Mamana batanan?" Tace "inta dawo kya fada mata." Cikin hanzari tai waje.
Mamaki ne ya kama Aina'u ta biyota waje dan tabbatar ma idanta, aikuwa shine a zaune matarsa na gefensa.
Aina'u kishi da takaici ya kamata ko fita daga gate din batai ba ta koma ciki ta fada gado tana hawaye, itafa ya kamata ta zauna a kusa da Hassan ba wannan yarinyar ba.
Ameera ta shiga baya bakinta yaki rufuwa, yauce rana ta farko da yayanta zai fita da ita guri a motarsa.
Jalila sai murna take taga Ameera tana ta neman jan ta da hira, Hassan yai gyaran murya sannan yace "maganar ta isa, inkunje gida kwayi."
Jalila tai gum da bakinta.
A kofar wani store ya ajiye su ya kalli Ameera yace "Ameera kuje tare kaya za'a siyoma mahaifiyarta, sannan ya mika mata Atm dinsa."
Tace to yaya, ta fita.
Jalila na neman fita ya riko hannunta, juyowa tai ta kalleshi yace "yanzun ma inkin je ki kara bari wani katan ya miki magana."
Tace "wancan din ma ni na bari? Sannan bafa komai yace min ba cemin kawai yai wannan yafi......."
Wani kallo ya maka mata, ya rufe bakinta tace "to."
Ya saketa ta fita.
Da kallo ya bita har ta shiga cikin shagon na Jifatu.
Meke damunshi? Meke damunshi????
Abinda yaketa tambayar kansa kenan.....
#OneLuv๐
[12/7, 9:51 PM] El-hajj: ๐ฏ *JALILAH* ๐ฏ
Written By : *AYUSHER MUHD*
โ๏ธote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_๐ก)
*47*
Hankalinsa ya kasa kwanciya, fitowa yai daga motar tare da dan matsowa kadan da kofar shiga yadan leka ciki kadan.
Security din dake gun ne ya kalleshi yace "Yallabai shiga zakai?"
Hade rai yai ya juya jikin motarsa, hannayensa ya hada yana dan hadasu da waresu, kafin ya koma cikin mota ya dauko wayarsa.
Mintinsu sha biyar kenan da shiga, me sukeyi haryanzu? Ko alert bai gani ba bare yasa ran sun biya.
Wayarsa ya dauko ya danna number Ameera.
Sukuwa suna ciki Jalila kome Ameera ta dauko indai taga kudi sai ta maidashi, Ameera ta tsaya tace "to nidai bansan me kikeso mu siya ba, duk abinda na dauko sai ki maida." Ta karasa maga