ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 91 of 172

yana cewa "In bazata biyoki ba sai ki dawo kindai san ran monday zaku koma makaranta." Jalila ta wuce ta hau sama, a hankali tasa hannu tadan murda kofar, tadan fara kokarin budewa a hankali. Jitai an jawo kofar da karfi har ya hado da ita data rike kofar, ta taho ciki da dan gudu ga tire a hannunta. Da sauri ya rike tiren yana kallanta. Daidaita tsayuwarta tai sannan tace "yaya irin wannan fizgar kofar fa?" Yace "ke kuma irin wannan bude kofar fa? Kamar wata munafuka? Ko laifi kikai?"yai maganar da alamar tuhuma. Da sauri ta ajiye abin hannunta tace "laifin me? Ni wlh ba laifin danai." Baisan yanzu ma bakinsa yadan motsa ba yace " kin tabbatar?" Ya fada tare da matsowa. Da sauri tai baya tana cewa "ni wlh banyi komai ba, kawai dan na murdo kofa a hankali." Yadan kalli idanunta yace "why do i have this kind of feeling?" Tace "ikon Allah, dama dai fada kakesan yi, daga shigowata?" Ya zauna akan gado yana cewa " ramawa nai." Tace "me nai da zaka rama?" Bai tanka taba ya dau littafinsa tare da gyara zama, ido ta kuramai a ranta tace "so? Hahh lalai Ummy wannan mutumin nan?" Bai kalleta ba yace "kallan fa?" Ta dauke idanta da sauri tace "sauko kaci abinci." Yace "banaci." Tace "bakaci jiya da daddare fa?" Yace "shiyasa ai bazanci yanzun ba." Tace "ban gane ba???" Ya shareta. Ta matso tana neman amsar littafinta, wani kallo ya mata yace "littafin kike san amsa ko rikeni kike sanyi?" Da sauri ta matsa baya tace "rike ka kamar ya?" Yace "kamar yanda kika saba." Mamaki ne ya kamata tace "kaima ai kana rike ni." Wai meke damun mutan nan? Jiya da daddare kamar bashi ba. Kallanta yai kamar bazai yi magana ba sai jitai yace "inma na rikeki ai ke matatace." Mamaki me ya kamata ta saki baki tana kallan ikon Allah, shikuwa kamar baiyi maganar ba ya cigaba da karatunsa. Tace "dan Allah ka sauko kaci abinci." Yace "Allah bazan ci ba." Tace "bangane hakan ba." Mikewa ma taga yayi ya ajiye littafib ya nufi toilet, mamaki ne ya kamata ta bishi da kallo. Haryaje zai shiga toilet sai taji yace "inkin gama ki shirya muje a siyoma Goggo kayan dakinta da abin bukata." Ya shiga ciki yana cewa jiya dana jira kizo muci ai shareni kikai kema kiji ko da dadi...... Duk da taji dadin abinda yace sai dai wulakancin daya mata yasa tama rasa abinyi. Da kyar tasha ruwan tea, duk kuwa da tanajin yunwa amma takaici ya hanata, wai Allah bazanci ba, kalmar nan ta bata haushi. Tana nan a zaune ya fito daga wanka daure da towel, da sauri ta juya baya. Ko kallan inda take baiyi ba ya fara shiryawa. Yana gamawa ya dau key yace "ina jiranki a mota."yai waje. Da kallo ta bishi tai tunanin jiya bayan ya warke, kamar ba shiba yana mata magana a hankali, to yanzu me ya sameshi kuma? Ramawa? Me tamai? Haka ta mike tai wanka duk ranta ba dadi, ta fito tana kokarin sa bra a saman towel din jikinta ya turo kofar. Idanunsa ne ya sauka a kanta, zaro ido tai tana kallansa, da sauri tasa hannu ta rufe kirjinta. Ganinsa tai ha fara matsowa inda take, idanu ta runtse tana tsoron abinda zai biyo baya, sai dayazo daf da ita har tana jiyo numfashinsa yasa hannu cikin wardrobe ya dauko abu, kallanta yai yace "Wallet." Ya fada tare da nuna mata wallet din, ya juya ya futa. Wani nanauyan numfashi ta saki........ #OneLuv๐Ÿ’• ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* โœ”ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *46* Hassan na saukowa kasa ya nufi hanyar fita da sauri "Hassan!" Juyowa yai da sauri kamar mara gaskiya ya kalleta. Karasowa yai inda take sannan ya gaisheta, fuskarta dauke da murmushi tace "fita zakai?" Yace "eh ni da...." sai kuma yai shiru, murmushi ta sakeyi tace "ya zaka fita baka gaida sirikarka ba?" Yace "sirika?" Nunamai dakin Ameera tai da hannu, Hassan ya kalleta alamar rashin fahimta, tace "badai bazaka ba?" Kallan dakin ya kuma yi sannan taga ya nufi dakin, da kallo ta bishi cikin jin dadi. Hassan ya kwankwasa kofar dakin, daga ciki Lantana ta mike ta bude. Tsayawa yai yana tunanin me ma zaice inya shiga? Goggo dake zaune a kasan carpet tana ganin shine ta mike tace "Hassan? Shigo mana." Shigowa yai ya zauna daga gefe yace "Ina kwana?" Kansa na kasa. Goggo tace "ka tashi lafiya? Ya dawainiya da mu?" Hassan yai shiru dan bai san me zaice ba, Goggo tadanyi shiru haryana shirin mikewa. Tace "Hassan." Komawa yai ya zauna tare da kallanta, Goggo tace "in ba damuwa magana nakeso muyi." Yace " ba komai, menene?" Tadanyi shiru kafin tace "da farko dai nasan kafi karfin Jalila, saboda ita ba gata gareta ba, ba kudi gareta ba sannan ba 'yan uwa dake santa take dashi ba, yarinyar tasha wahala agidan mahaifinta wanda har bata iya cewa ko kawo kawarta da sunan gidansu, tunda nake da ita bata taba kawo kawa ba, bata taba zuwa gidan kawa ba, nasan bawai dan batada shi bane
๐Ÿ