NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 90 of 172

zamuyi, inyaso company din nasu ya nukushe." Tace "ayi haka kuwa?" Yace " baki kula da rainin hankalin da suka mana ba? Sannan yarinyar nan da mahaifiyarta, gaba daya ba tausayi a harkarsu, Hajiya taban mamaki duk da nasan macece wace kanta yake a waye amma i didn't expect that from her." Tace "na sani sai dai in muka duba abin ta wata fuska zamuga mu taimakonmu sukai, da farko dabadan sun yaudaremu ba da bamu san wacce zamu aurana Hassan ba, in muka duba saukin da muka dade muna nema akansa yanzu gashi abinda likitoci da dama suka kasa yi yarinyarnan a ciki wata daya ta mana, duk da bawai ya warke ne ba sai dai canjin daya samu nada yawa." Abba yai shiru yana kallanta zuciyarshi na dana sanin abinda ya aikata mata, yace "yanzu me kike tunani?" Tace "just live them." Yace "kina nufin duk abinda sukai ya tashi a banza?" Tace "ko daya sai dai ina tunanin mu barma Allah, yanda suka cutar da Jalila da mahaifiyarta Allah bazai barsu ba, mu murikesu, gatan da basu samu ba mu basu, mu jira hukunci Allah akan su." Abba yai shiru sai kallanta kawai da yakeyi, tace "kallan fa? Shawarar batai ba?" Yace "akoda yaushe in kina abu sai na dinga yin wani tunani, sau dayawa akance mata basukai maza zurfin tunani ba, sannan sai kaji namiji na ta aibata mace, in naji haka a koda yaushe sai insan Allah yamin baiwar da ba ko wani namiji yama ba, samunki a matsayin matata yana daya daga cikin abubuwan da nake alfahari dasu a rayuwata." Kallansa tai sannan tai murmushi tace " Kasan abinda yaban mamaki? Ban taba tunanin Hassan zai sauko kasa ba wlh, kasan kawai nama Jalila zancen ne amma a raina nasan bamai yiwuwa bane?" Abba ya kalli yanda taketa farinciki yace "ni kaina nayi mamaki, kinsan rabon da Hassan ya shigo falona kuwa harya zauna ya dade haka?" Tace " kasan ya sauko ya gaida baban Jalila ran nan?" Abba yai murmushi yace "da alama yanda nai dace da mata haka Hassan yai dace, sai muyi addu'a Allah yaba Sageer mace shima ta gari." Tace "insha Allah." Washegari. Dakin Sageer ta nufa tasa hannu tai knocking. Yana kwance akan gado ya taso ya bude mata. Kallansa tai cikin kulawa tace "Sageer lafiya? Naga baka fito ba." Ya kalleta yace "Ummy...." A rikice ta kalleshi tace "menene? Bakajin dadi ne?" Yace "a'a kawai dai..." Tace "na kula ma gaba daya yanzu kadan canza, Sageer menene ke faruwa?" Yace "kai Ummy wacce canzawa?" Tura kofar tai ta shiga dakin, binta yai ciki da sauri yana cewa "Ummy." Hannu tasa ta zuge labulen dakin ta zauna akan kujera. Ya matso yana cewa "Ummy!!!" Cikin shagwaba ya kirata, ta harareshi tare da hard'e hannayenta tace " In baka fadaminba ba inda zani." Dariya ya saka sannan ya zauna a kasa kusa da ita yace "shikenan sai muyi hira." Tace "Sageer dan Allah meke damunka? Sai yanzu na fahimta sam da yake banda nutsuwa ban kula da canzawar dakai ba." Yace "Ummy wlh ba komai, muje na tayaki aikin kitchen kafin sirikarki ta sauko." Kallansa tai sannan tai murmushi ta mike ta fito, yabiyo ta. Dakin Ameera ta kalla tace "bari in nakai musu breakfast sai mu gaisa." Shima dakin ya kalla sannan ya matso yace "Ummy me kukai da Abba akan su?" Tace "Goggonta zata zauna anan kamar yanda Hassan yace, su kuma su suka sani." Sageer yai murmushi zaiyi magana ya hangota a kitchen. Tsayawa yai yana kallanta, Jalila ta juyo jin motsin mutane, kallan Ummy tai sannan ta matso fuskarta dauke da fara'a tace "Ummy ina kwana?" Ummu ta kalleta cikin jin dadi tace "Jalila kin tashi lafiya?" Tace "lafiya kalau Ummy." Sannan tadan kalli Sageer a hankali tace "Ina kwana?" Sageer yace "kin tashi lafiya?ya yaya?" Lafiya kawai tace. Ummy tace "Jalila naji dadin ganinki haka kamar ba abinda ya faru." Jalila tai kasa dakai tana murmushi, a zahiri itakam ganin Goggonta yasa takejin kamar duk wani abu daga baya kenan, sannan ta rasa me yasa takejinta haka. Sageer ya zauna a falo su kuma suka nufi kitchen, suna aiki suna yar hira, Ummy tace "Hassan abin nashi na tashi sosai yanzu?" Jalila tace "ba sosai ba sai yai kwana biyu zuwa uku lafiya." Ummy tai murmushin jin dadi ta kalli kular data suko dashi ta bude, kallan Jalila tai tace "jiya bakuci abinci bane?" Tace "yayane baici ba, inaji bacci ne ya daukeshi." Ummy tace "ba matsala tunda ya fara bude zuciyarsa nasan komai zai daidaita a hankali." Jalila ta kalleta cikin rashin fahimta tace "bude zuciya?" Ummy ta dauko kukar tana cewa " eh mana akanki ba." Jalila tace "ni?" Ta fada cikin mamaki da alamar tambaya, Ummy bata tanka mata ba ta cigaba da aiki. Jalila tai shiru tana nazarin abinda Ummy ke nufi, ba dai so take tace wai Hassan ya fara santa ba? Tab shi wannan har akwai zuciyar soyayya ma a ransa?lalai Ummy. Haka suka gama ta kaima Goggo ya zauna suka gaisa da dan hira, Ummy na shigowa ta mike ta dawo kitchen ta dau nasu. Sageer na zaune kan dinning shi kadai yana cin abinci, waya yakeyi da alama da Ameera yake waya dan
🏠