ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 86 of 172

Goggo ta kalleta tace " kin gama gudun?" Jalila tace "gudun me?" Goggo ta tureta daga kafadarta tace "kindauka bansan guduna kike ba? Kar na miki tambayoyi? Shiyasa tunda kika fita kikaki shigowa?" Jalila ta tuntsire da dariya tace "ni? Wlh ba haka bane aiki mukeyi ne bakiga Lantana ma batanan ba?" Goggo tace "ba wani." Jalila fa kara kwanciya a kafadarta tace " Ummy tace inkaiki falon Abba, anan zakiji komai." Tace "kaini dan ni kaina so nake naji." Nan suka fita tare, sai data kusa kaita falon, suna tafe tare sai ga Ummy tace " Jalila barta zamu shiga tare." Ta matso kusa da kunnenta tace "ki je ki lalabo mijinki." Jalila ta kalleta, Ummy tai murmushi sannan ta nuna mata sama da kanta. Jalila ta kalli saman sannan ta nufi matatakalar, anya zai fito kuwa? Gashi bashida lafiya. Kofar dakin ta tura ta shiga, yana kan sallaya yana karatun kur'ani. Zama tai a bakin gado tana jiransa, bai dade ba yakai ayar karshe ta cikin suratul maryam, yana neman dauko wata surar ne dan izu daya yake yi a duk tsakanin sallar magrib da isha'i tai saurin cewa "Yaya!" Tsayawa yai bai fara wata surarba sannan bai juyo ya kalleta ba, tace "Yaya za'ayi maganar." Ya juyo yace "magana?" Ta kalleshi tace "maganar nan.... ba Abba yace sai anjima ba?" Yace "and so?" Tace "shine za'ayi yanzu ka sauko." Yace "in me?" Tace "ka sauko, muje tare." Yace "kinsan me kike cewa? Nine zan sauko inje inda kowa zai zauna ayi magana?" Kallansa tai tai raurau da ido, yace "ki tashi kije, ni ba nayi nawa part din ba? Saurab ya rage naki." Haryanzu kallansa take da idanun kafin tace "Yaya Please" Juyawa yai ya bude kur'ani zai dora daga inda ya tsaya. Da sauri ta sauko ta bayansa ta rike gefen rigarsa ta kafadarsa. Juyowa yai yace "wai........" Bata jira me zaice ba tace " yaya dan Allah ka taimaken, ba wai wani abu zakace ba, inka zauna agun ma ya isa." Yace "in zauna?" Tsugunawa tai ta gefensa tace "Dan Allah yaya." Hade rai yai ya juya, tace "kan ne?" Ya mata shiru, tace "yahkuri yaya, na sani ina takura maka, sannan ina takura maka da neman yin depending akanka akan komai na rayuwata, kayi hakuri nasan bana kyautawa." Ta mike tai waje, a falo ta tsaya tai ajiyar zuciya sannan tace " who do u think u are?" A hankali ta fara sauka daga matatakar, jiki a sanyaye. A falo kuwa Abba da Ummy na zaune daga bangare daya, Goggo na dayan bangaren Jalila ta shigo. Tana shigowa Sageer ya shigo, tunda ya shigo Goggo ke kallansa, inata san fuskar nan? Abba ne ya katseta da cewa "yaki saukowa?" Ta daga kai alamar eh. Jiki a sanyaye ta zauna a kasa kusa da Goggo. Sageer ya zauna a kasa kusa da Abba. Falon ya dan yi shiru kafin Abba yai gyaran murya yace "Sannu da zuwa mahaifiyar Jalila, muna baki hakuri akan abinda ya faru wanda mu kanmu bamusan takamaimai abinda ke faruwa ba, sai dai ina neman sanin dalilin dayasa ba wanda yasan da zamanki a gidan, sannan dalilin dayasa aka munafircemu mu dake akan auran nan, Jalila yar muce a yanzu shiyasa nake san sanin menene ke faruwa takamaimai." Goggo tace "nagode da karamawa, sai dai a yanda nasan mutanen nan ba damuwa sukai damu ba ina mamakin yanda akai suka kawo Jalila cikin gidan karamci irin wannan." Abba yai murmushi yace "mun gode da karamawa, Jalila inaso ki sanar damu abinda ke faruwa." Jalila ta kalli Abba, ta kalli Ummy sannan ta kalli Sageer. Ummy tace "duk wani abunda kika sani muke sanji, wannan shikadai ne abinda zaisa musan abinda ya dace muyi, kada ki munafurcemu, kada ki munafirci mahaifiyarki." Jalila ta kalli Goggo. Turo kofar da akai ne yasa suka kalli kofar, Hassan ne ya shigo. Kallan Jalila yai wacce itama kallansa takeyi, a hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta wanda yana ganin haka ya dauke kansa daga kallanta sannan ya nufi can gefe ya zauna akan kujera shi kadai. Goggonta kalleshi, wannan shine na dazu...... ******** Inna ce ta kalli Dady tace "take all the blame." Kallanta yai cikin mamaki yace "ban gane ba?" Tace "kace kaine kai komai, dama matarka ce da yarka, kaga kome kai dama kaine me hakki akansu, wannan shikadaine hanyar dazamu kwaci company dinmu." Dady yace "ni na kasa fahimta, kenan nine na shirya duk abinda ke faruwa?" Tace "eh ko dama nice na shirya? Ina naga matsayi? Matar data tsufa???? Dady yamata wani kallan tsantsan mamaki........ #OneLuv๐Ÿ’• ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* โœ”ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *44* Jalila tai ajiyar zuciya sannan ta kalli Goggo tace "sanda na sameki a bangaren su Dady akwance ba lafiya........................." Haka ta kwashe komai ta sanar dasu, gaba daya falon yayi tsiy saboda tsananin tausayin abinda kunnuwansu yakeji, Hassan na zaune ya kwantar da kansa a saman kujera, idanuwansa na lumshe kai kafe bai san me ake cewa a falon ba, sai da
๐Ÿ