NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 84 of 172

yai sannan ya mike zaune ya fizgi ruwan hannunta ya mikamata dayan hannun ta. Zubamai maganin tana dariya. Sha yai sannan ya kwanta. ********** Ummy na shiga falon Abba ya kalleta yace “meke faruwa? Nifa na kasa gane abinda ke faruwa.” Tace “ni kaina bansani ba sai dai na tabbatar Hassan yasan me yakeyi, kafi kowa sanin halinsa a da can inyai abu ma to akwai dalili, daga baya kuma da matsala ta faru gaba daya ma yadaina shiga rayuwar kowa inba tasa ba, kaga yanzu dayai abin nan kasan zuciyata dadi takeji dan na fara ganin Hassan dina na da na shirin dawowa.” Abba yai murmushi yace “na fahimta sannan nasan wanene Hassan, sannan ni koma menene ya faru ba wani abun dan ni dama ita na gani sannan ni ita na zaba, ko da a lokacin zasu nunamin wata ba lalai zuciyata ta amince da ita ba.” Ummy tai murmushi itama tace “ maybe suna tunanin sun cuceta ne da alama sunyi bincike akan Hassan..........” Karar wayar hannunta ne yasa ta kalleshi, kashe kiran tai sannan ta kalleshi, yace “ Sim dina na wayarki ne?” Tace “eh, da na cire sai kuma nai tunani kar san zuciyata yasa wasu dasuke nemanka ko na taimako ko na aiki suyi ta nemanka, shiyasa nasa Sim din a wayata.” Shiru yai tare da maida kansa gefe can yace “Kiyi hakuri.” Tace “ kadaina fadar haka, kaddara ce ta zo mana, sai dai mu roki Allah akan ya taimakemu yasa mu wuce kaddarar nan.” Abba yai shiru bai sake cewa komai ba...... ********* A can gidan Inna kuwa, Dady cikin takaici ya dawo gida, bakin cikinsa ko waya bai fita da itaba bare yasa a zo a daukeshi, rabansa da taxi haryamanta amma haka yahau ransa a bace. Yana isa gida ya wuce daki cikin zafin rai, Mumy dake kitchen tana bada umarnin abincin da za’ai ta taho da sauri ta shiga ciki. A tsaye ta ganshi tace “Abban Yasmeen lafiya?” Juyowa yai rai a bace yace “ kinsan yaran nan......” sai kuma yai kwafa. Ta matso da sauri tace “ya kukai? Yadauke Goggon Jalilan?” Yace “ya dauketa mana, yaran nan yana abu kamar shine gaba dani, kinga yanda yake wulakantani, amatsayina na uban matarsa?” Mumy tai shiru can tace “nikaina yaran nan yaban tsoro, wai garin yaya kukaba Jalila yaran nan? Bakusanshi ba? Na dauka kunyi bincike.” Cikin masifa yace “bincike? Abinda Inna ke bada umarni mu ina mukaga ta cewa?” Mumy tai tsaki tace “ai gashi nan ta ja mana masifa, ita kanta yanzu abun ya dameta, gashinan abinda take tunanin samu ma ba samu zatai ba, wanda take dashi ma yana neman wargajewa.” Dady yace “wai yaran nan ni zai kalla yacemin wai inada kudi a jikin? Sannan ya mikon wai 1000 wai na hau mota shi bazai kaini ba?” Mumy tace “mene?” Yai kwafa cikin takaici yace “ni nama rasa ma me zance, kamar ni????” Mumy ta rungumeshi tace “cool down Dadyn Yasmeen, zamu san mafita, bari Mu sanar ma Inna.” Yai tsaki cikin takaici, tace “Safeena ta kira, ta isa Paris lafiya.” Yace “Wai paris taje dama?” Tace “eh can Inna tasa a nemar mata skul.” Yai shiru baice komai ba.... Inna gaba daya tunda Hassan ya fita ta kasa tsaye t kasa zaune gaba daya ta kasa samo mafita, cikin takaici ta kira Sani tacimai mutunci akan kin yimata binciken daya kamata akan Hassan kawai yacemata bashida lafiya alhalin bai bincika wani irin ciwo na kwakwalwa yake ba.... ************ Kuka Zaliha take sosai tana cema Yayarta ita wlh kome zata yi tayi amma itafa kawai ta aura mata Taura in ba haka ba wlh barin gidan zatai ta shiga duniya... Hankalin yayarta ya tashi tace “ kar ta damu dan dole zata koma Niger.” #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *43* Inna tana zaune tananin mafita Mumy ta banko kofa da sauri, Inna ta kalleta tace "naga sanda hankali zai ratsaki ki daina buga kofa haka, yarki ta kai a mata aure amma haryanzu inkina wani abu kamar karamar yarinya." Mumy ta zauna da sauri tace "ni Inna ki bar fadanki zuwa anjima yanzu akwai matsala." Gaban Inna ne ya fadi ta kalleta tace "Abakar ya dawone?" "Ya dawo sai dai yaran ya dauke Goggo" Inna tai shiru hankalinta ya tashi, ta kalli Mumy tace "yanzu kenan da alama sunsan komai ko?" Mumy tace "me zai hana? Shiyasa Inna ni dama na kasa gane dalilinki na......." Wani kallo data mata ne yasata yin shiru, Inna tace "kinsan menene yake bakantamin rai?" Bata jira amsartaba tace " rashin wayau da auna tunaninki, daga ni har mahaifinki munada saurin tunani da kwakwalwa amma ke ni bansan ina kika dauko ba, da farko kince yaran ubanki zaki aura yaran da ko A bai sani ba lokacin, dole da ganin bamuda wani da bayan ke yasa muka jure, sannan kikasan wannan yaran ya munafirceki ashe har aure gareshi, amma tsabar rashin kwakwalwa kika dage ke sai shi, sannan abin bakin ciki duk yanda nai dake akan kiyi aiki a company din da muka gina nida m
🏠