NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 83 of 172

kacin.” Goggo kallanta kawai take tana mamakin yanda mace mai kudi, mai aji, mai kyau haka take magana cikin sanyi da nutsuwa, da alama Matarnan macece mai tsananin imani, da kaunar jama’a da sanin darajarsu. Kasa musama Ummy tai ta daga mata kai alamar fahimta, Ummy tace “nagode, ga toilet nan in zakuyi amfani dashi.” Ta fada tana kallan Lantana. Goggo tace “Angode.” Ummy tai waje ta turo kofar. A waje taga Jalila a tsaye, murmushi ta mata tace “me kike anan?” Jalila ta kalleta da idanunta da sukai raurau tace “Ummy kiyi hakuri, sannan nagode....” Ummy tai murmushi tace “wanda zakima godiya daban bani bace.” Sannan ki barta ta huta zuwa anjima, amma meke damunta?” Tace “hawan jini da diabetes.” Ummy ta kalli kofar dakin cikin tausayawa sannan tace “shikenan mu barta ta huta.” Jalila ta daga kai alamar to sannan tai hanyar sama. Hannu tasa tana neman bude kofar dakin, tsayawa tai tana rike da hannun kofar amma bata bude ba, tana tunanin abinda zata cemai, da wani bakin zata fara mai godiya? A hankali tai ajiyar zuciya sannan ta tura kofar, a kwance ta ganshi kamar mai bacci, kusa dashi taje ta tsugunna tana kallansa, hawaye ne yazobo mata wanda batasan ya diga akan kuncinsa ba, a hankali ya bude idanunsa. Kallanta yai tana share hawayenta, a hankali ya ke magana yace “Menene? Wani abun ya faru ne?” Hawayenta ta karasa gogewa da sauri sannan ta girgiza kai tace “bakomai.” Yace “and why?” Tace “bansan me zance maka bane, kawai sai naji hawaye....” Idanunsa ya lumshe kansa na sarawa yace “ it looks like it’s ur hobby.” Tace “kukan?” Ya lumshe ido kawai, kallansa tai sannan tace “bakajin dadi ne?” Bai tanka ba sannan bai bude ido ba, hannunta tasa a kansa wanda ke mai ciwo kamar zai tsage, jin zafi rau akan tai, da sauri ta kai hannu wuyansa, nan ma zafi a rikice tace “Yaya bakada lafiya, zazzabi ne a jikinka, jikinka zafi.” A hankali ya bude idanu yace “why? Are u worried about me?” Da sauri tace “sosai ma, ka tashi muje asibiti.” Ta fada tare da mikewa tana kokarin dagashi, hannu tasa ta riko hannunsa tana neman dagashi. Jawo hannunta yai, ta fada jikinsa, shiru ne ya ratsa dakin, ita kuma zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, a hankali ta kalleshi, idanuwansa a rufe suke, sai cewa yai “ sai yaushe za’a daga ni?” Ta kalleshi ta kalli kanta data danneshi, neman dagawa tai sai taji hannunsa na rike da ita gam. Tace “to ai.....” Idanu ya bude a hankali ya kalleta, a hankali tai kasa da idanunta. Saketa yai ta mike ta zauna a gun, bata tashi ba tace “Yaya dan Allah muje asibiti.” Yace “bana zuwa asibiti, sannan ni nasan jikina kawai nayi abinda bansaba bane shiyasa, karki damu.” Idanu ta kuramai bayan ya maida idanunsa ya rufe, a hankali tana kallansa tace “Yaya nagode, ban taba tunanin wannan ranar ba.” Bai tanka mata ba, idanunta ne suka ciciko tace “Kayi hakuri Yaya nagode sosai har bansan ta ina zan fara ba.” Yace “hakurin me?” A ranta tace “da na dauka kai mutum ne mara tausayi da mutunci.” A fili tace “for everything.” Idanunsa ya bude a hankali sannan ya kalleta, itama kallansa takeyi, sai dai da sauri ta maida idanunta gefe. Yana kallanta yace “ya zakiyi?” Tace “name?” Idanunsa na kanta tana kallansa taga ita yake kallo ta dauke idanta da sauri, yace “ya zakiyi insu Ummy sun tambayeki?” Tace “ bansan ya zanyi ba, wata zuciyar na sanar dani in fadi komai, wata kuma na tunanin abinda zai faru da Dady dan na tabbatar Inna bazata barshi ba.” Kamar bazaiyi magana ba, dan harta mike zata nemomai maganin zazzabi ragowar tata wanda takaima Ummy taji muryarsa yace “ kiyi abinda ya kwanta miki a rai.” Juyowa tai ta kalleshi tace “In na tuno abinda yama Goggo tundaga haduwarsu zuwa yanzu, sai naji kome zai sameshi bazan damu ba sai dai bansan meke damuna ba, I wish nima inada dauriyar zuciya ko rabin taka ce.” Alama yamata da hannu akan ta matso, matsowa tai gunsa, ya mata alama data kara matsowa, nan ma ta matso takai kunnenta saitin bakinsa, a hankali yace “in fada miki sirrin?” Kai ta daga da sauri, yace “kisa Goggonki a saman komai.” Abinda ya fada kenan yai shiru tare da juya mata baya ya rufe idanunsa, tsayawa tai tana kallansa me yake nufi? Tace “yaya!” Shiru yai baice komai ba, itama shiru tai tana tunanin me yake nufi. Ta dade a tsaye kafin ta daukon mai maganin, ta dauko ruwa a karamin fridge din dake dakin, tazo kusa dashi tace “Yaya tashi kasha magani.” Bai bude idanunsa ba, ganin bashi da alama ne yasa ne ta kara cewa “Yaya Please, ko in fadama Ummy?” Idanunsa ya bude yace “wato kina neman kiyi amfani da weakness dina ko?” Dariya tai tace “ inkaki tashi yanzu sai na sanarma Ummy.” Yace “eh lalai kinga gadon bacci na...” Ta kuntse dariyarta tana nunamai gadan da yake kwance akai, harararta
🏠