miki bayani, zaifi cancanta ta miki bayani da kanta.”
Goggo tai shiru tana addu’a aranta, Allah yasa Jalila ba wani mugun abu ta fada ba, sai dai kallan Hassan yasa wannan ya tafi daga ranta.
Kallan tangamemen gate din da aka bude yasa Goggo ta kara cewa “tana cikin nan?”
Yace “eh.”
Kallan gida take har yai parking, da gudu Jalila wacce ke tsaye a waje ta taho bude kofar inda Goggo take a zaune.
Kallanta Goggo tai sannan ta kalli gidan zatai magana Jalila ta rungumeta ta saki wani irin kuka.
Hassan ya juyo ya kalleta, me yasa ta fita kuka ne? Shifa bayasan kukan nan.
Kallanta yai yace “ kuka zaki tsaya yi ba zaki taimaka mata ku shiga ciki ba?”
Ta share hawayenta tana cewa “Goggo muje.”
Hassan ya fito ya wuce ciki bai jira su ba, a falo ya taradda Ummy da alama fitowarta kenan, kusa da ita yaje yace “Ummy ina Abba?”
Tace “yana falon sa.”
Yace “Ummy muje akwai maganar da zamuyi.”
Kallansa tai cikin jin dadi tace “da alama Hassan dina yanzu bakinsa na kokarin yin magana akai akai.”
Hassan ya juya ya kwankwasama Sageer kofa ya fito, yace “muje.”
Nan suka shiga kofar falon Abba.
Yana zaune rike da qur’ani dan suna shigowa Ummy ta dauko ta mikamai itakuma da bata sallah tadau littafin addu’oi.
Shigowar su ne yasa ya kai aya sannan ya ajiye ya kallesu.
Zama sukai Abba yace “lafiya?”
Ummy tace “Hassan ne zaiyi magana.”
Abba ya kalleshi yace “Hassan!”
Zama yai sannan ya dansa hannunsa na haggu akansa dake ciwo yace “tare nake da bakuwa.”
A tare sukace “bakuwa?”
Hassan yace “eh, tunani nake boys quarters din mu zansa a gyara sai na maida ita can.”
Abba yace “naji ba wai wannan bace maganar, wacece bakuwar? Itace tambayarmu.”
Hassan yace “mahaifiyar Jalila.”
Abba cikin mamaki yace “me kake nufi? Taya zaka dauko mata a gidan mijinta da arzikinta da komai ka kawota boys quaters?””
Hassan yace “bansan ta ina zan fara bayani ba, sai dai ita zatayima Ummy kudan bata lokaci kadan, abu daya zan iya fada, wacce kuka sani a matsayin mahaifiyarta ba ita ta haifeta ba, ban kyauta ba na kawota ba da saninku ba sai dai wannan ne kadai solution din da yazomin”
Ya mike saboda kansa dake ciwo ya fita.
Abba yace “meke faruwa takamaimai? Ni na kasa ganewa.”
Ummy ta dafashi tace “ mu jira kamar yanda yace, na tabbatar yana da dalilinsa, kasan Hassan mutum ne da baya shiga abin mutane, tunda kaga ya shiga wannan i am sure da dalili.”
Sageer ta kalla wanda yai shiru yana tunani, tace Sageer taimaka muje mu shigo da ita, sai mu sata a dakin Ameera inyaso gobe sai a gyara can din.”
Nan suka mike suka fita.
A waje sukaga Goggo ta tsaya tana cema Jalila, “nifa bazan shiga ba sai naji inane nan.”
Jalila ta daure tace “ Goggo dan Allah mu shiga wlh zan fada miki.”
Goggo tace “Jalila.”
Jalila ta rike hannayenta tace “ Goggo gidansu mijinane.”
Goggo tace “me? Miji? Miji kamar ya?”
Sageer har zai fita ya tuna Goggo fa ta ganshi ta kuka san sunanshi, kallan Ummy yai yace “Ummy bari na dan shiga toilet it’s urgent.”
Dariya tai tace “to a fito lafiya.”
Ya juya da sauri, yana cewa gwara mu mata bayani kafin ta fada cikin mutane.
Ummy tana turo kofar taji Goggo na cewa “Jalila aure kamar ya? Aure bansani ba? Auran dole aka miki?”
Cikin mamaki Ummy a karasa tace “meke faruwa? Bangane aure mahaifiyarki bata sani ba, meke faruwa Jalila?”
Jalila ta kalli Ummy idanunta fal tace “Ummy.”
Ummy ta kalli Goggo sannan ta kalli kafarta dake ciwo, tace “muje ciki sai muyi maganar a nutse.
Goggo bata musa ma Ummy ba suka shiga ciki.
#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯
Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_💡)
_Should i start with sending my special greetings? Special greetings to u all my fans, thanks alot for the love and support, a sincere thanks to you all from the bottom of my heart 💕Luv u all._
*42*
Ummy ta zauna akan gadon kusa da Goggo akwai abubuwan da takesan ji, sai dai ta tabbatar matarnan ba lafiya ce ta isheta ba, dan ga kafartanan.
Kallan Goggo tai tace “ki kwanta ki huta dan Allah karkiyi tunanin komai har sai hankalinki ya kwanta.”
Goggo ta kalli Ummy tace “Hajiya ta ina zan kwantar da hankalina, aure? Bansani ba?”
Ummy ta kalli Jalila ta mata alama da ta fita, sannan ta kalli Goggo bayan Jalilan ta fita tace “ sai yanzu na fahimci me yasa yarki batada walwala duk kuwa da yanda naso ta saki jikinta da gidan nan, na fahimci an cutar dake, an munafurceki, sai dai bayanda za’ai a maida hannun agoggo baya, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, inkin huta anjima sai muyi magana, sai kiji abinda ya faru nima naji abinda ya faru, amma yanzu ko saboda ‘yarki da kwanciyar hankalinta kiyi hakuri, lafiyarki itace abin dubawa a wannan lo