NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 81 of 172

kin mamaki tace “me kake nufi?” Yace “sai ki taso ki zo kibi mijin yarki da kikasa ya daukeki daga gunmu.” Goggo cikin mamaki tace “mijin ‘yata kamar ya kenan?wace yar tawa?” Yace “ni banda lokacin munafircinki, ki taso ki fito, in kuma bazaki iyaba ki cigaba da zama.” Goggo gaba daya kanta ya daure ta kasa gane me yake nufi, kwallama Lantana kira yai yace “zo ki kwashe kayan nan an sallameta. Goggonta mike tsaye tadan dosana kafarta tace “Wai Abubakar me kake nufi ne? Ni na rasa me yasa kullum kai burinka ka jefeni da sharri.” Cikin takaici yace “sharri? Ai kece kike bina da sharri dan na tabbatar badadan ke ba da tuni Inna ta bani company dinsu, amma saboda tana ganin naci amanarsu na kawoki, daga ke har ‘yarki banda bakinciki me kuke tsinanamin? Da na dauka yanzu zan moreta sai gashi yau ta wargaza komai, ni ki wuce mu tafi dan ganinki ma bakin ciki yake sani.” Goggo kallansa kawai take zuciyarta na wani irin kunna, tace “nikam menene matsayina agunka? Ma dauka ni matarka ce.” Wata irin dariya yai wanda yasa ta kallansa cikin wani yanayi, yace “mata? Wa? Kedin? Kema kinsan ni ba sa’an auranki bane ko a can baya bare yanzu, ni ba wani aure ko makamancinsa tsakaninmu, ina zaune dake ne kawai saboda yarki da tazamarmin dole.” Goggo ta share kwallar ta tana neman yin magana ya fita yana cewa “kuma ki sauko yanzu.” Lantana ta shiga saukar da kaya kasa, dady ya nuna mata motar Hassan, nan aka bude boot din mota aka sasu, itakam Goggo ta dade tana kuka, nurse tazo ta kara dubata sannan ta taimaka mata ta sauko, shigowar Lantana na karashe suka sauka tare. Tsayawa tai tana kallan motar, Hassan ya taho da sauri gunta sannan ya kalleta. Kallansa tai cikin mamaki tace “wanene?” Hassan ya kalleta sannan yace “bari na kira kuyi magana da Jalila.” Dan baisan me zaice ba. Matsawa yai ya kira number Sageer. Sageer na daki lokacin da Hassan ya kirashi, yayi mamakin kiransa ya amsa da sauri yana cewa “yaya lafiya?” Hassan yace “Sageer ina Jalila?” Yace “tana sama dazu ta hau.” Hassan yace “please ka dan kai mata waya.” Yace to sannan ya mike ya fito. Jalila tafito daga wanka kenan ta zura wata doguwar rigar atamfa, dan dama kwalliya bata dameta ba saboda ba barinta ake tana yi ba, sannan bama wani iyawa tai ba, balle hankalinta ma ba’a kwance yake ba bare tai tunanin yi. Mai kawai ta shafa ta dan shafa hoda tasa turare, dan kwalimta kawai ta yafa akanta, ta zauna kenan ta dau wayarta taji knocking. Mikewa tai ta bude. Ganin Uncle ne yasa ta tsaya tana kallansa, shima kallanta yai sannan ya mika mata waya yace “Yaya ne.” Amsa tai bata rufe kofar ba ta juya zuwa ciki tana cewa “Yaya!” Yace “yauwa.” Tana jiran ya sake magana kawai taji sallamar Goggo, jikinta na rawa cikin rawar baki tace “Goggo.” Goggo tace “jalila?” Jalila hawaye ya zubo mata tace “Goggo kina ina?” Tace “gani a kasan asibitin ance wai wani ne ya zo daukana shikuma naga bansanshi ba, shine ya kiraki, kinsanshi ne?” Jalila tana kuka tace “ki biyoshi Goggo, ke kadai ce?” Tace “a’a mahaifinki nanan.” Jalila tace “Goggo dan Allah karki nuna bakinsanshi ba, ki bishi zai kawoki inda nake.” Cikin mamaki Goggo tace “inda kike? Kedin bakya gida?” Jalila tace “inkinzo zan sanar dake komai.” Goggo tace to, sannan ta kalli Hassan ta mikamai waya, baice ma Jalila komai ba kawai ya katse wayar. Jalila ta juyo inda Sageer yake tana hawaye, tace “Uncle!” Shikam hankalinsa ya tashi ganin tana kuka yace “menene? Wani abun ya faru ne?” Gani yai tana dariya tana kuka, tace “Uncle, Yaya ya daukomin Goggona.” Tsayawa yai sai dai yanzu baisan me zai kwatanta abinda yakeji ba, yai murmushi yace “duk da bansan meke faruwa ba, it look like abin farinciki ne, sannan alama ce ta shakuwa na shiga tsakaninku, tunda gashi har yasan abinda ba wanda ya sani, sannan lafiyarsa ma nasan samun kusanci dake ne yasa, uhm congratulation, Allah ya barku tare.” Ya juya jiki a sanyaye da kallo ta bishi zuciyarta na tausayamai, ta tabbatar Uncle na santa sosai bawai ya rabu da ita bane dan kansa sai dai zumunci da kaunar da ke tsakanin shi da yayansa. Hawayenta ta share sannan ta zauna abakin gadon tana tunanin me zata ce ma Goggo? Hassan kam Goggo na shiga mota ya kalli Dady yace “Allah yasa akwai kudi a jikinka” Dady yace “babu, menene?” Hassan ya sa hannu a aljihu ya dauko 1000 yace gashi ka hau mota dan gida zan wuce daga nan.” Dady yace “mene? Kai ni na haifi Jalila fa, bawai dan aikin gidansu bane, wai me yasa......” Ganin Hassan yai ya shiga mota kamar ma badashi yake ba yaja yayi gaba, ran Dady a bace yabi motar da kallo. Hassan kam jan motar yai sukai gaba, Goggo da Jalila na baya, suna fara tafiya Goggo tace “meke faruwa? Ya akai Jalila tabar gida?” Hassan ya dan shafi kansa dake ciwo yace “ Jalila zata
🏠