NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 80 of 172

ofar gidansu yai horn ya shiga, Mumy da Dady na zaune a falo, Yasmeen na gefe tana shan chocolate tana wasa aka sanar dasu zuwansa. Ba Dady kadai ba har Mumy sai da gabanta ya fadi, ta kalli Dady da sauri tace “ Dadyn Yasmeen meke faruwa? Cikin rawar baki yace bansani ba nima wallahi.” Yafada yana tuna kalaman Hassan badai zuwan dayace zaiyi yau ko gobe ba shine yai? Mumy ce ta bada umarnin akan a shigo dashi, ita kuma tai sama da sauri. Inna na zaune tana jiran Dady wanda tun jiya take sa ran ganinsa amma baizoba haryanzu. Shigowar Mumy ne yasa ta kalli kofar ta dauka Dady ne, ganin Mumy yasa tace “ya akai kuma?” Mumy da sauri tace “Inna yaran ya dawo.” Tace “yaro? Sultan?” Da sauri tace “bashi ba, mijin Jalila.” Inna ta kalleta da sauri tace “ya dawo ina?” Mumy tace “yana gidan nan, bansan dame yazo ba.” Inna ta mike hankali a tashe tace “gidan nan?” Mumy tace “yana falo.” Inna ta dau mayafi ta fito, mumy ta biyota a baya tana cewa “Inna badai wani abun ya sake faruwa ba?” Itadai Inna batace komai ba, har suka isa kasa. Dady na kasan beni da alama jiransu yakeyi, Inna na saukowa yace “Inna.” Kallansa tai tace “badai jiyan kwafsawa kai ba?” Dady yace “kwafsawa kamar ya?” Haushi ya kamata tace “ wuce muje, koma menene let’s hear it together.” Nan sukai falo? Hassan na zaune akan kujera suka shigo su uku. Kowa ya samu guri ya zauna, Hassan ya gaishesu sannan ya kalli Inna wace itama kallansa take, ya kalli Mumy da Dady wanda suma hanyace “ zuwa nai mahaifin Jalila ya rakani inda mahaifiyarta take, zai sanya hannun sallamarta.” Inna ta kalleshi sannan ta kalli Dady wanda a ransa yace Oh My God! Wannan wani irin yarone? Ya gama hargitsamin plan dina. Dasauri ya girgizama Inna kai alamar ba shi bane. Inna ta kalli Hassan tai dariya tace “Hassan taya za’a sallami mara lafiya? Bayan ba warkewa tai ba?” Yace “eh wannan damuwarmu ce, dan in aka sallameta hannuna zata koma.” Mumy d Dady da Inna a lokaci daya sukace mene? Hassan ya kallesu yace “menene abin mamaki? Ba mahaifiyar matata bace? Banaji cikinku akwai mai hakkinta.” Inna tace “mene?” Yace “ why? Bazai yiwu ba? In bazai yiwu ba bari na kira Abba na sanar dashi, ina tunanin kamar zamu amshi kudin mu.” “kudi?” Hassan ya daure dan kansa wani irin sara mai yakeyi, ya mike ya kalli Dady yace “ina mota.” Ya juya ya fita alamar wai yana jiran Dady a mota. Inna tabi kofar daya fita da kallo, sannan ta kalli Dady, takaici da bakin ciki ne suka kamata. Dady yace “Inna ya zamuyi?” Cikin takaicinsa da bakin ciki tace “dalla wuce kaje ka rakashi, ko so kake company dinmu ya mutu?” Dady ya mike ya fita. Inna takaici ya kamata tace “lalai ba yaran nan bane bashida hankali nice banda hankali dana kawo babban makiyi har cikin gidana da kaina......” Dady ya shiga mota Hassan yaja suka tafi. A asibitin premier sukai parking, ya zaiyi?Gashi bayasan asibiti, gashi yabar Jalila agida sabofa bayasan su nemi wulakantata. #Oneluv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *41* Tsayawa yai shi bai fita daga cikin motar ba sannan baiyima Dady magana ba, Dady kam wanda yake a zaune yana nazarin yaran ya kalleshi yace “muje?” Hassan ya fito daga motar sannan ya tsaya yana kallan asibitin, babban matsalarsa bawai shigar bane, zai iya shiga reception ko gun da ba marasa lafiya kamar office, sai dai daga yayi bangaren dakuna na marasa lafiya hankalinsa yake tashi, shiyasa kwanaki yana fara hawa saman beni yaji gaba daya hankalinsa da tunaninsa na neman gushewa. Da kyar ya daure suka nufi reception din, nan yamusu bayanin abinda sukeso, suka turasu wani office, nan ma sunyi cike cike, suka rubuta kudin da za’a basu, Hassan ya biya, suna fitowa ya kalli saman benin sannan ya kalli Dady dabara ce ta fadomai yace “kaje ka sanar da ita, ka kuma nemi yafiyarta sai ku fito tare ni ina mota.” Dady ya kalleshi a ransa yace “lalai wannan yaran bashida tarbiyya, ina sirikinsa amma ya maidani dan aike? Kamar wani masinjansa, ko driver? Yana tsaye har Hassan ya fita sannan yai kwafa ya hau saman. Goggo na zaune tana shafa mai a hannunta, yau kam jikin da sauki, lantana na tattare kwanukan da aka kawo abincin safe zata maidasu gida. Dady ya turo kofar ba ko sallama, Goggo ta kalli kofa, ganinsa sai dayasa gabanta faduwa, ya shigo fuskar nan a hade ya tsaya yana kallan dakin, kallan Lantana yai yace “ke dan fita.” Lantana ta mike tai waje, Goggo ta kalleshi tace “ina kwana?” Dady bai amsa ba yace “ hankalinki ya kwanta?” Tace “da me fa?” “A haka in aka kalli fuskarki ba wanda zaiyi tunanin zuciyarki akwai hassada, bakinciki da tsantsar munafirci.” Goggo ci
🏠