NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 172

osai sannan ya kalli Sagir ya mikamai jarkar. Sagir ya amsa sannan yace "akwai abinda kake bukata?" Kai ya girgiza alamar a'a. Cikin tausayawa Sagir ya kalleshi sannan ya mike yace "Yaya kazo dan Allah ko waje ka fita kaji iskar duniya." Bai kalleshi ba haka kuma bashi da niyyar amsamai, Sagir ganin haka yasa ya fita tare da ja mai kofar. Sagir yabi bayan kofar da kallo sannan yace "Allah ya yaye maka ya baka lafiya." Dakinsa Sagir ya shiga kallan kayan da ya cire dazu yai sannan yai murmushi ko a ya ta koma gida? Cikin nuna halin damuwa yace " ba ta dai jike ba ko?" Kai ya girgiza yace " ya za'ai ta jike ga lemar da ya bata sannan ya tabbatar tace ai zuwa za'ai a daukesu." Murmushi yai sannan ya dau wayarsa dayazo dayka ya sauka kasa. ************** Jalila ce zaune tanacin abincin dare ita da Goggo, tunanin abinda ya faru dazu takeyi. Jitai Goggo ta tabata tace " Jalila wani abun ya faru ne dazu?" Jalila ta kalleta tace "Bakomai kawai dai ni akwai abinda na dade ina san tambayarki ne Goggo." Goggo ta kalleta tana neman karin bayani, Jalila tace " Bawai da wani abin bafa nake san ji Goggo, kawai dai tambaya ce." Goggo tace "Ina jinki." Jalila tace " Ni Goggo baki da kowa ne sai Dady?" Murmushi tai tace"Ban gane banida kowa ba sai shi? Kin tabaganin wanda bashida kowa a duniya?" Jalila tace " To ni Goggo na kasa fahimtarki ne sam, na rasa takamaimai ke mukeyi a cikin gidan nan." Goggo ta tsame hannunta sannan tace " Lalai Jalila, muhallin Mahaifin naki kike fadama haka?" "Muhalli? Ai kowa yasan gidan Mumy ne ba nashi ba, sannan ni waye ma yasan ni 'yarsa ce, ko suna a makaranta ni ansa nayi amfani da Auwal wato kakan Dady, dan kawai karma asan ni yar sace." Goggo tace" ya isa to, ke dai ba ruwanki da wannan, mahaifinki da mahaifinki ne, sannan banaji yana da laifi a harkar nan, laifin na iyayenmu ne." Jalila tace "Goggo dama tun can baya sanki" Harararta tai tace"Wai yau me kikesan ji ne haka?" Tace"ni dan Allah ki fadamin tarihinki Goggo." Hannunta ta wanke a robar ruwan da Jalila ta kawo ta dan matsa kadan tace " sai randa hankali yazo miki." Jalila ta dan turo baki tace "ni yau meyasa ake tacemin banda hankali?" Goggo tace " Ce miki akai mara hankali a cikin gida?" Tace "Safeena ce." Goggo tace "Fada kukai kenan?" Jalila ta hade rai tace " ni ai....." Goggo tace "sai yaushe ne zaki dinga hakuri Jalila? Na dauka na rokeki akan kai zuciya nesa?" Jalila ta kalleta tace "Yanzu duk hakurin da nakeyi bakya gani? Wlh a yanda nake ji da wata rana sai na fasama 'yar nan baki, kawai hakuri nake sawa a zuciyata." Goggo tausayinta ya kamata tace"kiyi hakuri, duk tsanani yana tare da sauki, shiyasa a koda yaushe nake miki fatan miji na gari, wanda ke sanki ina tunanin hakan ne kadai zai kawo salama a zuciyata da taki." Jalila tace "ni duk wanda zan aura sai dai in zai iya rikemin ke, dan bazan iya aure na barki ba." Dariya Goggo tai tace "Lalai yarinta na damunki Jalila." Haka sukai ta hira har suka kwanta............. ********* Washegari......... Yau tana gama aiki ta shirya ta fito dan jiransu, dadi takeji yau ta rigasu shiryawa, yanda taga Dady ya fito da sauri ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba tasan lalai da matsala, mota taga ya shiga da sauri, sai ga Mumy ta taho da gudu tare da shiga gefensa itama, nan taga sun fita a guje. Baki ta tabe tace "ko ina zasu haka oho" Su Safeena ne suka fito,Yasmeen na ganinta ta isa gunta da gudu tana nuna mata sabon school bag din da Dadynta ya siyo mata. Jalila tace "inyee lalai tayi kyau." Tafada tana kallan wata yagwalgwalaliyar jakar dake bayanta. Mota suka shiga, Safeena ta kalli Sultan tace "Sultan kamar akwai matsala a company dinsu Dady ko?" Sultan ya kalleta yace" ina na sani, in so kike kiji me yasa baki tambayeshi ba da zai fita?" Haushi ne ya kamata tace " Wai kai meyasa mutum bai isa yai maganar mutunci dakai ba?" Tsaki tai sannan ta maida kanta kan Jalila cikin masifa tace "ke kuma uban me kike kallo?" Jalila tace "Ba ni na kar zomon ba Hajiya." Safeena ta kara kuluwa, da saninta tasa kafa ta tako kafar Jalila, Jalila ta kalleta. Safeena tace " sry fa ban kula ba." Jalila ta kalli safarta wacce ta baci sannan ta kalli Safeena tace " mantawa nai ashe idanunki basa aiki." Ran Safeena ne ya baci tace "mene?" Jalila ta kalli window ganin sun kusa isa, me zata gani? Uncle Sagir ta gani yana parking din mashin dinsa, ga mamakinta murmushi ne ya bayyana a fuskarta, Safeena ce ta kalli inda take kallo nan idanunta suka sauka kan Sagir. Idanu ta kuramai, waye wannan? Batasan a fili ta fada ba, Jalila ta kalleta tace "Uncle dinmu ne na Math." Safeena ta kara kallanshi sannan tace "Driver tsaya anan mana ta sauka." Jalila ta kalleta ta tabe baki sannan ta sauka. Muryarta yaji tace "Good Morning Uncle." Juyowa yai ya kalleta, yanayin fuskarsa kadai zaka kalla kasan ganinta ya sashi farinciki. Jalila ta dan matsa gunsa
🏠