NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 76 of 172

i Dadynki yazo." Kallansa tai cikin mamaki tace "Dady?" Yace "eh, yana fallon Abba." Ya fada tare da juyawa. Jalila ta mike gabanta na faduwa, me yazo yi? Badai wani abin bane ya samu Goggon ta? A rikice ta shiga dakin tana neman hijab dinta, gashi a gabanta wanda ta ninke bayan tayi sallah amma tsabar hankalinta baya jikinta sam ta rasashi. Hassan dake zaune yana kallanta shine yace "menene?" Matsowa kusa da shi tai kamar dama jiran kiransa takeyi, tace "Yaya! Dady ne yazo, baka tunanin ko wani abun ne ya faru da Goggona? Ko kuma wani abun suke shirin yimata?" Ganin yanda ta rikice ne yasa yace "Dan yazo shine kika rikice haka?" Tace "Yaya bansan........" Tai maganar cikin wani irin murya mai raunin gaske, da yatsarsa ya nuna mata hijab din sannan yace " a haka zaki?" Ta kalleshi alamar rashin fahimta, yace “ bazaki daidaita kanki ba?” Tsayawa tai tana ajiyar zuciya wai tana calming din kanta, baisan yanzun ma bakinsa ya motsa ba saboda yanda takeyi. Yace “yimin magana naji.” Tace “Yaya!” Yace “sake.” Tace “Yaya.” Yace “bai yi ba.” Baki tadan turo tace “dazu amma inasan maka magana ai hade rai kayi.” Ya kalleta yace “ ni yanzu inaji damuwar dake gabanki tafi tawa, ke mahaifiyarki zaki ceto wace take hannunsu, ni kuma i am confidence akan I will protect mine.” Tace “ni ma.......” Sai kuma tai shiru dan tasan she is not confident. Yanzu ma bakinsa sai da ya sake motsawa yace “jeki, bari na jira naga yanda zakiyi.” Ta kalleshi tace “yaya zakazo?” Yace “ina kenan?” Tace “ gun Dady, tsoro nakeji kar ya sani abunda banzan iya bijerewa ba.” Kafada ya daga mata alamar ba ruwansa. Jalila tai raurau da ido tace “Yaya Please!” Samun kansa yai da kallanta cikin wani yanayi sannan yace “ki wuce kije ko?” Ta dau hijab jiki a sanyaye ta fita.......... Da kallo ya bita har ta fita daga dakin, yabi kofar da kallo. #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *39* Fitowa tai jiki a sayaye, abin duniya duk ya dameta ga tsoron abinda zai fito daga bakin Dady da takeyi. Tana sauka kasa taga Ummy, Ummy ta nuna mata hanyar falo tare da mika mata tiren dake dauke da juice da cup, Jalila ta amsa tare da yin murmushin dole sannan ta nufi falon. A gefen kofar da zata shiga da ita falon taga Sageer a tsaye, kallansa tai da idanunta wanda suka cika da taoro, yace "Jalila, menene wai?" Kai ta girgiza mai alamar ba komai, zata shiga yankara kasa da murya yace "Jalila?" Juyowa tai ta kalleshi, yace "Bakyasan ganin mahaifinki ne? Naga tunda na fada miki yazo naga fuskarki ta canza." Murmushin yake tai sannan tace " bakomai, nagode." Kawai ta shiga, dan batasan me zatacemai ba. Abba na falon suna ta magana ta shiga bakinta dauke da sallama. Abba da Dady suka amsa, Dady ya kalleta cikin farin ciki yace "Jalila!" Jalia tace "naam sannan ta karasa ta ajiye tiren a gabansa ta gaisheshi. Abba ne ya mike yace "yanzu ba abin business kazo ba, uba ne yazo ganin yarsa, kaga bai kamata na shiga tsakani ba, later mayi magana." Dady ya mike yana godiya har ya fita, kallan Jalila yai wacce ke tsugunne a inda ta ajiye juice din, Dady yace "zauna mana." Ta gyara zamanta tana kallansa, gabanta sai faduwa yake. Dady ya zauna sannan ya kalleta yace "hmm ya gidan?" Tace "lafiya, wani abun ne ya samu Goggona?" Yace "wani abun? Kamar me kenan?" Tai shiru ta kasa magana, yace "dan uba yazo ganin yarsa sai ya zama sai akwai matsala?" Jalila ta kalleshi tace "a'a ba haka bane." Yace "Jalila ni mahaifinki ne, ki daina dararewa da ni." Ta kalleshi kawai bata ce komai ba. Matsowa ya danyi kusa da ita yace "jalila magana nakesan muyi." Kallansa tai cikin tsoro, yace "Nikam ya kukai da mijin naki?" Tace "wani mijin?" Yace "wanda kukazo tare mana, badai wani abun kika fadamai ba ko? Naga kamar baiji dadi ba ranar." Jalila ta kalleshi gabanta na faduwa ta kasa magana, Dady yace "amma yasan Goggo ce ta haifeki ko?" Jalila ta daga kai alamar eh, Dady yace "ya fadama wani ne?" Tace "ban gane ba?" Yace "ya fadama wani kamar mai gidan nan cewar Goggo ce ta haifeki?" Jalila tai shiru, yace "ba dai duk wani sirri na gida kin fadamai ba?" Jalila ta kalleshi yanzun ma batace komai ba, ya kalleta ransa a bace, badai duk wahalar da wulakancin da ya hadiye ba lokaci daya wannan yarinyar zata zo ta ruguzamai? Dan ya tabbatar in har Taura ya kwace kudin daya basu tabbas Inna korar sa zatasa ayi daga company din. Kallan Jalila yai rai a bace yace "Wai Habiba ba magana nake miki ba? Sai dai ki kalleni? Ko kema munafircin uwar taki zaki koya?" Jalila cikin tsoro ta kalleshi, hannunya daga a zuciye zai kai mata mari. Jiyai ance " da alama sararka kenan?" Juyowa tai da sauri ya kalli mai maga
🏠