"Budurwarka ce?"
Abba yace "Hassan ni kaina ina mamakin kaina, wai nine nakesan........"
So? Hassan ya kalleshi ya sake cewa, so? Abba so kace?"
Abba yace " Hassan wai me yasa kake kokarin juya kalamai na zuwa abinda ranka ya raya maka?"
Hassan cikin dan daga murya yace "ta ya bazan fassara ba? Ta yaya Abba zaka kalleni kacemin wai so? Ta yaya zaka furtamin kalmar so, sannan kalmar san bawai akan Ummy kake yinta ba, ta ya........"
Kasa karasawa yai saboda numfashinsa dayaji yana seizing.
Abba ya mike da sauri yazo kusa da shi yace "Hassan menene?"
Hassan ya zare jikinsa daga rikon da Abba yamai ya dan ja baya cikin takaici yace "ni danka ne, banida ikon hanaka abinda kai niyya, sai dai wlh Abba kamar yanda na fada in dai had ina numfashi bazan taba bari ka tozarta Ummy ba."
Kofar dakin aka bude, Abba ya kalli kofar shikam Hassan kai ya juya cikin takaici dan yayi tunanin Jalila ce.
Muryar Ummy yaji tace "Hassan!"
Juyowa yai da sauri ya kalleta, Ummy ta share kwallarta data zubo mata sannan ta matso kusa dashi dariya yaga tanayi tana share hawayenta, tace " Hassan yanzu Sageer ya kirani, Dr yace sauki ne ke samuwa a gareka, ya gama min bayani naga bazan iya hakuri ba sai na ganka."
Ta kara share hawayenta tace "Hassan bansan yanda zan kwatanta maka dadin da nakeji ba."
Cikin takaici ya kalli Abba sannan ya kalli Jalila wacce ta juya ta fita, Hassan ya kalleta yace " Ummy?"
Tace " fadanku da Abbanka a kaina?"
Ya kalleta cikin tausayawa, tai murmushi tace "karka damu Hassan bakomai, ko ka manta ba mace daya aka halarta ma namiji ha aura ba? Ta yaya zaka nemi mahaifinka ya zauna da mahaifiyarka ita kadai? In mukai haka bamuyi san kai ba? Ko baka ga na fara tsufa bane?"
Idanunsa ya rufe cikin takaici yace " ya wani irin zance kikeyi Ummy? Waye zai ga Ummy yace ta tsufa?"
Ummy tai dariyar takaici tace "ba wani kai dai sankai zakai, Hassan gashi nan na fara gani."
Yace "me?"
Tace "samun saukinka mana, rabon da kayimin magana mai tsayi haka har na manta, yau gashi nan kana min magana."
Shiru yai kawai yana kallanta, Ummy cikin jin dadi tace "Kar kasa komai a ranka, ka manta da maganar da kukai yanzu, kayi kokari ka dawo Hassan dinka ma da, I really miss that Hassan."
Baice komai ba sai kallanta kawai da yakeyi, Abba ne ya share kwallar data dan zubo mai, sannan yai waje da sauri.
Ummy ta kalli Hassan tace "Please ka kula da matarka, wannan shi kadai ne abinda ni nakeso, kaji?"
Hassan yai shiru, ta juya tai waje.
Jalila na zaune a kasa a falo ta sa kanta akan gwiwowinta, gaba daya abinda ke faruwa ya sa tausayin Ummy ya sa ta zubar da kwalla, wannan wace irin macece? Ita lafiyar Hassan ce a gabanta bawai abinda taji ba?
Tana kallan Ummy ta fita, mikewa tai ta shiga dakin, gani tai har ya tada sallah.
Nan itama ta wuce tai alwala tai sallah, ganin bashida niyar mikewa daga kan sallaya yasa ta fito daga dakin.
Abba kam daki ya shiga ya shiga zagaye dakin cikin takaicin abinda zuciyarsa take sashi aikatawa, wani irin butulci ne hakan yake shirin yi? Ummy ce ta shigo dakin tacemai, yallabai ka fito kaci abinci, ko in kawo ma nan?"
Jiki a sanyaye yace "muje can din."
Ya zauna akan kujera ta zubamai sannan ta turamai abincin gabansa, sannan ta juya tai daki.
Da kallo ya bita dan baisan ta ina zai fara magana ba, shi yanda takeyi kamar ma batasan me ake ciki ba shine ya kara tsoratashi, dana sani ya kara kamashi.
Jalila kam, sai yamma liss ta samu taci abinci kadan, sam ba fuska agun Hassan, dan ko kallanta baiyi ba bare ta samu damar yi mai magana.
Haka tai tayin abinda zatai har dare, shikansa Abba har dare bai samu damar yi mata magana ba.
Bayan sallar Magrib ne Sageer zai shigo yaga motar Dady.
Nan yasa aka budemai yai parking din motarsa, Dady ya fito suka gaisa, Sageer ya jashi ciki.
Yau gidan tsit ba dadi, Hassan na daki, Jalila na falo a kan carpet a kwance tana latsa waya, Ummy na falo shi kuma Abba yana daki.
Sageer ne ya shigo ya kalli Ummy yace "Ummy dadyn Jalila me yazo."
Mikewa tai da sauri tace "ka shigar dashi falon Abba"
Nan Sageer ya shigo dashi yai bangaren Abba.
Ummy ta bude dakinsu ta kalli Abba dake zaune yayi shiru abin duniya ya dameshi tace "Abban Ameera ka fito Baban Jalila ne yazo."
Abba ya mike tare da cewa to.
Ta juya ta fita, Sageer ne ya karaso yace "Ummy na kaishi."
Tace "Sageer dan hau sama kama Jalila magana, bari na shirya abin sha."
Yace to, sannan ya hau sama har zai kwankwasa kofar yaji motsi a falon, nan ya juya ya falon, a kasa ya ganta tana ta latse latsen waya, tv din ma ba'a kunne take ba.
Kallanta ya tsaya yana yi cikin tausayawa, sai dai ya taya yayansa murna ta fara samun lafiya, sai dai shikam tausayin kansa yakeyi, anya zai iya san wata kuwa?
Jalila ce ta juyo, ganinsa tai a tsaye ta mike zaune tana kallansa, yace "ashe kina nan?" Ya dan sosa keyarsa.
Tace "Eh."
Yace "Uhmm dama Ummy ce tace nazo na fadamik