NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 74 of 172

ne, sannan in ma shine ba laifinki bane laifinane tunda ni na matsa miki sai kin fadamin.” Kallansa tai sannan tace “ akansa ne ko?” Kai ya girgiza mata alamar a’a sannan ya shiga toilet. Kallansa tai sannan tai ajiyar zuciya tace “Goggo ya zanyi? Inaji nayi laifi ga wanda zai taimakeki, na tambatar da ban fadamai ba kila yau zai dauke ki daga asibitin sai dai da alama wannan bakin nawa ya ja min........ ************** Inna ce ta kalli Dady tace “Abakar!” Kallanta yai sannan ya amsa, tace “ sai yaushe zaka gidan Jalila?” Yace “so nake sai Taura ya dawo, naji ance yayi tafiya.” Tace “meye damuwa ta da haduwarka da Taura?” Dady yai kasa dakai yana cewa “ai kinga ya kamata mu sake mai godiya da taimakon daya mana.” Inna tace “wace godiya bayan abinda muka aikata yana neman wargajewa saboda shirmanka.” Dady yace “Inna ni......” “Dalla rufemin baki, so kake kace ba laifinka bane? Ka tabbatar ka lalabata da mijin nata, dan kafi kowa sanin dayan plan dinmu da mukesan sake bude wani branch dinmu, ka kuma tabbatar inba da taimakon Taura ba abin nan bazai yiwu ba, ya kamata kasan abinyi, kafin ni insa hannu, kasan in nasa bazata ma kyau ba.” Dady yace “To inna.” Ta kalleshi sannan tace “tashi kaje, ka kuma tabbatar kaje gun Jalila, dan a yanda na ganta da yaran nan ina tsoro karta fadamai komai, wannan yaran idanunsa kadai zaka kalla zaka fahimci ba kara a idanunsa balle ya mana.” Yace “to sannan yai waje. Shiru tai tana sake wani tunanin, yanzu me ya dace tayi?????? (Nace “ kya tambaye ni😏”) ********* Sageer ne ya kalli Dr yace “kana nufin hakan alamu ne na samun nasara? Dr ya kalli Sageer sannan ya jinjina kai yace “Sageer kasan Hassan yana dauke da trauma ne wanda shikadai yasan abin da kuma faruwar abin, tunda abin ya faru ka taba gani yayi ihu ko fada da karaji?” Sageer yace “a’a sai dai zafin rai, rashin magana da kadaicewa, sai kuma rashin nuna emotion na farin ciki ko na tsantsan bakin ciki a fuskarsa, a koda yaushe fuskarsa a hade take wanda yake nuna alama ta bakin ciki ba alama na canji.” Dr yace “Good, yau kuma fa?” Sageer yace “ yau yayi kara sannan kana kallansa kasan ransa a bace yake wanda bacin ran ne da alama yasashi yin karan.” Yace “Very Good, ka gano improvement?” Sageer yace “na fahimta Doctor, a da yana fada sai dai bawai da jikinsa yakeyi ba, ko zuciyarsa yanayi ne da fuskarsa da bakinsa.” Yace “Very Good ka fahimceni yanzu?” Sageer ya daga kai cikin gamsuwa da jin dadi yace “nagane Dr, na kuma gode sosai. #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *38* Saukowa kasa tai, tana matatakalar karshe, taha an bude kofar dakin Ummy, tsayawa tai tana jira Ummyn ta fito sai ta karaso. Ganin Abba tai ya fito daga dakin, mamaki ne ya kamata da sauri ta karaso dan yana fitowa suka hada ido, tsugunawa tai ta gaisheshi. Kallanta yai bayan ya amsa yace " Jalila Hassan yana sama ne?" Tace "eh." Da sauri ya wuce ta ya nufi sama, bata kawo komai a ranta ba kawai ta wuce falo. A kitchen taji Ummy nan ta nufi gunta, tanashiga tace "Ummy ashe Abba ya dawo?" Ummy ta juyo tace "eh, ya jikin Hassan din?" Jalila tace "da sauki." Ta fada tare da karasawa gunta tana neman taimaka mata gun rufe kullar da ta gama zuba ma abinci." Ummy tace "dauki abincinku la'asar har tayi ba wanda yai lunch." Ta amsa da to. Abba kam dakin ya karasa yai knocking din kofar, Hassan daga ciki ya fito daga toilet kenan daure da alwala ya bude kofar. Tsayawa sukai yana kallansa hannunsa rike da kofar, fuskarsa kuwa ya kara hadeta tamau, Abba ya kalleshi yace " Hassan baka ganni bane?" Hassan ya saki hannun kofar baice komai ba ya wuce ciki. Abba ya shiga dakin sannan ya maida kofar ya rufe, yace "Kayi mamakin ganina ko? Bayan dazu mukai waya." Hassan bai kalleshi ba balle yai magana, Abba ya zauna akan sofa sannan yace "Hassan!" Hassan ya juyo ya kalleshi da jajayen idanunsa, yace "How can u? Of all people?" Abba ya runtse idanunsa cikin takaici sannan ya mike ya kamo hannun Hassan suka zauna akan kujerar. Hannayensa na cikin na Abba yake kallansa, Abba yai shiru kafin yace "Hassan." Hassan ya kalleshi cikin takaici sannan ya zare hannunsa daga nashi yace "Zina kake?" Abba cikin mamaki ya kalleshi yace "Hassan wani irin magana kakeyi haka? Taya zaka cemin ni mahaifinka? Ka kalleni kace zina nake?" Hassan ya mike tsaye tare da dan matsawa daga inda yake yace " Ni kaina ina fatan hakan ya zama laifi ne na aikata." Abba yai shiru yana kallan Hassan, gaba daya ma ya rasa ma mai zaice. Muryar Hassan yaji yace "wacece?" Abba yai shiru tare da shafar fuskarsa, Hassan ya juyo ya kalleshi cikin bakin ciki yace
🏠