ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 172

anunta sun firfito, bakinta ne ya shiga rawa tace "In nn nna......" Kallanta tai sannan ta kalli Safeena tace " ke kuma Jalila matsayinku daya da zaki dinga zama tana fada miki kalamai irin haka?" Jalila ta hadiyi wani miyau me daci tace " in na bahaka bane......." "Dake nake magana?" Jalila gabanta sai faduwa yakeyi. Sultan ne ya fito daga kitchen rike da jarkar ruwa na faro yace " Inna ita Safeenar itace da laifi bai kamata ku dinga yanke hukunci ba tare da bincike ba." Kallansa tai tace " Sultan shiga daki" Baice komai ba ya wuce ciki, Jalila kuwa kamar wacce aka tsunduma a wani ruwan haka takeji, muryar Dady ne ya ratsa falon wanda maganganu Inna ne suka sa shi fitowa, da sauri yace "Hajiya ki mata afuwa ni zan hukuntata da kaina." Kallansa tai a wulakance tace " kai har wani hukunci zaka iya? Ka saisaita yarinyarka in ba haka ba daga ita har uwarta zasu bar gidan nan, karka kuskura ka manta gida da dukiyar wanene kake mora daga kai har su." Mumy ce ta rike hannunta tace " Kiyi hakuri ki bari dan Allah." Ta fada tare da jan hannun ta zuwa dakinta. Suna shiga tace "Inna sai yaushene zaki daina disga Abakar cikin yaransa? Karfa ki manta 'ya'yansa sunanan kuma suna jin zafin abin." Kallanta tai tace " ke meyasa bakida hankaline? Kin nace sai kin aureshi dake da mahaifinki, bakya tunanin wannan cin mutuncin da nakemai shine dalilin da yasa yake nuna miki kulawa haka?" Tace " Wlh Inna ke kike ganin haka Abbakar na sona kamar yanda nake sansa, dan Allah ki daina wulakantashi." Ta karasa maganar cikin lalashi. A falo kuwa Dady a zuciye ya sa hannu ya fizgo Jalila ya kaita kitchen, cikin fada yace " sai yaushe ne zakiyi hankali kisan darajarsu Safeenan kikeci ke da uwarki?" Kallansa tai cikin rawar baki tace " Dady itace........" Cikin tsawa yace " so kike in fasa miki baki? Ko me ta miki bazaki hakura ba? Shashashar banza to wlh ki bala'in shiga hankalinki in har kinaso mahaifiyarki dake ku zauna a gidan nan." Yana gama magana yai falo, yana shigowa Safeena taje da gudu da rungumeshi. ************** Yana shigowa cikin gidan ya tadda mahaifinsa a zaune a falo, karasawa yai ya gaidashi sannan ya fara kokarin mikewa. Mahaifinsa yace "Hassan!" Komawa yai ya zauna tare da kallansa, Abba yai ajiyar zuciya sannan yace " Baka manta badai karshen satin nan zamu koma asibiti ko?" Hassan ya kalleshi yace "Abba please ka hakura Abba cikin kulawa yace " Ka taba ganin inda uba ya hakura da dansa? Karka damu insha Allah da yardar Allah wannan matsala taka zata warware sannan zaka samu sauki cikin yardar Allah." Kallan mahaifinsa kawai yake shidai sun kasa fahimtarsa, mikewa yai baice komai ba zaiyi gaba. Kaninsa ne ya dafashi yace " Yaya kace Ameen mana ko hankalin Abban zai kwanta?" Ummy ya kalla wacce ke tsaye ita da Ameerah yai shiru sannan a hankali yadan motsa baki yace Ameeen. Murmushi sukai dukansu m, Sagir ya dafashi yace " Ko kai fa Yaya." Hannunsa yasa ya ture nashi daga kafadarsa yai wuce, Ummy tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Ameera. Kai Ameera ta daga sannan tai kitchen. Faten dankali wanda Ummy ta masa ta zubo a plate sannan ta dau spoon ta fito, sama ta hau sannan ta shiga dakinsa. Yana zaune a kasa kan carpet ta shiga. Gabansa ta ajiye abincin sannan ta ce "Yaya abinci." Kallanta yai yace " BAna......" Tace " Na sani yaya baka jin yunwa dama ko da yaushe zancen kenan, sai dai Yaya ka ci ko dan Ummy ta samu sukuni a ranta." Yace "Naji zanci, ke kuma fita." Ta mike tace " to" Waje tai sannan ta turomai kofar. #OneLuv๐Ÿ’• ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *AyusherMohd* _Gaisuwa mai yawa tare da fatan alkairi a koda yaushe gareki Aunty na ta kaina.....Aunty Goggo Allah ya kareki ya ja da ranki๐Ÿ˜ much luv Sister_ *No 4* Da kyar ya tura abincin sannan ya mike ya shiga bandaki, wanka yai tare da dauro alwala. Jalabiya ya zura ya tada sallah, ya dade sosai akan sallayar yana mika rokonsa gurin Allah sannan ya kwanta a kasa, a takure ya kwanta , sam baisan sanda bacci yai gaba dashi ba. Ummy ce ta leko ta ganshi yana bacci, kusa dashi taje ta zauna tana kallansa cikin tsantsar so da kulawa da kuma tausayi, jan numfashi tai sannan ta mike ta dau tiren abincin da yaci tai waje. Gab da magrib yana bacci yaji kamar ana shakemai wuya, wani irin mumunan mafarki yakeyi wanda ya shiga sandarewa yana kankake jikinsa, idanunsa a runtse sai wani irin zufa da yake kwaranya daga jikinsa, numfashinsa ne ya shiga hawa da sauka, shure shure ya shiga yi saboda tsananin azabar da yake fuskanta. Har zai shiga dakinsa yaji alamar motsin Hassan, da sauri Sagir ya tura kofar, ganin Hassan a kankame yasa yai saurin shiga dakin, tabashi yai yana cewa Hassan! Yaya! A firgice ya bude idanunsa tare da jan wani irin numfashi, Sagir ya dagashi zaune yace "in kawo ma ruwa?" Hassan ya daga kai, da sauri ya mike ya dauko mai ruwa, amsa yai ya lafa bakinsa, sai dayasha s
๐Ÿ