ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 67 of 172

Agoggo ya kalla, karfe biyar saura, mikewa yai ya nufi toilet har zai shiga sai yace " forget what I just said." Sannan ya shiga, ajiyar zuciya tai sannan ta sa hannunta shafi fuskarta. ********** A abuja kuwa, Abba ya kalli Abokinsa Hafiz yace " sry muna magana yarona ne ya kira." Hafiz yace " to yaya? In sanar da ita ne ko ka fasa?" Abba yai shiru kafin can yace "bari dai sai zuwa gobe, in na sake yin nazari." Hafiz yai dariya yace "nazarin me? Bayan abinda ranka ke so ne sannan ba haramun bane?" Abba yai shiru yana tunanin yanda idanun Hassan sukai alokacin daya shigo, can yace "sai dai goben." Hafiz yace shikenan Allah ya kaimu. Nan Abba ya fito, yana neman fita gate yaji muryarta tace "Ba gaisuwa?" Juyowa yai da sauri ya kalleta, gani nai ya hadiye wani yawo, Zaliha tayi kyau iya kyau kamar mai shirin zuwa dinner doguwar riga ce a jikinta ba dankwalli balle mayafi. Gashin kanta kawai ta saukar wanda yasa gyara. Bakinsa na rawa yace "Zaliha ko?" Ta dan kashe mai ido sannan ta matso inda yace tace "badai sunan ma an manta ba?" Yai dariya yace " ina zan manta?" Tace "muje ciki mu gaisa, bana iya jurar tsayuwa." Nan yaga ya juya tana gabe yana binta a baya, komai na jikinta motsi yakeyi. #OneLuv๐Ÿ’• ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* โœ”ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *Thanks for all your comments, it really give me strength ๐Ÿ’ช๐Ÿผlol.....Really Love u ๐Ÿ’• * *35* Abba yaje shiga falon ya tsaya yana kallanta, meke faruwa dashi? Me yasa baya iya controlling din kansa? Juyawa yai da sauri yana neman fita, hannunsa yaji ta kamo. Kallanta ya juyo yai cikin bacin rai sai dai yana kallanta yaji ya kasa cewa komai. Tace "Tafiya zakai?" Yace "a'a." Haka taja hannunsa har cikin falon sannan ta zauna a gefen da yake. Tace " Sai naga kamar na takura ma." Yace "kamar ya kenan?" Ta dan shagwabe fuska tace " gashi nan ka hade rai." Da sauri yace " ba hade rai nai ba, kiyi hakuri." Murmushi tai sannan ta zubo mai juice a cikin cup ta mikomai tace " gashi." Amsa yai yana kallanta yana sha, can yace "Zaliha inaji ya kamata na tafi." Kanta ta kwantar akan kafadarsa ta sakala hannunta cikin nasa tace "da wuri haka? Ni anya ka damu dani kuwa?" Taura bakinsa na rawa yace "damuwa dake din danai shiyasa kika ganni anan garin, nabar tarin aiyukan dake gabana." Murmushi ta saki sannan tace " nikaina mamakin yanda zuciyata ta kamu da kaunar ka nakeyi." Washe baki yai yace " nikaina ban taba tunanin hakan zai faru dani ba." Haka tai ta jansa da hira tana kara dirkamai juice din abarba da kwakwa da suka hada wanda suka hadashi da rikaken maganin da aka basu. Sai dare sosai ya tafi shima harda wani kwallarta wai batasan ta rabu dashi. Haka ya lalabata ya tafi, da yaso barin garin washe gari amma dole ya hakura sai jibi. Yana fita ta shiga dakin Yayarta da gudu tace "Aunty !" Kallanta tai ta mata alama da tai shiru, nai tai shiru ta matso kusa da ita tace "Aunty gaskiyar malamin nan kinga yanda ya mato kuwa?" Auntyn tai dariya tace " an fadamiki barno gabas take? Sanda malamin yace mu koma gida zaizo da kansa me nace miki?" Tace "ai ni ban dauka abin zaizo da sauki haka ba." Tace " kedai kiyi abinda malam yace karki kuskura ki nemi jin rayuwarsa da matarsa ko 'yayansa har sai mun amso dayan maganin." Tace "To Aunty zan kiyaye." Nan ta fito tana murmushi, dolene ta fara rubuta abubuwan da take bukata intayi aure da irin wayar da takeso, da motar da takeso da gidan da takeso. Dan bataso a wuce wata daya basuyi aure ba. Taura kuwa yana shiga hotel dinsu yai sallah sannan ya kwanta akan gado yana kara tunano abinda ya faru dashi, yaushe zuciyarshi ta koma budurwar zuciya? Me zai cema Ummy? Sagir? Ameera? Has......... goshinsa ya dafa dan ya tabbatar akwai gagarumar matsala babba in Hassan yasan halin da ake ciki, dan tabbas shikansa tsoron abinda zai biyo baya yake. Baisan sanda ya dau waya ya kira Zaliha ba, nan ya baje sukai ta hira har sha biyu sannan ya kwanta. ********* Jalila kam batai baccin safe sosai ba dan karfe takwas ta sauko danyima Ummy abinci, dankali ta fara firewa bayan ta saka tafashen naman kaza, tana suya tana dan kara gyara kitchen din har masu aikin gidan suka iso. Bayan ta gama suya ne tadan tafasa indomie tai awara da ita sannan ta jera akan dinning. Dakin Ummy ta nufa ta kwankwasa. Ummy ta taso ta bude mata, Jalila ta rusuna ta gaisheta sannan tace "Ummy ya jikin?" Ummy tai murmushi tace " Jalila na warke, na barki da aiki ko?" Tace "kai Ummy wannan ne aiki?" Ummy ta riko hannunta suka fito falo tana cewa "Hassan fa?" Tace "bacci yake sanda na fito." Ummy ta dan tsaya sannan tace "Jalila haryanzu a kasa kike kwana?" Jalila ta sunkuyar da kai saboda kunya sannan tace "Ummy yaya ya fara canzawa, yanzu yana amsawa in namai magana.
๐Ÿ