wani abun, Jalila bazata taba zuwa ta tafi a aranar ba.
Jalila ta shiga mota ya tada suka fara tafiya, yanda taga yanayin fuskarsa ne yasa tai shiru dan taga ba alamar wasa.
Can ta kasa daurewa tace βYaya nagode.β
Bai kalleta ba yace β 4 wat?β
Tace β taimakon da kamin.β
Shiru sukai sai tafiya kawai da yakeyi, can tai murmushi cikin sanyin murya tace β at first tsoronka nakeyi, later sai na fara fahimtar ka, yau kuma na ga wani side naka na daban.β
Hassan bai kulata ba sai da aka dade yace β kina tunanin adan karamin kwanakin da mukai ne kike tunanin kin fara sanina?β
Tai murmushi tace βaβa bansanka ba, sai dai na fahimci abu daya.β
Juyowa yai ya kalleta, yana jiran abinda zatace.
A ranta tace u are kind, amma a fili dariya tai tace βna fahimci kana matukar san Ummynka.β
Kansa ya dauke daga inda take ya cigaba da tukinsa.
Tana san sanar dashi matsalar Ummy sai dai tana tsoro.......
#Oneluvπ
π― *JALILAH* π―
Written By : *AYUSHER MUHD*
βote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_π‘)
*34*
Yana tafe yana tunanin kalaman Abba har suka iso gida, parking yai sannan ya maida kansa ya kwantar a jikin motar.
Jalila ta fita daga cikin motar, sannan ta juyo ta kalleshi, ganinsa tai bashida alamar ma fita.
Komawa tai cikin motar ta zauna tace "Yaya! Bazaka shiga ba?"
Bai kalleta ba bashi kuma da alamar bata amsa, Jalila ta kalleshi tace "Yaya?"
Idanunsa ya bude ya kalleta yace "Nikam bakinki baya shiru ne?"
Kallansa tai ta rufe bakinta da labanta, yace " jeki, ko dole sai tare zamu shiga?"
Jalila ta mike sum sum tai waje, ita kanta mamaki take, tana da surutu sai dai ba'a ko ina ba, a gaban Goggonta kadai take magana san ranta, amma ta rasa me yasa yanzu ta saki jiki da Hassan har take magana haka dashi, duk kuwa da dizgatan da yake.
Rufe masa motar tai ta tako zuwa cikin gida, tana kokarin bude kofa shi kuma ya turo kofar zai fita.
Tsayawa sukai suka kalli Juna, Jalila ta matsa ta bashi hanya.
Sagir ya kalleta yace " ki shiga."
Ya fada tare da rike da matsa mata, kallansa tai sannan ta tako ta shiga.
Har zata wuce taji yace " kinga Goggon?"
Ta kalleshi ta daga mai kai alamar eh, murmushi yai tare da cewa "Alhamdulila."
Bata amsa mai ba ta wuce ciki, dakin Ummy ta nufa ta kwankwasa mata kofa.
Ummy na kwance dan zazzabi ke neman rufeta tace "shigo."
Jalila ta murda kofar dakin ta shiga, Ummy na kishingide akan gado Jalila ta shiga.
Tace "Ummy ina wuni?"
Ummy ta kalleta tace "kun dawo?"
Jalila ta matso tace "eh, amma Ummy lafiya dai ko na ganki a kwance"
Kallanta tai tace "kai na kemin ciwo."
Da sauri Jalila ta matso tace "Sannu Ummy, kinsha magani?"
Murmushi ta sakar mata tace "kar ki damu daga nayi bacci zai ware."
Jalila ta tsaya tana kallanta cikin tausayawa, tabbas abinda ya faru jiya ne kila yake damunta.
Daurewa tai tace "Abba fa?"
Ummy tace "dazu ya tafi Abuja."
Jalila tace "Ummy ko dai in kira Yaya akaiki asibiti?"
Hannunta ta kamo tace "Jalila karki fadama Hassan banajin dadi."
Jalila cikin mamaki tace "Ummy me yasa?"
Tai murmushi tace "Tun yana karami bayasan yaga ko ya ya ne banda lafiya, in kuwa ya sani to ya dinga kuka kenan, yanzu kuwa da ba lafiya gareshi ba inya sani abin nashi karuwa yake."
Jalila tace "to a kira Ya Sagir."
Ummy tace "Jalila karki damu, daga na kwanta shikenan."
Jalila tai shiru kafin tace "bari nai sallah."
Nan ta fito zuwa sama, baya dakin nan tai alwala tai sallar isha'i sannan ta sauko zuwa kitchen.
Duk da batajin dadi Ummy sai data musu jollof din taliya wacce tasha kayan ciki.
Jalila ta dau nasu takai sama sannan ta dawo gun Ummy.
Hassan kam ya dade a mota kafin ya fito, kofar dakin Ummy ya murda dan yana san ya tabbatar da gaske Abban yayi tafiyar?
Ummy na kwance da alama bacci take, ita kuma Jalila na zaune a kasan carpet ta daura kanta akan gado, itama da alama bacci ya fara dan daukarta.
Tsayawa yai yana kallansu, yanayin kallan da yake musu ba irin kallan daya saba bane, yau kallo ne yake na jin dadin ganin Ummy da Jalila.
Yana neman juyawa yaji Ummy tace "Hassan!"
Juyowa yai ya kalleta, tace "zo ka dauki matarka ku tafi."
Yace "in dauketa kamar ya?"
Tace " Badai dan rashin tausayi tashinta zakayi ba?"
Yace "Ummy tanada kafa fa?"
Ummy ta mai alama da hannu akan yai shiru sannan ta mai alama da dayan hannun akan ya shigo.
Shigowa yai fuskarsa a daure, a hankali tace "dauketa, da alama baccin yanzu ya dauketa, kuma da karfi ya dauketa."
Hassan ya kalli Ummy sannan ya kalli Jalila dake bacci, ta karamai alama da hannu akan ya dauketa.
Cikin takaici yasa hannu ya dauketa kamar yarinya.
Jalila kam yana daukanta taji alama sai dai muryar Ummy dataji tace "to sai da safenku."
Yasa ta fahimci Hassan ne sai ta kara rufe ido dan batasan ta ina zata fara kallansa ba.
Hassa