NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 63 of 172

an ikon Allah. Ganin yana neman fita yasa ta mike da sauri kar a rufeta da duka tai waje. Suna shiga mota ya ja yai gaba. Jalila ta zubamai ido tana nazari akansa, can tasa wata dariya tace "Yaya kaga idon Inna kuwa?" Kallanta yai yace "wacee hakan?" Jalila tace "kaka ta? Ahh ba kakata ba kakar su Yasmeen." Hassan bai kula ta ba ya juya yana tuki, ita kuwa in ta tuno yanda sukai sai ta kara sa dariya. A haka har suka isa, suna shiga ya nemi a duba musu sunan Goggo. Nan wata nurse ta wuce dan nuna musu dakin, Hassan ya kalleta yace "ina mota." Da sauri ta riko rigarsa ta kasa tace "mota?" Kallanta yai, tace "dan Allah kuje ka gaidata. Batasan anmin aure ba fa?" Ta fada tare da canza fuska xuwa tausayi...... #Oneluv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *33* Hassan ya kara kallanta yace “kina nufin in shiga ciki?” Ta daga kai, ya kara kallan asibitin, batasan nan ma dakyar ya shigo ba? Jalila ta kalleshi tace “Yaya!” Kallanta yai sannan ya fizge rigarsa ya juya. Binshi tai har jikin motar ta tsaya a jikin kofar inda yake tace “Dan Allah yaya kazo muje.” Kallanta yai yace “ wai meke damunki? Ana abu dole ne?” Tace “i am really scared” Kallanta ya sakeyi, tace “bansan a wani hali zan sameta ba, bansan me zance mata ba in ta tambayeni, Yaya dan Allah kazo muje.” Oh God! Wannan wace irin yarinya ce? Yace “to in naje ta tambayeki wanene ni me zaki ce?” Kallansa tai sannan tai shiru, yace “ki je ki fito in kuma in barki anan ne sai ki zauna sai dare.” Jalila ta kalleshi tace “zan zauna anan din.” Yace “ ur choice.” Sannan ya kalleta yace” zan rufe kofa.” Jiki a sanyaye ta matsa daga jikin motar, ya ja yai gaba, ta glass din mota ya hangota tana tsaye inda ya barta. Bazai iya shiga ciki ba dan shikadai yasan memory din da yake dawomai in ya shiga cikin asibiti gun marasa lafiya. Jalila ta juya jiki a sanyaye, tana shiga nurse din ta tareta tace “ina yayan naki?” Jalila ta kalleta tace “a ina Goggon take?” Nan tai gaba Jalila ta bita a baya. Goggo na zaune akan gado, ba laifi kafar tata ta samu sauki sosai, tana shiga tai gunta da gudu ta rungumeta ta saki wani irin kuka. Ita ma Goggon kuka ta saka, sun dade a haka kafin Goggon ta daure tace “Jalila ina kika shiga?” Jalila ta dago ta zauna kusa da ita tace Goggo na. Goggo tasa hannu ta share mata kwalla tace “ kukan ya isa hakanan, me ya faru? Ko jikin naki ne?” Jalila ta kalleta tana girgiza kai tace “ba komai Goggo na, ya jikin naki?” Goggo ta kalleta kallon tuhuma tace “Jalila kin tabbatar? Dan nikam tsoron mutanen nan nakeyi.” Hassan har ya fara tafiya naga yayi kwana da motarsa ya dawo asibitin, bude kofar motarsa yai ya fito sannan ya nufi asibitin. Nurse din tana ganinshi ta taho inda yake, tace “ ka dawo?” Hassan yace tana ina? Nan Nurse din ta fara tafiya yana binta a baya. Suna taka steps din gaba daya kawai takawa yake, suna zuwa second floor yaji kansa ya fara juyawa, da sauri ya rike bango, sannan ya tsaya ya rike gefen zuciyarsa. Wani irin numfashi yake fitarwa, juyawa yai da sauri ya sauka kasa, nurse din ta juyo kawai taga bayanan. Hassan ya sauka da sauri ya shiga mota ya ja ya rufe ya fita da gudu. Sai da yai nisa sannan yai parkin ya kifa kansa akan sityarin motar yana maida numfashi. Jalila tai murmushi tace “Allah Goggo ba komai, kawai dai ina bakin cikin laifin dana miki ne.” Goggo tace “laifi?” Jalila ta kwantar da kanta akan cinyarta tace “ ni dai ki yafemin Goggo na.” Goggo ta shafi kanta tace “ba abinda kika min Jalila, na tabbatar ko da kin min ba daidai ba sai dai a rashin saninki ko kuma tirsasaki akai, kawai dai inaso kisan ke kadai ce dani a duniya” Jalila ta share kwallar data gangaro mata tace “ tsoron sanar dake nakeyi.” Goggo tace “ko menene ki fadamin.” Jalila tai shiru can tace “zan fada miki amma sai kin warke an sallameki.” Goggo tai murmushi tace “ shikenan, da alama akan Sagir ne.” Jalila tai murmushin yake batace komai ba. Haka ta zauna makale da Goggonta, Lantana na gefe tana kallansu gwanin sha’awa. ************* Su Hassan na fita Inna ta matso kusa da Dady ta daga hannu ta sharara mai wani wawan mari, da sauri ya kalleta dan sam baiyi zatan abinda zatamai ba kenan. Mumy ta matso da sauri ta tsaya agan Inna tace “ Inna menene hakan?” Inna cikin takaici tace “Uban wa yace ka fadi inda take?” Dady ya kalleta ransa a bace takaicinsa agaban Yasmeen dan wulakanci. Mumy ta kalleta tace “Ta ya bazai fada ba bayan yaran yasan komai, da alama Jalila ta gama sanar dashi duk abinda ke faruwa?” Inna cikin kunar rai ta zauna akan kujera tace “Akace bashi da hankali?” Mumy ta zauna kusa
🏠