ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 61 of 172

wantar da kansa kan pillow. Ummy kam sai wajen takwas da kwata ta farka, kallan agoggo tai cikin mamaki, wani irin bacci tai haka? Shiru tai tana tunanin abinda ya faru itada Abba a daren jiya. Bayan ya dawo tanemi ya fito falo yaci abinci, tunda haka suka saba. Kallanta yai yace mata "bayajin yunwa." Tai murmushi tare da ajiye jakarsa tace "haka ka koshi a waje ne da alama." Ganin sun saba irin wannan abin bata daukeshi a komai ba, sai cewa yai ban gane na ci a waje ba? Me kike nufi? Gun wata naje ta bani ko me? Mamaki ya kama Ummy tace "meye hakan? Ai kafi kowa sanin ba hakan nake nufi ba." Ai kuwa ya kara hawa wai ta rainashi, nan ya fara masifa ta inda yake shiga bata nan yake shiga ba. Haushi yasa ta fito tabar mai dakin, ajiyar zuciya tai sannan ta mike, ta fito falo. Tayi mamakin ganin masu aikin har sun gama shara suna mopping. Can tai tunanin Sagir, murmushi tai sannan ta nufi kitchen. Jalila ta hango tana aiki, da sauri ta karasa tace "Jalila?" Jalila ta juyo tace "Ummy ina kwana?" Ummy tace "Jalila? Yaushe kika tashi haka?" Jalila tai murmushi tace "kije ki zauna Ummy na kusa gamawa ma." Tace " banyarda ba bari naje na dawo dai." Ta juya ta nufi dakinta. Shikansa bai samu barcin arziki ba, dan bayan ta tafi abin duniya ya dameshi, ya rasa mai yasa yake saurin hawa akan kome ta masa wanda ya tabbatar basai wani abin bane, ya rasa meke damun zuciyarsa da yanzu duk abinda Ummy tai matar da yake ganin kimmarta a rayuwarsa bata birgeshi yanzu. Zaliha....... Duk sanda wannan sunan yazomai saurin mikewa yake yana girgiza kai, bai isa ba, ta ina zai fara yima Ummy butulci? Yasan bazata taba hanashi aure ba dan macece mai class da sanin rayuwa wacce sam batasan fada balle musu, to amma yarinya sa'ar danta? How can he? Yana kallanta ta shigo ko kallansa batai ba ta shiga toilet, can ta fito ta bude wardrobe ta dau abu zata fita. Yace "Hajiya! Ina tunanin zuwa Bauchi gobe." Tace "Adawo lafiya." Ta fita. Adawo lafiya? Ita kuwa tana fita tai kitchen gun Jalila, tare suka karasa aikin. Jalila tace "Ummy bari na hau sama." Ta fada tare da saurin yin saman. Hassan ya farka ta turo kofar dakin, kallansa tai tace "ina kwana?" Bai amsa ba, tace "bari na shirya." Ya daga kai alamar to, juyawa tai tadau towel tai cikin bandakin sanye da kayan jikinta. #OneLuv๐Ÿ’• ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* โœ”ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *32* Kallansa tai bayan ta fito cikin zumudi tace "Yaya na fito ka shiga wanka." Yace "in nayi wanka me zan miki? Ko dama ke kike sani yin wanka?" A ranta tace "hmm wannan mutumin?" Amma a fili tace " a'a gani nai zamu fita." Yace "zuwa inafa?" Ya fada yana gyara gadan daya kwanta dan shi kam badai gyara muhalinsa ba." Jalila da sauri ta fara tayashi ta dayan bangaren tana cewa "jiya fa kace yau zamu." Yace "yau din ta kare ne?" Baki tadan turo mai mutumin nan yake da ita? Hassan ya matso kusa da inda take a tsaye, hannu yasa ta bayanta ya dauko wani littafi sannan ya koma kan kujera ya zauna. Jalila ta tsaka sakato tana kallan ikon Allah, amma mutumin nan.... Cikin takaici ta fita waje tana wata irin tafiya, bugo kofar tai sannan tabi kofar da kallo, dama ita tasan ba lalai ya taimaketa ba. Da alama Uncle kawai zata fadama, haka ta zauna a kujera ta kuna Tv. Shikuwa tunda ta fara cika tana batsewa yake kallanta ta gefe ido, da ta fara wata irin tafiya kuwa tsayawa yai yana kallanta harya banko kofar. Mai zan gani? Hassan naga ya murmusa sannan ya girgiza kai. Shikansa bai fahimci murmushin yai ba saboda rabansa dayai murmushi ko dariya har ya manta. Amma tabas yau kam da saninsa ya kular da ita, dan ya fahimci wani sabon zumudi da takeyi. Ajiye littafin yai sannan ya mike ya shiga toilet, yana fitowa ya dauko jeans da shirt yana shirin sawa, baisan msi ya tuna ba sai naga ya cire ya dauko farin yadi mai shara shara ya sa. Bayasa hula dan haka ko dubata ma baiyi ba. Zama yai ya bude tiren data ajiye. Kallan plate biyun dake gun yai, kenan bataci abinci ba? A falo taji yunwa ta kamata ta turo kofar daki fuskarta a hade, kallanta yai sannan ya dauke kai kamar bai ganta ba. Ganinsa a gaban abinci yasa ta tsaya turus tana kallansa. Kallanta yai yace " Kin fasa zuwa ne?" Da sauri tace "zamu?" Kallan abinci yai sannan ya kalleta, da sauri ta matso tana dariya, duk yanda taso ta boye farin cikinta ta kasa. Shikam ya hade rai yana kallan ikon Allah, shi ta fara zubama sannan ta zuba nata. Dan kadan taci ta fara neman mikewa, kallansa tai taga shima kallanta yai fuskarsa a daure. Da sauri ta koma ta zauna tana kara cin abincin. Yana mikewa kuwa itama ta mike, gani tai ya koma ya zauna akan gado. Tace "Yaya na......" Kasa karasawa tai sai ta wayance tace "Yaya naga bakasha tea din ba, ko na kawoma ruwa?" Yace "later." Juy
๐Ÿ