NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 172

nar dake bakinta sannan tai saurin juyawa, dan ji take gabanta na faduwa. Murmushi yai sannan yace "muje in kaiki gida." Tace " Naam" Yace "Baki ji bane ko bakya so ne? Hadari ne a garin in aka fara ruwa kina tunanin yanda zakiyi kije gida? Ko su Kannen naki ne bakyasan ki tafi ki barsu?" Shiru tai tana dan nazari kafin tace " Nagode da kulawa Uncle Sagir sai dai in na tafi ba tare dasu ba fada za'amin." Kamar zai sake magana sai kuma taga ya juya ya koma ciki, tana tsaye ya fito da lema ya mika mata bai jira tace komai ba ya hau mota yai gaba. Da kallo ta bishi yau da mota yazo? Hmm ita kadai tasan cin zarafin da za'ama mahaifiyarta in har ta tafi. Tana tsaye aka fara yayyafi da sauri ta bude lemarta ta shiga, kan kace me ruwa ya tsuge, ruwa ake mai karfin gaske wanda tana cikin lemar ma amma ba tsira tai ba, komawa gefe tai ta rakube. Kamar motar zata tsaya sai taga ta yi gaba da gudu, cikin tsananin tsoro ta kalli motar tare da kwalla kara da karfi tace "Safeen ina nan fa......" A cikin motar kuwa wanda Safeena tacema Malam Auwal da alama ta tafi ganin hadari, wanda akasan ranta ta tabbatar bata tafi ba, tsabar mugunta ce. Haka ta rakube dan tsoro takeji ta koma cikin makarantar ita kadai, ganin a tsayen ma tsoro ya kamata kawai ta fara tafiya tana tafe tana kuka mai sauti, sai dai kasancewar karar ruwa bai sa tasan da karfi take kukan ba. Yana zaune a cikin motarsa daga gefen titi wanda shi dama yafisan gurin shiru inda ba mutane, shiyasa mafi akasari zaka sameshi ne a zaune a cikin motarsa ya zuge glass kawai ya kwanta. Jikin motar ta tsaya da taga ruwan ya dan yi sauki duk jikinta ya jike jagaf, ga lemarma sai lankwashewa takeyi saboda iska. Juyawa tai ta kalli glass din motar, da yake motar mai tints ce sai ta shiga kallan kanta tana kara wani kukan,sam tunaninta bai kawo mata da wani a cikin motar ba. Kallanta kawai yakeyi sai sharar kuka take wiwi. Komawa yai ya maida kansa ya rufe idanunsa kamar mai bacci. Kara juyowa yai ya kalleta, kuka take sosai, kamar dama neman kukan takeyi, haushi duk ya isheshi kamar a kansa take kukan, kofar mazauninsa ya bude, a tsorace ta kalli motar, kallansa tai a tsorace, sannan ta kalli motar . Kallan tsoro tamai tace "Hmm hmm." Hannunsa ya dago ya mata alama da ta matsa daga gun, tace "Ban gane me kace ba." Alama ya sake mata da hannunsa akan tai gaba, sannan ya maida kofarsa ya rufe, da harara tabi kofar motar sannan tace " wannan kuma wani kwarantancen dan duniyar ne? Maganarce yafi karfin yimin ko kuwa tsabar rashin mutumci ne?" Harara ta sake yi sannan ta juya, kallan motar ta sakeyi sannan tace "irin motar jiya" Taja tsaki tace " da alama duk masu hawa irin motar nan basuda mutunci." Sam ta manta da kukan da takeyi saboda masifa, tana tafe yayafi na digar mata tana yan mitocinta, sai da ta gama gajiya ligif sannan ta isa gida. Goggo kuwa duk ta kasa zama saboda tsoro ganin yanda ake ruwa ga har yanzu bata dawo ba. Tana shiga Goggo ta kalleta cikin tsananin tausayawa. Jalila fadawa tai jikinta duk da jikarta ta sa kuka, idanun Goggo suka ciciko sai kanta kawai da take shafawa. Jalila ta dago tana kuka tace ""Goggo Allah nasan da sanin Safeena, ai tasan ban taba tahowa ba." Goggo tace "Kiyi hakuri" Jalila tace "Goggo sai yaushe ne zaki daina cewa inyi hakuri? Gaba daya rayuwarmu ni dake a hakuri ta kare, nikam ina takaicin cewa ma Dadyne mahaifi......." Marin da Goggo ta mata ne yasata yin shiru, kallan Goggo tai kuncinta a rike,Goggo ta kalli hannunta cikin dana sani sannan tace " taya zaki dinga kushe abinda Allah ya hada?" Jalila tace "kiyi hakuri Goggo bazan kara ba" Hannunta ta kamo tace " na sani, na sani sosai abinda ke ranki Jalila sai dai bayanda zamuyi da hukuncin Allah, sannan komai zaiyi ko kowa zai zageshi to lalai banda ke, domin shine silar zuwanki duniya." Tace "Na daina Goggo kiyi hakuri." Goggo tai murmushi tace " yi maza ki cire kayanki." Mikewa tai ta shiga dan dakinsu. Tana cire kaya tai sallah sannan ta mike tace "Goggo bari naje" Goggo tace abinci fa? Naga da safe ma a tsatsaye kikaci, shiyasa kullum gakinan kamar a hure. Tace " Goggo in na dawo naci" tace ban yarda ba sai dai ki tafi dashi can kici, ina zaki jira sai wajen magrib kici abinci? Jalila tai murmushi sannan tace " to in na gama ma rana zam deba inci a namu." Goggo tace "kin tabbatar?" Tace eh karki damu Goggo na Tana isa ta tadda Safeena a falo tana kallo, wata banzar harara ta maka mata sannan tace " da kuka taho kuka barni sai kuma gashi mai rai da lafiya yayo gida da kansa." Safeena tace " au da gaske kina can dama? Ni danaga ana zabga ruwa sai naga ina mai hankali zai tsaya a cikin ruwan nan?" Jalila tace " mai hankali kikace ai ni kuwa ina na ganshi?" Ta karasa maganar tana harararta, jitai ance " Uban wa ya baki damar cimata mutunci?" Gabanta ne yai wani irin faduwa, duk gidan ba wanda take tsananin tsoron ya mata fada irin Inna, a tsorace ta kalleta id
🏠