ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 59 of 172

a tana kallansa, ajiyar zuciya tai tace "Jalila u are really a fool." Shikam yana fita ya sauka kasa zai fita, Ummy ce ta leko daga daki tace "Hassan?" Kallanta yai sannan ya matso yanasan jin menene, ta kalleshi tace "ina zaka kuma?" Yace " fita." Shiru tai alamar damuwa wanda yasa yace "menene?" Tace "Hassan na rasa meke damun Abbanka." Kallanta yai cikin kulawa, sai dai baisan ta ina zai fara jin matsalarta ba, yace " Me yayi?" Ta girgiza kai tace "bakomai, jeka kawai amma dan Allah ka dinga zama a gida kaga Ameera tunda taje gun Aina'u bata dawo ba, Sagir kuma na rasa me yakeyi yanzu sam ya rage zaman gida, ni kuma kasan dole tadingajin nauyi na, ka taimaka ka dinga zama ko da ba lalai ka yarda kuyi hira ba at least dai zataji motsinka a kusa da ita." Kallanta yai kawai bai amsa ba sai cewa dayai "Abban me ya miki?" Tace "me zaimin kuwa? Kawai dai naga ne kamar akwai abinda ke damunsa" dan tasan intacemai ya canza mata gaba daya, ya daina zaman gida, ya daina zama suyi hirar business data duniya lalai tafi kowa sanin halin Hassan, abin ne ke cinta yake damunta shiyasa ma tamai magana. Kallansa tai tace "sai ka dawo." Tai saurin komawa daki, haryakai jikin kofa sai naga ya juyo ya kalli sama sai kuma ya fita. Jalila ta zauna a kasa ta baza tagumi, takaicin kanta duk ya isheta, sai yamma ta sauko. Kofar Ummy taje ta kwankwasa, Ummy ta fito sanye da hijab da alama sallah ta idar. Jalila tace "Ummy me za'a dafa?" Ummy tai murmushi tace "dauko hijab dinki mu fita cefani. Jalila cikin mamaki tace "Cefane Ummy?" Gani tai tunda tazo gidan bata taba gani anje cefane ba masu aiki ne ke siyowa. Ummy tacemata yi sauri. Jalila ta juya zuwa sama, hijab dinta ta dauko sannan ta sauko. Ummy ta daga waya tace "Dan Ummy ka iso?" Yace eh, nan suka fita. Sagir na tsaye jikin mota yana hangosu ya fito ya bude musu baya yanama Ummy salute. Ta harareshi tace " Officer ka iso?" Yace "barka da isowa." Jalila tai dariya tana kallansu abin sha'awa, bata taba gani mace mai saukin kai kamar Ummy ba, tasan itakan Goggonta kadai ta sani sai yanzu dataga Ummy. Suka shiga baya dukansu, Ummy tace "Driver mu fara zuwa Wellcare. Nan suka tafi ahanya sai hira sukeyi, Jalila kam sai dai tai murmushi sai in an tambayeta tace eh ko a'a. Ummy kam ta fito ne dan ta debe musu kewa da ita da Jalila, dan tasan Jalila na bukatar kulawa, ita kuma saboda gudun tunani da zargi yasa take neman abinda zai debe mata kewa. Haka sukaje sukai siyayya sosai, sannan suka biya shagon wayoyi, Ummy da kanta ta zaboma Jalila waya irin ta hannunta Sumsung ce Note 9. Jalila kam gaba daya ta rasa me zatace, dan itakam batasan ta inda zata fara magana ba. Sagir kam dadi yakeji ganin fuskar Jalila na dauke da murmushin da yake har zuciyarta bawai na iya baki ba. Haka suka isa gida sannan sukai abinci ta dau nasu ta hau sama, yau kam zuciyarta ta ragu da damuwa, sannan ta kara samun karfin gwiwar yima Hassan magana. Bayan isha'i ya dawo ta jawo mai abinci kusa dashi, Hassan ya kalleta yace "nasha yogurt, later." Jalila ta dauke tasa a gefe, zama tai a kan gadon daga inda kafafunsa suke can karshen gado, ta mikomai wayarta. Kallanta yai sannan ya amsa, yace "na meye?" Tace "Ummy ce ta saimin." Ya juyata sannan ya mika mata yace "to." Tace "bakasa number ka ba." Yace "me zakiyi da ita?" Tace " In wani abin ya taso." Ya kalleta yace "kamar me?" Wayarta ta amsa tace "shekenan kawai kace dai bakasan sawa." Kallanta yai yace " kawo dai." Ta mika mai tana dan tabe baki kadan kanta a kasa, ya amsa yace "in zaki harareni ko murgudamin baki, ko tabemin baki ki tabbatar kinyishi ina kallo dan ko ban kallekiba ina sanin inkinyi hakan. Jalila ta kalleshi tace "ni banyi komai ba." Wayar ya mika mata yace "yi saving." Ta amsa tasa "Yayah." Sannan sukai dan shiru, can tace "Yaya me zanyi in taimaki Goggona?" Kallanta yai yace "zancen dazu ne?" Tace "eh, na gane dazu na fara ma magana ne kamar i am hopeless bansan me zanyi ba, bani kuma da plan." Littafin sa ya dauka baice komai ba, saukowa tai kasa ta tsugunna a kusa dashi tace "Yaya dan Allah ka taimakeni." Littafin ya ajiye yana kallanta........... #OneLuv๐Ÿ’• ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* โœ”ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *31* Kallanta kawai yake baice komai ba, ta dago tace " Yaya Goggona......" Sai ta kasa karasawa saboda kukan daya kwace mata, kallanta yake baida niyyar tanka mata, balle ya lalasheta. Sai dai yanayin kukan da takeyi ya fahimci lalai she is desperate. Yace "in kuka zakimin zan iya tashi in fita." Ta share hawayenta tace " bansan ta inda zan fadamaka halin da Goggona take ciki ba." Yace "ban tambayeki wannan ba, abinda kawai nakesan naji me kike tunanin yi, sannan me kikeso nayi miki?" Ta mike da sauri tace "Yaya zaka taimaken
๐Ÿ