NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 56 of 172

higowarka gari?" Abba yai ajiyar zuciya yace "kawai!" Hassan yace "kawai? Taya Abba zaka taho nan bayan kasan Ummy dole tana jiranka? Ai tunda kake tafiya koda bana kula na tabbatar baka taba yin haka ba." Abba ya mike tsaye ya tako zuwa inda yake yasa hannu daya kan kafadarsa yace " kai fa?" Hassan yace "me?" Abbba yace "naji ni wannan karan ne kadai na tabayin haka kaifa? Kana kula da taka matar?" Hassan kallan mamaki yamai fuskarshi cike da mamaki yace " ban gane ba? Abba ya muna maganar Ummy kana zancen wata?" Abba yai murmushi yace "kai namiji ne kafin d'a na yanda nima nake namiji kafin na zama mahaifinka." Yanzu kam kallan zargi Hassan yama Abbansa yace "mekake nufi Abba?" Abba ya girgiza kai yace "nima bansani ba, kawai dai sanar dakai nai abinda nakeji." Hassan ya kalleshi baice komai ba, kawai ya juya zai fita. Abba yace "sai ka maidani gida koba d'aukata kazoyi ka kaima mahaifiyarka ba? Dama kai a rayuwarka damuwarta ita kadaice abinda ka sani." Hassan ya kalleshi kawai sannan ya juya ya shiga motar sa, zama yai yana tunanin kalaman Abba, me yake nufi? Fada sukai da Ummy? Shifa a duniya ran Ummynsa ne kadai bayasan yaga ya baci. Yana zaune sai ga Abban ya bude motarsa ya shiga gefensa. Hassan baice komai ba yaja suka fara tafiya.......... Su Ummy na kitchen itada Jalila suna aiki, Ameera ta tafi gidan Aunty Nana kai sako, Ummy sai mamakin kwarewa da Jalila tai a gunki take, wanda haryasa tace mata "Jalila nayi mamakin yanda kika iya girki a shekarunki." Jalila tai murmushi tace "ai kullum ni nake abinci a gida, daga na safe, na rana har na dare." Ummy tace "makarantar fa?" Jalila tace "ina zuwa." Ummy ta kalleta cikin jindadi sannan suka cigaba, suna cikin aikin sukaji muryar Abba yace "Amarya da kanki?" A tare suka juyo, Ummy ta kalleshi cikin kulawa sannan ta taho inda yake, Jalila kuwa sunkuyar dakai cikin kunya. Ummy ta karaso inda yake tace "Sannu da zuwa." Murmushi ya mata yace " yauwa." Sannan ya juya, Jalila ce ta juyo, hada ido sukai da Hassan wanda batama san tare suka shigo ba sai yanzu, kallanta yai sannan ya dauke idonsa daga kanta. Itakuwa kura mai ido tai zuciyarta na raya mata meke damunshi? A haka dai gashi garau sai ta tuno. Abinda yai jiya, tace da daddare kuma sai ya rikide? Ko inyai bacci? Alamar kamawar dataji ne yasa tai saurin kallan tukunyar sannan ta cigaba da girkinta. Shikuwa Hassan sai dayaje zai hau sama sannan ya sake juyowa ya kalleta, ya suka kare da mutanen dazu? Tsaki yai sannan yace "meye damuwata?" Sannan yahau sama. Dakinsa ya shiga kawai ya zauna akan gado. Ummy kuwa a daki ta kalli Abba da ya zauna akan kujera tace "gajiya ko?" Ya kalleta yace "a gajiye nake tilis naje gidana na governor road in huta danki ya taso ni." Tace "kamar ya?" Ya mike yana balle botiran jikin rigarsa yana cewa " bari nai wanka." Rigarsa ya cire ya shiga toilet da kallo ta bishi, danta? Hassan kenan dan Sagir tare suka fita da Ameera. A iya saninta Hassan kuma kamar abin da wuya, mikewa tai ta fito ta nufi kitchen. Jalila ta kalla tace "ko zaki kai mai abincin safe? Banaji ya karya." Jalila tace "Ummy azahar fa?" Ummy tai murmushi tace "haka yake, ni kaina ina mamakin yanda yake tauyewa cikinsa hakkinsa, kamar bai san darajarsa ba." Jalila tai shiru tana tunanin Goggonta wacce kullum take mata fada akan cin abinci, ashe ba ita kadai bace ga namijima da girmansa ana fama. Ummy ta kalleta tace "me kike tunani?" Jalila ta girgiza kai sannan ta nufi sama, a hankali ta tura kofar, sannan ta leko kanta. Yana tsaye jikin madubi daga shi sai dan towel, da sauri ta maida kofar ta rufe shi kuwa yana tsaye yana kallanta. Tana rufewa tai ajiyar zuciya tare dasa hannunta akan kirjinta tana maida numfashi, meye hakan? Taya katan namiji zai hau cire kaya haka? Kara tura kofar tai tana tunanin ai dole ya sa riga tunda dai yaga tana neman shigowa, gani tai ba kowa a dakin, baki ta tabe sannan ta shiga ciki tana cewa dole ai yaji kunya ya shige toilet. Motsi taji a bayanta ta juya da sauru bayanta, yanda yake dazu haka yake yana neman abu a cikin drawer, idanu ta zaro sannan tasa hannu ta rufe idanta da sauri. Shaver zai dauka yana ganinta ya dauka yazo ya wuce kamar baisan da mutum agun ba, toilet ya bude ya shiga. Jin karar rufe kofa yasa ta bude idanunta a hankali sannan ta kara sakin ajiyar zuciya tana cewa "Woah! Kamar bai ganni ba?" Kallan kofar toilet din tai sannan ta fito, ta sanarma Ummy, suna kammala girkin Ummy ta zuba a kula ta bata tace "ki hau muku dashi sama, Jalila ta dauka ta hau sama, itakam batasan hawa saman nan kwata kwata." Tana shiga ta taraddashi yana ninke sallaya, ya ajiye sannan ya kwanta tare da dauko littafin da yake karantawa. Abincin a ajiye ta dibi nata dan kadan ta fito falo. Yau gidan shiru kamar ba mutane, Ameera da Sagir basa nan, Ummy na daki ita da Abba shima waccan yana daki, sai ita kadai a f
🏠