ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 55 of 172

sanda ta iso gidan nan, ta tabbatar Bazasu taba ajiye Safeena su dauketa ba. Yanda take kallan Mumy ne yasa Inna tace" me kikeyi? Na dauka cewa nai muje ki rakamu." Zubewa akan gwiwowinta tai tana hawaye tace "Inna dan Allah na rokeki kiyi hakuri, zanyi komai amma dan Allah banda gurbin mahaifiyata." Inna ta kalli hanyar sama tace" me kike yi hakan? Salan wani ya ganki yace cutar dake mukeyi?" Jalila ta mike tana matse kwalla, Inna tace "muje." Haka suka sauko kasa tana bayansu. Ummy ta fito daga daki tace "har zaku tafi?" Mumy tace "eh wlh." Ummy ta kalli Jalila tace "Jalila ana kukan rabuwa ne?" Jalila ta sunkuyar dakai, Mumy tace " Ga tanan mun barmuku amana." Amana? Abinda ya darsuna zuciyar Jalila kenan, su basu riketa amana ba shine suke bada ita wai amana? Ummy taji tace "ai Jalila diyace agurina, insha Allahu yanda zan rike dan cikina haka zan riketa." Inna tace "mun gode sosai, Allah yabar zumunci, amma Taura fa?" Ummy tace " yana Abuja yau dai muke sa ransa." Sannan ta kalli Jalila tace "ki daina kuka dan Allah." Jalila ta daga kai tana share hawayenta. Haka suka fito Ummy ta mikoma Jalila leda tace " ki basu." Jalila ta amsa tama Ummy godiya. Sai da suka shiga mota sannan tamikama Mumy tace "tace gashi inji Ummy." Inna ta kalleta tace " ki tabbatar kinji abinda na fada miki." Jalila batace komai ba har motarsu, ta fita daga gidan, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata. Komawa cikin gida tai, wucewa dakinta tai kawai ta zauna tana kuka. Ummy ce ta shigo dakin, itakanta Ummy tun jiya hankalinta ba'a kwance yake ba ta nemi number Abba harta gaji, yanzu kuwa bama ta shiga gaba daya. Hannun Jalila ta kamo, tace "ya isa haka nan, insha Allahu bazakiyi dana sanin auranki cikin zuri'ata ba, Hassan na cikin wani yanayi ne sai dai ba haka Allah ya halliceshi ba, lalurace ta afkomai shekarun baya da suka wuce wanda muke addu'ar neman mai lafiya, da taimakon ki." Jalila ta kalli Ummy, Ummy tai murmushi tace "jiya a kasa kika kwana?" Jalila cikin mamaki tace "ya akai ki...." sai kuma tai shiru, Ummy tai murmushi tace " ya miki magana?" Jalila tace "hmm amma baifi sau hudu ba." Tace "Ba laifi dan banyi tunanin ma zai kula ki ba kwata kwata." Shiru tadanyi kafin ta kara riko hannun Jalila cikin murya mai rauni da tausayi tace "Jalila ki taimakeni." Jalila ta kalleta jiki a sanyaye, tace "Jalila ki taimakeni gun ceto Hassan daga halin da yake ciki." Jalila tai shiru sai kallanta da takeyi, Ummy tace "Kiyi hakuri da duk abinda zai miki ma tabbatar wata rana zakiyi mamakin shi" Jalila ta share kwallarta tace "Insha Allahu Ummy." Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace "Jalila nagode sosai, sannan karki bari ya wulakantaki, inya miki ba daidai ba ki fito ki fadamai, hakan ne zaisa ya saki jiki dake." Jalila tai shiru, Ummy tace "Sannan inaso duk wani abu da kikeso ko ya dameki ki sanar dani, inaso mu zama daya ni dake, yanda na dauki Ameera haka na daukeki, kema inaso ki daukeni a matsayin mahaifiyarki...." Kalmar mahaifiya itace ta sa jikinta yin sanyi, a ranta tace Goggo kina ina???? Ummy ce ta mike sannan tace " bari naje lokacin abincin rana yayi." Jalila ta mike da sauri tace "bari inyi abincin Ummy." Ummy tace "ah hb? Daga yin aure sai girki?" Jalila tace " dan Allah ki barni nayi." Ummy tace "muje muyi tare to, dan ina tunani Abbansu yau zai dawo." Haka suka sauko kasa abin sha'awa, sai dai zuciyar Jalila ciki take da tunani wanda take kokarin nemo ma kanta mafita." #OneLuv๐Ÿ’• ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* _ "There are three constants in life...change, choice and principles." -Stephen Covey_ (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *29* Abba suna shigowa garin kano yacema driver dinsa su wuce gidansa na governor road, driver din yayi mamaki dan Abba ya dade bai ko leka gidan ba, ko yazoma sai dai yai abu minti kadan ya fita. Yau kam suna isa ya shiga ciki ya kwanta a falonsa, hannunsa yasa asaman goshinsa yana tunani. Mamman driver ya juya ya fita da mota, yana kokarin shiga layinsu shi kuma lokacin ne Hassan ya fito shima. Ganin motar Abba yasa ya danyi parking, Maman ya bude motar da sauri ya matso jikin window din da yake zaune, Hassan ya zuge glass din sannan ya kalleshi. Mamman ya gaisheshi, bai amsa ba yace "Ina Abban?" Mamman yai shiru kafin yace "Yallabai na gidansa na governor road." Kallan mamaki yamai yace " me yake acan?" Yace "ban sani ba wlh, kawai cewa yai in kaishe." Hassan ya tada motarsa yai gaba, direct gidan ya wuce ya shiga ciki. Kofar falon yai knocking sannan ya tura ta, Abba me kwanc akan doguwar kujerar dake falon, shima Abban jin motsin kofa yasa ya bude idanunsa. Hassan na tsaye a jikin kofar yana kallansa, Abba ya kalli Hassan sannan ya mike zaune yace "Hassan?" Hassan yana daga jikin kofar yace "me kake anan daga s
๐Ÿ