NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 51 of 172

h dana shigo ciki ne matata ta dage akan sai na kiraka kaci abinci shiyasa nace Zaliha ta kiraka." Yace "meyasa to baka fadamin gidanka bane?" Yace "banasan ne kaji ba dadi, haba Taura dan Allah kayi hakuri." Kashe wayar yai sannan yai cilli da ita kan gado, ya rasa me yasa yarinyar ta tsayamai a ransa...... *********** A can gidansu Hassan Kuwa jalila tana zaune a dakinsu Ameera, har wajen karfe 10, Ameera ta kalleta tace "ki tashi kije ki kwanta kafin Ummy tai magana." Jalila tai ajiyar zuciya sannan tace "bazan iya kwana anan ba ko?" Ameera da sauri tace "a ina? Ba ruwana wlh." Jalila ta kara yin ajiyar zuciya sannan ta mike, ta fito. Haka ta haura sama jiki a sanyaye, hannu tasa a hankali ta murda kofar dakin, yana kwance akan gado yana karatu. Kamar munafuka haka ta shiga cikin dakin, ko kallanta baiyi ba ya cigaba da karatunsa. Jalila tana tsaye har kusan minti ashirin, jitai kafafunta sun gaji nan ta matso kusa da gadon kadan, ta karasa kan kujerar dake dakin ta zauna tana dan matsar da littatafan dake jere agun. Jitai ance "karki kuskura ki hargitsamin abu, komai da kika gani agun a jere yake." Baki tadan tabe sannan ta daina taba litattafan, dama haushi yakeji dalilinta duk an canzamai tsarin dakinsa. Shiru ne ya kara ratsa dakin sai sanyin Ac dake kara sanyaya dakin. Bacci ne ya fara kamata dan har 11 ta wuce, tana zaune tana tunanin Goggonta. Ganin bashida niyyar fadamata inda zata kwanta yasa ta mike ta dau pillow din dake gefensa sannan tazo tana san daukan bargon dake kan gadon. Kafafunsa ne akai ta kalleshi tace "zan dan dauka." Kallanta yai yace "banaji naki ne." Tace "a ina zan kwanta?" Alama ya mata da kasa da hannunsa ba tare da ya dauke kafarsa ba. Jalila haushi ya kamata, harararsa tai cikin takaici, sannan ta sa pillow ta kwanta a kasa, ai bayau ta saba kwanan kasa ba, dama saboda sanyi takesan luluba. Shikuwa bai kalleta ba sai dai ya tabbatar ta harareshi dan ya kula idanunta sun kware da harara sannan bakinta ya kware da murguda a bayan fage. Kwanciya tai ta lulube kafarta da zani, bacci ne yai gaba da ita....... Kallanta yai sannan shima ya juya ya kwanta, abinda zai baka haushi bafa luluba zaiyi da bargon ba haka kawai......... Wajen asuba ya farka, yai hamdaka da samun bacci mai kyau dayai, dan dama ba kullum abin tashi ba. Dome light din dakin ya kunna sannan ya mike. Alwala yai sannan ya dauko sallaya zai shimfida, kallan Jalila yai tana kwance a inda yake shimfida sallayarsa, bacci take sosai kafa yasa ya zunguri kafarta. Kara gyara kwanciya tai, ya kara sa kafa ya dan kara zungurar kafar tata, a hankali ta bude idanunta. Ganin namiji tai a kanta da doguwar riga fara, tsorata tai, da sauri tai baya tare da yin ihu, tace wayyo Allah...... Da sauri ya rufota ya rufe mata baki, yace meye hakan? Sai alokacin ta tuna ashe fa wai a wani gidan take, sannan daki daya da namiji. Shiru tai sannan ta kalleshi, shima kallanta yai sannan ya mike yace " bakiji kiran sallah ba?" Tai shiru, dan batasan me zatace ba. Mikewa tai ta nufi ban toilet. ******** Inna ce ta kalli Dady tace "bazaka iya ba?" Yace "ba wai bazan iya bane sai dai banga dalilin dazaisa a dauketa daga asibitin da take ba zuwa wani ba." Ranta a bace tace "kayi abinda na saka kawai, ko kana tunanin zan cuceta ne?" Kallanta yai yace "ba haka nake nufi ba." Tace " kamaida ita Premier m, sannan kasa a gyara mata bangarenta, asa mata duk wani abu da ya kamata." Mamaki ya kamashi, a canza mata asibiti sannan a gyara mata bangarenta? Ya tabbatar wani abun take shiryawa na cigabanta ko na cigaban yarta. Bai musa ba yace to sannan ya mike ya fita. Shiru tai tana tunani........ #OneLuv💕 ********** 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *27* Dady na fita daga dakin ta dau waya ta kira Mumy. Mumy na shigowa ta kalleta tace “ki shirya muje ganin daki.” Mumy tace “ganin daki kamar ya?” Inna tace “ au a aurar da yarki guda? Sannan babbar jika a gareni ina tunanin ya zama dole muje bayan an kaita muga muhallinta.” Mumy tai yar dariya tace “Lalai Inna, jikarki? Ni dai a kara za’a iya cewa ‘yatace amma Inna ke ai......” Kallanta tai fuska a d’aure tace “ me kike nufi?” Mumy tace “Inna ai kece bangane me kike nufi ba.” Inna ta ajiye wayarta sannan ta mike tace “ na rasa sai yaushe ne kwakwalwarki zata fara aiki yanda ya kamata.” Mumy ta mata kallan rashin fahimta, Inna tace “nikam wacece babbar ‘yarki?” Tace “Safeena mana.” Inna ta kalleta cikin takaici tace “wacece babbar yarki?” Mumy tace “ni Inna rudani kikeyi.” Inna ta harareta sannan ta girgiza kai cikin takaici tace “ni wuce muje ki shirya mu tafi, ni in munje gidan na miki bayani.” Mumy ta mike ta fita tana tunanin kalaman Inna, batagane w
🏠