ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 49 of 172

janu? Hauka? Abinda ya fado mata arai kenan, Ummy tace "Hassan nada larura wanda mu kanmu iyayensa bamu sani ba, haka kawai tundaga mutuwar dan uwansa da dan kanin mijina Hassan ya koma haka, duk yanda mukaso musan matsalarsa mun kasa, munje asibitoci kala kala sai dai maganar daya ce, ba abinda ke damun kwakwalwarsa sai dai bamu san meke damunsa ba." Ummy ta juyo tare da goge kwallarta tace "Jalila ki yafe mana wannan laifin da muka aikata." Ganin Matar da ta sani a rana d'aya tana share kwalla sai taji gaba daya hankalinta ya tashi, batasan sanda tace "Bakomai na yafe muku." Ummy ta kalleta cikin jin dade sannan ta kara riko hannunta tace " jikina yana bani ke alhere ce a gareshi da mu kanmu, daga sanda naganki hankalina ya kwanta dake, Jalila ki daukeni a matsayin mahaifiyarki, ni kuma zan yi miki duk wani abu da uwa takema danta." Jalila tai murmushin jin dadi, dan haka kawai taji tanasan matar, dazu kukanta kadai yasa hankalinta tashi. Ummy ta kalleta tace "wa aka kwantar a asibiti?" Jalila ta kalleta idanunta suka ciciko, a hankali hawaye ya fara zubo mata. Ummy hankalinta ya tashi tace "ya isa haka nan Jalila, bazan kara tambayarki ba harsai sanda hankalinki ya kwanta da ki sanarmin." Jalila share hawaye kawai take, Ummy ta mike tace "tashi kije dakin nasan abu zakiyi na tsayar dake." Jalila ta dago sannan ta mike, sama ta fara hawa, Ummy taji tace "dakin kusa da wanda aka kaiki jiya zaki shiga. Jalila tace to, nan ta tura kofar dakin, sanyin Ac dake kadawa a dakin da wani sansanyan turare ne suka bugeta, idanu ta lumshe a hankali sannan ta kalli dakin, yanayin kan madubin kadai yasa tasan dakin hade yake da namiji. Da sauri ta fito ta nufi dakin data shiga jiya, jin dakin tai a kulle, komawa tai dakin ta bude wardrobe gefe daya kayanta ne kaf, dayan kuma na namiji. Daki daya zasu zauna kenan? Inners dinta ta ciro sannan ta shiga wanka, kamar ba dakin namiji ba dan komai nashi a tsars suke, haka ta fito ta saka wata doguwar riga sannan ta kwanta agefen gadon, tana tunanin rayuwa, tabbas itakam zata fadama Ummy matsalar Goggo dan bazata iya kwana biyu ba bata ganta ba. Ta tabbatar Ummy zata fahimceta. Batasan bacci yayi gaba da ita ba, dan dama in tana zazzabi ta dinga bacci kenan, tsabar bacci ya mata dadi har da kara kwanciya, sanyin Ac din yasa ta jawo bargo. Bacci take hankalinta a kwance. Kofar dakin ya turo, gaba daya shi gidan ma baya san zama, tunda ya fita yana cikin mota a zaune. Sai yanzu daya gangaro gida, ganin magrib tayi, ya tabbatar Ummy yanzu zata shiga nemansa. Cak ya tsaya a kofar dakin yana kallan ikon Allah, tunda yake yau ne rana ta farko da wani ya taba bajemai akan gado haka, harda jan bargo? Ransa ne ya turnuko dan shi sam bayasan yaga wani a dakinsa, kusa da ita ya matso ya sa hannu ya fizgi bargon da karfi. Jan bargon da yai yasa ya hado da kasan doguwar rigarta yadan kwaye ta. Da sauri ta bude idanu, kallansa tai a zabure, shima idanunsa ne suka kai kasanta daya kwaye, da sauri ya dauke kansa, ita kuma ta mike zaune da sauri tana gyara rigarta tace "Malam me kenan?" Kallanta yai yace "Malam? Malam me kenan?" Bakinta na rawa tace " Umm." Ya hade rai yace "will you get up?" Kallansa tai cikin rashin fahimta, yace " bakyajin yaren?" Nan ma tai shiru, yace "banasan magana please tashimin daga kan gado." Jalila ta kalleshi tace " dan zaka ce in tashi sai ka min haka?" Wani kallo ya buga mata wanda batasan sanda ta mike ba, yace "a haka kika gadon?" A ranta tace "ahh yau ga wani irin mutum." Kallanta yai sannan ya kalli gadan, Jalila ta fara gyara gadan da karfi kana gani kasan na mugunta takeyi, tana yi tana dan murguda baki. Kallanta yai a ransa yace wannan kana gani kasan batada kunya wannan bakin sai ba fasashi wata rana. Jalila kuwa tana gyara wa tana cewa yo matsala ma ai basai an tambaya ba, mutum ba mutunci ai babbar matsalace. #OneLuv๐Ÿ’• ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *26* Toilet ya shiga ya d'auro alwala, yana fitowa ya kalleta, tana tsaye tsuru dan itama jiransa take ya fito, ga fitsari ya matseta. Tana gani ya fito ta shiga ciki, kallan kofar data rufo yai ransa ya kara baci dan bakin cikinsa ya ganta a dakin nan. Tada sallah yai, bayan ya idar ya zauna ya fara addu'oinsa, itakam daga gefe ta dan rakube tai sallah, tana idarsa ta zauna agun tana yima Goggonta addu'a. Ameera ce ta buga musu kofa tana cewa "Yaya Jalila ki fito kici abinci" Juyowa yai ya kalleta ransa a bace, mikewa tai da sauri zata bude kofar. Batasan ya mike ba sai gani tai ya rigata sa hannu ajikin kofar. Kallansa tai yanda taga idanunsa sunyi yasa taji tsoro. Da karfi ya bude kofar sannan ya kalli Ameera. A tsorace Ameera tace "Yaya kana nan?" Kallanta ya sakeyi,ba sai ya mata magana ba tasan me yake nu
๐Ÿ