tai ta kalleshi idanunta sun canza suna neman yin kuka.
Yace "Jalila wacece dazu a asibiti?"
Tace " me kake so ka sani?"
Yace "Kina nufin haka zamu zauna ko magana bakyasan ta hadamu?"
Kallansa tai zuciyarta na kuna, sannan ta juya da sauri ta banko kofar.
Hannu tasa ta rufe fuskarta saboda bakin ciki, wasu hawaye ne suka gangaro mata, ba santa yake ba, ta tabbatar yanzu kila kawai tausayin halin da ya ganta yakeyi.
Sagir tsayawa yai ajikin kofar tare da kurama kofar ido kamar tana gun, sannan ya juya jiki a sanyaye.
Yana neman fita yaji Ameera nacewa "Ya Sagir!"
Juyowa yai ya kalleta, yana tsaye harta karasa gangarowa daga saman benan, ta matso gunsa tace "ina zaka?"
Leda ya mika mata yace "Gashi kiba matar Yaya."
Amsa tai tana cewa "menene ya Sagir? Sam ka canza gaba daya yanzu bakasan magana sosai."
Murmushi yai na dole yace "Ummy fa?"
Ta nuna sama da hannu tace "tana sama" sannan ta matso kusa dashi sosai alamar rada tace "Ummy fa ta dage sai yaya ya amince da matarsa."
Sagir ya kalleta yace "bangane ba...."
Tace "tana sama tana hada musu daki daya."
Wani abu ne yaji ya harba kirjinsa me kake tunani Sagir? Abinda wata zuciyar ta tambayeshi kenan?.
kallanta yai yace "haba."
Dakyar yai maganar, tace "Ai Ummy ta dage wannan karan."
Harararta har sannan ya ture kanta yace "yaushe kika zama mara kunya? Wato harkin fassara zamansu a daki daya kena?"
Tace " ko yaro dan shekara sha biyar ai yasan me ake nufi a wannan lokacin."
Buge kafadarta yazoyi ta zille da sauri yace "Ameera? Kece kuwa?"
Dariya tasa tace "ni ba ruwana Ya Sagir."
Da kallo ya bita yana murmushi harta shige daki, tana shiga yanayin fuskarsa ya canza, daki daya? Wata zuciyarce ta kara cewa me kake tunani ne wai? Daga lokacin da aka daura aure ai kaima kasan abinda ya kamata.
Juyawa yai jiki a sanyaye ya fita.
Tana zaune tana kuka Ameera ta turo kofar, da sauri ta goge hawayenta, Ameera ta kalleta tace "jikin ne?"
Kai ta daga alamar a'a sannan tace "Sunanki Ameera ko?"
Tace eh, Jalila tace "ni sunana Jalila."
Ameera tace "na sani."
Jalila tai murmushi tace "Oh, yahkuri."
Ameera ta kalleta tace "Ummy ce ta fadamin, sannan na gani a katin daurin aure."
Jalila ta jinjina kai, Ameera ta mika mata ledar tace "gashi inji Ya Sagir, ah bakisanshi ba ko?"
Jalila ta kalleta batace komai ba, Ameera tace "shine kanin Yaya, daga shi sai ni, mu uku ne."
Jalila tace "Yaya?"
Ameera tace "Ya Hassan fa nake nufi mijinki."
Jalila batasan sanda tai wata dariya ba wace ni kaina bansan irinta ba, miji? Mijin da sai yanzu ma tasan sunansa?
Kallanta tai a ranta tace Husainin fa? Tace Hassan sannan tace Sagir.
Kamar Ameera tasan me take tunani tace "ya rasu, dan uwan nasa."
Jalila ta kalleta tace "Ayya Allah ya jikansa."
Ameera ta ajiye ledar tana cewa Ameen.
Jalila ta dau maganin tasha.
Jalila can tace "wanka nakesan yi kayana fa dan Allah?"
Ameera tace "muje sama."
Jalila ta mike ba tare da ta musa ba, Ummy na saukowa suna fitowa, Ummy ta kallesu murmushi tai sannan tace "Jalila kin mike?"
Kai ta daga tare da sunkuyawa, tsugunawa sukaga tayi tace "Ina wuni."
Ummy tasa hannu ta dagata sannan tace "ke da bakida lafiya?"
Jalila kanta na kasa, Ummy tai murmushi sannan ta kamo hannunta, maimakon su hau sama sai ta riketa zuwa falo.
Ameera ta kalla tace "Ameera asa mana abincin dare."
Ameera tace "Ummy yau ma nice?"
Ummy tace "ai na fada miki dama, daga kin shiga aji shida shikenan girki ya kamaki, yanzu kuwa kunyi hutun canjin aji kinga kuwa a matsayin yar aji 6 kike."
Ameera ta shagwabe fuska ta nufi kitchen ranta ba dadi, ita kam tana ganin ya kamata a samarmusu mai aikin yin abinci amma taki, mai musu aiki ma suna gama gyara gidan suke tafiya sai kuma gobe.
Ummy ta maido da hankalinta kan Jalila ta zauna sannan ta zaunar fa ita a gefen ta.
Jalila ta zauna a darare, Ummy ta riko hannunta tace "Jalila!"
Jalila ta kalleta kadan sannan ta maida kanta kasa tana kallan yanda Ummy take rike da hannunta, Ummy tace " ya jikin naki?"
Jalila tace Da sauki.
Ummy tai shiru kafin tace "da rokonki nake san yi."
Jalila ta kalleta da sauri tana san jin menene, sai dai bazata iya dadewa tana kallanta ba, da sauri ta maida idanunta kasa.
Ummy tace "rokonki zanyi akan ki saki jikinki da mu, ki maida gidan nan kamar gidan ku koma sama da gidanku, nasan zama da iyayen miji ba abune dayake da dadi ba, abu ne mai wahala tun balle ga yarinya, sai dai mu lalurace tasa muke sanki anan gidan, sannan bawai dan mu cutar dake bane sai dan muna ganin in kina kusa damu hankalinki da namu sai yafi kwanciya."
Lalura? Abinda yazo mata a ranta kenan sai dai batace komai ba har Ummy tace "Jalila mun miki laifi wanda nikaina nasan bamu kyauta miki ba."
Jalila ta kalleta tace "Laifin me?"
Ummy ta saki hannunta sannan jiki a sanyaye tace "mun miki laifi gun b'oyemiki larurar Hassan."
Kallanta tai sannan ta tuno sanda ya fadi akan titin nan, al