a bazata taba wulakanta ba indai har Ummy na nan, kaf a duniya shi agunsa bai taba ganin mace kamar Ummy ba.
Ameera ce ta shigo da tiren abincin, Ummy tace "zubo mata dankalin kadan"
Ameera ta zuba mata ta mika ma Ummy, da kanta ta gyara mata zama sannan ta mika mata abinci, kallan mamaki Jalila take mata, bata taba tunanin zata samu kulawa haka ba, balle daga zuwanta ko sanin ta ba'ai ba.
Haka ta dinga dan ci dan samon kanta tai da kasa yima Ummy musu, sai data gama Ummy ta miko mata magani da ruwa.
Sai data sha, sannan Ummy tace karki kwanta kidan jira abincin ya tsirga miki kadan sai ki kwanta.
Jalila ta d'aga kai, sannan ta maida idanta kasa.
Ummy tai murmushi ta fita.
Ameera ta mike ta biyota.
Sagir na zaune a falon suka fito, yace "Ummy na!"
Tace " Sagir sannu da kokari."
Yai murmushi sannan yace "Ina Yaya yaje? Naga ya fita yanzu."
Yanayin fuskarta ne ya canza, tace "yaushe rabon da insan inda Hassan zaije?"
Sagir yai shiru dan ya fahimci yayi laifin tambayarta, Ameera ya kalla yace "Ashe kawarki ta koma gida?"
Ta dan turo baki tace "sai yanzu ma ka kula?"
Yace "kinsan dazu muna kan Jalila sam ban kula ba."
Ya mike yai kitchen.
Ameera ta kalli Ummy tace "Ummy nikam dazu a asibiti, na rasa wa taje dubawa."
Ummy tace wa kenan?
Ameera tace "matar yaya."
Ummy tace "ya sunanta ita matar yayan?"
Ameera ta kalleta tace "Ja....."
Kallan da Ummy ta mata ne yasa tai saurin cewa "Yaya Jalila."
Ummy tace "me ya faru?"
Sagir ne yai saurin katseta yace "to uwar gulma, ki bari ita Ummyn ta tambayeta da kanta mana."
Ameera ta turo baki, Ummy tace "Sagir ya akai?"
Hannunsa rike da plate din da ya zubo abinci ya zauna akan dinning yana cewa "Wlh nima bansan wacece a asibitin ba Ummy, sai dai yanda hankalinta ya tashi da alama mai mahimmancice a gareta....."
Ummy tace " shikenan, zan tambayeta."
Sagir shiru yai ya kasa ko kai loma d'aya bakinsa, tunawa yai sanda suna zance da Jalila a makaranta yawanci in zatai abu zai ji tace ai Goggo kaza, ai Goggo kaza.
Kallan Ummy yai da sauri yace "Ummy wannan matar data kawo Jalila itace "Mahaifiyarta?"
Ummy tace "eh mana."
Sagir yai shiru can yace "me suke ce mata?"
Ummy tai murmushi tace "ina fa na sani? Dan jarida?"
A tare sukai dariya
^********^
Jalila tayi bacci sosai dan sai azahar ta tashi, Ameera na dakin tana sa kaya sanda Jalila ta farka.
Kallan Agoggo tai sannann ta mike da kyar ta kalli Ameera tace "Dan Allah zanyi alwala."
Ameera tace "ki shiga ga toilet."
Jalila ta mike tai alwala, Tana idar da sallah Ameera tace mata ga abinci nan kici, Jalila tace "banajin yunwa.
Bata sake mata magana ba, ta karasa kwalliyarta dan fita zatai ta fito daga d'akin.
D'akin Ummy ta shiga tana zaune tana ta kiran number Abba, tun safe take ta ringing amma no answer.
Ameera ta shigo tace "Ummy dawa zan kai sakon gidan Aunty Nanan?"
Ummy tace " dama abin gara ne, gashi ba driver a gidan, ki duba ko Sagir nanan."
Har ta juya Ummy tace " yayar taki ta tashi ne?"
Tace "eh tayi sallah ma."
Ummy ta mike ta fito tare da ajiye wayar.
Sama ta hau dan taji alamar dawowar Hassan dazu, dakin ta kwankwasa.
Yana kan sallaya rike da littafin Riyadul Salihin, ajiyewa yai ya bude kofar.
Kallansa tai tace "Hassan ya jikin matar taka?"
Kallanta yai yace "Ummy ni ai banganta ba?"
Tace " baka ganta ba? Tana ina kenan?"
Yace "ina na sani ni ai tun da suka fita ban kara ganinta ba."
Tace "ko?"
Baice komai ba sai kallan mamaki da yake mata, Ummy me take mai haka? A iya saninsa batasan abinda zai bata mai rai, sannan ko magana zatamai a cikin sanyi take mai.
Kallanta yai yace "Ummy na kasa gane me ke faruwa, kince na amince da auran nan na amince ba tare da na musa ba, yanzu kuma gaba daya kin canza."
Kallansa tai, yanayin fuskarta ya canza, abinda bataso dan ta kula in tama Hassan lago lago tabbas yarinyar nan zata kuntata a gunsa.
Tace "Hassan ko kare ne aka baka shi akace ma gashi an baka shi, baka tunanin ya zama hakkinka ka kula dashi? In har kasa hannu ka amsa a iya tunani na dolene ka bashi hakkinsa, Hassan dabba ma kenan, balle dan adam, dan adam din ma mace mai rauni, yarinya karama."
Kallanta yai baice komai ba, tace " yanzu da ace gidanku daban kenan haka zaka barta har ciwo ya mata illa?"
Hassan ya kalleta yace "ba gaku nan ba,Ummy? Na tabbatar abinda zaku mata ni bazan mata ba."
Tace "Hassan zuciyarka ma ta fara rikidewa?"
Kallanta yai sannan ya kauda kai gefe, tace " a iya sanina yarona mutum ne mai tausayi da kula da abinda yake nasa da wanda ba nashi ba, Hassan yaushe zuciyarka ta fara rikidewa zuwa rashin tausayi?"
Shiru yai jikinsa yai sanyi bai ce komai ba, tace " na haramta mata kwana a d'akinta, daga ranar jiya Hassan ko me zai faru in ganta a d'akin nan.
Yace "Ummy...."
Tace "zan kulle d'akinta ne ma in tafi da makullin, zan sa Ameera ta dawo da kayan sawarta nan dakin."
Ran Hassan ya baci sai dai bai iya cewa komai ba