NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 44 of 172

*Ayusher Muhd* _Gaisuwa Gareku 'yan Jalila Fans, nagode sosai, ba shakka ina alfahari da yanda kuka cika grp din cikin lokaci kadan.....Thanks for the love_ *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 23* Har yasa hannu zai bude dakin nata, sai kuma naga ya maida hannunsa, komawa yai d'akinsa, yana shiga ya rufe. Bandaki ya shiga yai wanka sannan ya kwanta. Jalila kuwa tayi gurum a d'aki, tana nan a zaune, da kyar ta iya tashi tai fitsarin da ya matseta. Shiru tai tana tunanin abinda ke faruwa, Goggo! Hawaye ne ya zubo mata, haka ta kishingida a kan gado har bacci yai gaba da ita. Zazzabi ne ya kara hawa mata, wajen asuba ta farka. Haka tai ta karkarwar sanyi har aka shiga sallah, da kyar ta mike tai sallah sannan ta samu ta kara kwanciya. Sai wajen karfe 10 Ummy ta turo Ameera dan kai musu abincin safe. Yanda taga Jalila ne yasa tasan ba lafiya ba, a ranta tace ko first night din ne? Ameera ta daure ta mika mata tiren tace "Ga breakfast dinku." Jalila kuwa da kyar ta iya cewa "Banajin yunwa nikam." Yanda taga Jalila tayi ne yasata saurin cewa "Lafiyarki kalau kuwa?" Jalila tace "bana d'anjin dadi ne." Cikin mamaki Ameera tace "ina yayan?" Jalila ta girgiza kai alamar bata sani ba. Da sauri Ameera ta ajiye tiren ta sauka kasa da gudu. Ummy na zaune akan dinning itada Sagir tana tambayarsa menene dan ta kula jiya sai dare sosai ya dawo, sannan yanzu ma taga yana kokarin fita shine ta sashi zaman cin abincin dole. Ameera ce tazo da sauri tace "Ummy batada lafiya fa." Ummy tace "wa? Jalila?" Sagir ne ya mike da sauri, a rikice ya haura saman. Tana kwance sharkab a kasa hankalinsa yayai mugun tashi, har yakai hannu zai dagota sai ya fasa, da sauri ya fito yana yina Ummy magana da karfi. Ummy kizo, Ummy. Ummy da itama take ta sauri ta shigo d'akin hankalinta a tashe. A kasa suka ganta. Ummy ta rungumota jikinta, zafin da jikinta ya dauka ne yasa hankalinta ya tashi. Ta kalli Sagir rai a bace tace "buga mai kofa." Sagir ya mike ya nufi dakin Hassan. Yana kwance akan sallaya yanajin lecture na Sheik Ahmad Deedat, jin knocking yasa ya mike ya bude kofar. Sagir ya kalleshi yace "kazo." Haka kawai yace ya juya, bai musa ba yabi bayan Sagir, gani yai ya shiga d'akin sa na da. A bakin kofar ya tsaya, Jalila ya gani a kwance a jikin Ummy. "Ummy!" Kallansa tai rai a bace tace "Hassan me kenan?" Yace "me ya faru?" Sagir ta kalla, tace "Sagir muje akaita asibiti." Sagir da sauri yai waje, duk ya rikice, gani yake kamar duk laifinsa ne. Ummce y ta kalleshi tace "ni zan kaita mota?" Karasowa yai ya d'agata. Jin an d'agata yasa ta bude ido a hankali, kallansa kawai tai sannan ta maida idan ta rufe dan wani irin jiri take ji. Shikam fuskar nan a hade ya ajiye ta a bayan mota. Ummy ce ta fito itada Ameera ta kalli Sagir tace "Sagir ku kaita asibitin, sai muje ya ake ciki." Yace to, sannan ya shiga mota. Ko kallan Hassan batai ba ta juya ciki. Sagir ya kalleshi yace "Yaya mu tafi?" Yace "kuje ni banasan asibiti ka sani, amma me ya sameta?" Ameera tace "Yaya aikai za'a......" Kallan daya mata ne yasa ta guntse maganar ta, juyawa yai kawai yai ciki. Sagir ya kalli Jalila dake cikin mota, shiga motar yai yaja suka fara tafiya. Ameera tace "muje Standard tunda yafi kusa." Bai musa ba ya wuce, Ameera ta kalleshi tace "Yaya menene? Naga hankalinka a tashe." Kai ya girgiza kawai baice komai ba. Shiru sukai har suka isa asibitin. Ameera ce ta kamata suka shiga ciki. Sagir yaje a ciro musu file, yace Ameera ta zaunar da Jalila. Jalila ta kalli Ameera tace "Dan Allah zan hau sama." Ameera cikin mamaki tace "me zakiyi?" Jalila tana numfashi sama sama tace "Dan Allah ki rakani." Ganin yanda ta damu yasa ta rike hannuunta suka hau sama. Suna zuwa kusa da dakin Goggo, Jalila ta zare hannunta daga cikin na Ameera sannan ta tura kofar d'akin. Goggo na kwance tana bacci, Jalila ta shiga. Ameera cikin mamaki itama ta shiga d'akin ta tsaya a jikin kofa. Jalila ta karasa kusa da gadon Goggo sannan ta riko hannunta. Wasu hawayene suka taho mata, Goggo ta bude idanunta jin an riketa, kallan mamaki tama Jalila tace "Jalila kece?" Jalila tace "in ba ni ba wacece Goggo na?" Goggo tai dariya tace "wato dana ce ki zauna a gida ki huta kasa zama kikai ko?" Tace "ina zan iya zama banganki ba?" Goggo ta kara riko hannunta da sauri ta mike zaune sannan tasa hannunta a goshinta tace "Jalila! Bakida hankali ne? Kina irin wannan zazzabin kika fito?" Jalila tai murmushin yake tace "karki damu Goggo ba wani wahala yake ban ba." Goggo tace "ga wanda bai kalleki ba kenan, duk kin rame a dan kwana biyun da ban ganki ba?" Jalila tai kasa da kanta. Ameera ta kalla sannan ta kalli Jalila, tace "wannan fa?" Ameera ta matso ta gaisheta sannan tace " ni kanwar yaya......" Da sauri Jalila tace "kawatace Goggo, biyoni tai dan ta gaisheki
🏠