ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 43 of 172

wayenta su Zahra basu sani ba, ko Mahaifiyarta bata sani ba. Haka ta fito, jikinta na kara tsuma wani sabon tsoro da fargabar rayuwarta na kamata. Sukam mutane kowa ko a jikinsa, Mumy na rike da ita suka shiga. A gidan kuwa, Ameerra da Aina'u suna zaune a d'akinsu sunyi shiru, Ameera tace "Aina'u inaji ta iso naji guda." Aina'u ta kalleta cikin takaici tace "Ameera me yasa iyayenmu basa duba abinda ya kamata? Kowa yasan tun ina SS1 nakesan Yaya, ni nace bandamu da matsalarsa ba tunda dai nasan ba hauka gareshi ba, me yasa ba wanda ya duba zuciyata? Ba ruwan kowa da damuwa ta?" Ameera tai tsaki tace "nima Allah naji haushi, ita wannan din dame ta fiki daya sa su Ummy mantawa da ke?" Aina'u tai kwafa tace "ni yau ma zan bi Umma mu tafi." Ameera ta ce "haba dai?" Mikewa tai ta shiga toilet dan bata san jin gudar nan." Aunty Nana kam ta baza ido tana san ganin wacece matar Hassan, Ummy ta kalleta tace "Dan Allah karki bude mata fuska sai ta zauna." Aunty Nana tace "ni rikota kawai zanyi bance wani abu ba." Haka akai ta hawa sana ana ganin tsarin gidan, kowa sai ya yaba sai dai dayake bakin ciki suke. Jalila na zaune a kasa, kanta na kasa tana hawaye. Ummy ta d'agota tace "akaita sama. Nan Aunty Nana ta taso da sauri ta riketa, haka ta kaita d'akinta sannan ta bude mata mayafi, shiru tai tana mamaki dan gaskiya bata taba tunani....... Ummy ce ta dafata sannan ta rufema Jalila fuska tace " muje waje." Fita sukai a falo, Aunty Nana ta riko Ummy tace "kun tabbatar dai yarinyar batada wata matsala ko? Ko halayen banza, kinsan wasu yaran a ido baka ganewa amma a fili sai kiga wasu iyayensu ma sun gagaresu ne." Unmy takaici ya kamata tace " ba yanzu zaku tafi bane? Naga duk an fara watsewa." Aunty Nana ta tabe baki tace "ba sai kin kuremu ba." Haka ta sauko tana mamaki. Sagir kam yana maidasu gida yai cikin gari. Ummy na zaune sai kiran wayar Hassan takeyi, sai datai ringing har ta katse sau biyu sannan ya d'auka. Ummy tace "Hassan kana ina?" Yace "waje." Tace "ka dawo gida dan Allah, kaga duk an watse sannan an bar yarinya ita kadai tun dazu." Yace " to in ina nan ma me zan mata?" Ummy tace "nidai ka dawo yanzu." Ta katse wayar tana kallan Abba wanda ya shigo yanzu. Hassan na ajiye wayar yau shiru, can ya tada motarsa ya taho gida. Jalila na zaune gurum ba kowa a d'akin, har ta gaji da kukan tayi shiru, sai dai fuskarta a rufe take. Ummy ce ta fito daga daki ta shiga dakinsu Ameera ta kalleta tana assignment, tace "Ameera tashi kije gun Yayarki kafin Hassan ya dawo." Ameera ta turo baki tace "inje in mata me?" Ummy ta hade fuska hakan yasata mikewa ba tare da ta kara cewa komai ba. A zaune take akan gado Ameera ta shiga, sallamarta ta amsa. Ameera ta shiga dakin tana cewa "ki cire mayafin kisha iska tunda ba kowa." Jalila tace " bakomai hakan ma" Ameera ta zauna akan kujera tana latse latse waya. Haka suka zauna shiru kamar ba kowa a dakin. Sai wajen karfe goma da rabi dan har Jalila ta fara gyangyadi, taji karar bude kofar dakin. Ameer ta mie da sauri tace "Yaya." Kallanta yai sannan yai mata murmushi. Mikewa tai ta fita, Ummy ta gani a kasan beni tace "ina ya shiga?" Tace "dakinta." Ummy tai ajiyar zuciya dan sai data mai magana yanzu akan lalai fa dakinta zai shiga ba nashi ba. Zama yai akan kujerar da Ameera ta tashi, sannan ya kalli inda take a zaune, bai damu yasan yanayinta ba, balle kamaninta. Ita kuwa tunda taji Ameera tace "Yaya!"gabanta ke faduwa. Dakin ya sake yin wani shirun, jitai wuyanta yana neman sagewa. Hassan ya kara kallanta, batada niyyar yaye mayafin ne ko me? Ba dai aikinsa bane? Daga inda yake yace " ki zare mayafin ki kwanta inkinyi sallah, in bakiyi ba ki tashi kiyi." Abinda ya fada kenan, ya mike zai fita. Har ya bude kofa zai fita sai idanunsa suka kalli ledar da Abba ya bashi. Kara maida kofar yai ya rufe, ita kuma ta dauka ya fita ne jin rufa kofa sau biyu. Yaye mayafin tai sannan tai wata ajiyar zuciya. Idanunta ne ya sauka a cikin nasa, gabanta ne ya shiga faduwa, sai dai yanda yake kallanta yasa ta kasa dauke idanunta. Kamar yasan fuskar nan, a ina? Idanun Jalila ne suka firfito, juya baya tai da sauri. Hassan ya matso ya d'au ledar ya mika mata. Ganin bata ganinsa yasa ya ajiye a kasa ya juya. Jalila tana jin ya fita ta juyo tare da ajiyar zuciya. Hassan yayi shiru a dakinsa yana tunani, ina ya santa? Wayar Ummy ce ta shigo, kallan wayar yai hartai ringing uku sannan ya d'aga tana neman katsewa. Tace "kana ina?" Yace "Ummy." Tace "in har kanason na samu bacci ka koma gun yarinyar nan, haba Hassan taya zaka bar yarinya ita kadai bako tausayi?" Hassan yace "Ummy kinsan fa bana iya kwana da kowa." Bata ce komai ba ta kashe wayar. Kansa ya dafa cikin takaicin wannan abin...... #OneLuv๐Ÿ’• [08/10, 02:16] โ€ช+234 803 222 1758โ€ฌ: ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad:
๐Ÿ