ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 41 of 172

wo?" Kallansa tai cikin mamaki tace "me kake nufi?" Yace "Ummy kinfi kowa sanin me nake nufi." Ummy yanayin fuskarta ya canza tace "Hassan please ka dingama kanka fatan alkairi, sannan ka dinga sa salama a cikin zuciyarka." Kallanta yai kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya rasa me yasa duk basa gane abinda shi yake nufi. Ummy tai shiru, jiki a sanyaye ta fita daga d'akin, kallan kofar yai sannan ya runtse idanunsa dan jiya ma sam baiyi bacci sosai ba saboda matsalarsa data tashi, ta ina zai iya zama da mace a haka? Ya tabbatar daga randa ta ganshi cikin wannan halin zata gudu. ********* Jalila haka ta kwana a bangarensu ita kadai, abinda zai baka mamaki ba wanda yabi ta kanta sai abincin dare da aka kawo mata, sannan taje fita da safe mai gadinsu yace ai ance karta sake fita. Haka tanaji tana gani ta dawo ciki. Wanka kawai tai Mumy tazo ta d'auketa sukaje gun salon, a can ne ma ta daure ta tambayeta inda Safeena take. Nan Mumy tace mata tana gidan kanin Inna har yanzu, bayan alokacin ma tana Abuja gidan babban d'an Alhaji Sanusin wato kanin Inna. Jalila bata ce komai ba, haka aka fara mata gyaran jiki, Mumy ta barta agun suka tafi gidan Taura yin jere. Shikam Hassan da sassafe ya garkame dakinsa ya bar musu gidan, Sagir ma yaso gudu sai dai Ummy ce ta hanashi tace "ya kamata ace da namiji agun. Haka ya zauna cikin tsananin damuwa, yana bin masu jeren da kallo. Sai yamma aka turo aka dauketa, Mumyy ta kama hannunta sukai bangaren Safeena. Jalila tace "Mumy gun Goggo nake san zuwa." Mumy tace "kiyi hakuri Jalila sai dai ki je gunta da mijinki, dan umarnin Inna da Dadynki ne." Tasha kuka ranar sai a lokacin tai dana sanin guduwa da batai ba daga gun salon. Haka ta kwana tana kuka, bacci ma sai zarar ta yai. Abinci kuwa dama turawa kawai takeyi. Ba wanda ya damu da ita bare ya fahimci ranmar da tai a dan kankanin lokacin nan. Yau take asabar, Goggo na zaune akan gado tayi shiru tana tunani, me yasa tun jiya take tunanin Jalila? Ta tabbatar inhar lafiya bazata taba yin kwana uku bata zo ta ganta ba. Shiru tai ta shiga yin addu'a akan Allah yasa lafiya, sannan Allah yasa Sultan yazo ta tambayeshi. Jalila kam yau rufe kofar d'akin Safeena tai dan wani irin zazzabi mai zafi ne ya rufeta sam bata san hayaniya. Gudar da taji ne cikin bacci yasa ta bude idanunta a hankali, ba kowa a d'akin sai ita, sai dai daga falo tana jin ana guda. Mikewa taj da kyar ta sa saitin kunnenta a jikin kufar, duk lab'an bakinta sun bushe. Jitai wata ta sakeyin gudar, sai jitai ance "dalla malama yi mana shiru, sai wani guda kike kamar auran yar gata, da auran Safeena akeyi sai mu jure jin gudar nan amma kinzo kin cikamana kunne." Jalila tai murmushin takaici, har zata juya sai taji ance "Wai ke Fatima kin taba ganin mijin ma kuwa?" Tanajin muryar Mumy tace "inafa na ganshi?" Wacce tai magana tace "tunda ance yana da matsala na tabbatar babba ne, kila fa zaikai shekara 40 ko?" Mumy tai dariya tace "ina na sani? Sai ku bari sai ankai Amarya da daddare sai ku tambayeta." "40?" Gaban Jalila ne ya fadi, matsala? Meke faruwa? Duk da tasan dama bazasu taba mata auran mutunci ba amma batai tsammanin babba bane haka, da alama kenan akwai kanne dayawa tsakanin sa da Uncle?" A can gun d'aurin aure kuwa, Hassan dakyar ya tsaya aka d'aura auran, ana fitowa hoto d'aya ya daure akai dashi, shima wasu manyan mutanen Abba ne da bayanda zaiyi, sannan Abban na rike da hannunsa. Ai kuwa suna gama d'auka yai wuf ya tafi. Sagir kuwa, ba'a magana dan kuwa jiyai kamar an jefamasa katan dutse a sanda yaji sanarwar d'aurin auransu. Dole shi ya tsaya aka dinga gaishe gaishe dashi. Dady sai baza ido yake yaga ango amma bai ganshi ba, Sagir dayazo suka gaisa yake tambayarsa ina Angon? Sagir yace "Yanzun nan ya dan fita, kansa ne ke ciwo." Hassan kuwa yana shiga cikin mota ya rufe, jiyai gumi na keto mai ta ko ina, sam hayaniyar nan tasa gaba d'aya jikinsa ya ji gaba d'aya ba dadi. Idanunsa ne suka canza kala, kansa ya kwantar akan kujera ya rufe idanunsa. Firgigit ya farka dan baisan har yadan yi bacci ba, jiyai numfashinsa na neman d'aukewa, nan yasa hannunsa ya rike wuyansa yana kokarin jawo numfashinsa, gaba d'aya jikinsa ya kame, sai uban zufa dake karyomai, idanunsa sunyi jaa sosai, dakyar ya iya jawo numfashinsa. Nan ya shiga yin numfashi akai akai. Jinai gaba daya jikina yai sanyi, dan tabbas duk wanda yaga Hassan zai dauka ko Aljanu ne dashi ko kuma hankalinsa ba daidai yake ba, Hassan meke damunka? Abinda zuciyata ta shiga tambaya kenan? Nace masu karatu ku taimaka min....... #OneLuv๐Ÿ’• [08/10, 02:15] โ€ช+234 803 222 1758โ€ฌ: ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *No 22* Tana zaune a d'aki wajen azahar Mumy ta fara mata knocking. A kasan kofar take a kwance
๐Ÿ