ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 40 of 172

Hassan yamai a rayuwa bayaji akwai wani abu a cikin duniyar nan da zai kasa barmai, inya tuno da rashin lafiyarsa kuwa tabbas mace kamar Jalila itace best choice, sai dai kai fa?" Abinda zuciyarsa ke fadamai kenan, muryar Jalila yaji tace "Uncle have you ever love me?" Kallanta yai yana murmushin takaici, tace " me yasa kowa baya tunani na? Me yasa kowa yake san tsaramin rayuwata? Me yasa kowa yakesan ya zama nice mai sadaukarwa? Me yasa kowa yakesan yin amfani da ni?" Tsugunawa tai a gun kawai tasa kuka. Gana daya ya rasa yanda zaiyi, harcikin zuciyarsa yakejin kukanta. Baice mata komai ba sai tafasa da tasa zuciyar takeyi. D'agowa tai ta share hawayenta kawai ta meke zata fita. Sagir har ya kai hannu zai riko mayafinta sai ya fasa. Cewa yai "Jalila!" Kallansa tai sannan tace "zan shiga ciki." Yace " bamu gama magana ba." Tace " na fahimci me kakeso kacemin." Yace "Akwai sakon dana kawo miki." Cikin mamaki ta kalleshi, tana kallansa ya mike yaje inda yake a zaune dazu ya d'auko wata yar karamai jaka ta kwali sannan ya mika mata. Hannu tasa ta amsa sannan ta kalleshi, bai saki jakar ba yace "Jalila Please." Kallansa tai bakinta na rawa tace " zan shiga ciki." Sakin jakar tai, hakan yasa yai saurin mika mata yace "Yaya yace inkawo miki na hidindimo sannan yace kiyi hakuri bai samu zuwa ba rannan, da kuma yau." Jalila ta kalleshi kawai dan tama kasa magana. Juyawa yai da sauri, kallan bayansa tai sannan ta fita. #OneLuv๐Ÿ’• [08/10, 02:13] โ€ช+234 803 222 1758โ€ฌ: ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *No 21* Tana tsaye har ya fita daga falon, jitai kanta yayi wani irin sarawa kawai ta zube agun ta zauna, yanzu kam hawayen ma sun kame, sam ta kasa yinkukan, batasan sanda Mumy ta shigo falon ba. Sai jinta tai tana cewa "Dubu d'ari da Hamsin!" Lalai mutanen nan. Kallanta tai sannan ta kalli kudin hannunta, jakar da Uncle ya mika mata ne, har yaushe Mumy ta shigo ta amshi jakar? Mikewa tai dakyar sannan ta fita itama ta baya tana layi, Mumy ko ta kanta batai ba ta fita falo, ta haura sama. Bangarensu ta nufa kawai ta zube a kasa ta kwanta, me ke faruwa da ita? Uncle? Dady? Mumy? Inna? Me yasa kowa yake san tsara mata abinda yaga dama? Me yas ba wanda yake tunanin farincikin ta?" Wasu zafaffan kwalla ne suka gangaro mata, tana nan azaune sam batasan sanda bacci yai gaba da ita ba. ********** Sagir kam tana fita daya shiga mota ya ja ta da gudu, gaba daya ya rasa tunanin me ya kamata yai, ta ina zai fara iya zama gida d'aya da Jalila? Sannan amatsayin matar yayansa? Wani irin burki yaja, ya gangara gefen titi sannan ya kashe motar. Kansa ya kifa akan sityarin motar yana tunano kalaman Jalila, idanunsa ya runtse cikin tsananin damuwa, yace a fili "Am sorry, i am really sorry Jalilah." Kiran Ummy ne yasa ya d'ago, sannan ya daga wayar, Ummy daga can bangaren tace "My son ya kukai?" Ya kakaro murmushi yace "komai ya tafi daidai Ummy, sannan na tabbatar yarinyar nan zata kula da Yaya sosai." Tai dariya cikin jin dadi tace "kai ma ka gano hakan ko?" Yace "sosai Ummy, she is really kind, innocent and honest, yaya zaiji dadin zama da ita." Ummy tace "Na gode sosai Sagir, sai mumai fatan amincewa da ita." Sagir ya daure yace "sosai ma kuwa Ummy." Tace "Ka taho ne?" "Ina hanya zan dan tsaya wani gun ne." Yace "ba matsala, ka gama abinda kakeyi, sai na ganka." Nan ta kashe wayar tana murmushin jin dadi. Aunty Nana ta kalla wacce ke ce mata, wai da gaske a birni take? Tace "wai ke haryanzu baki yarda ba? Kindauka a kauye take?" Aunty Nana tace "ba wai haka bane." "Ko kina tunanin ba mai bawa Hassan yarsa ne ya aura?" Aunty Nana tace "ni ba haka nake nufi ba, inadai mamaki ne." Ummy ta kalleta cikin mamaki tace "indai har ke yar uwata kika fadi haka ai banaji akwai wanda zai fadi haka naji haushi." Ta mike ta fito daga dakin tanajinta tana cewa "ke dai bakya san gaskiya......" Ummy ta janyo kofar ta fito dan kara duba sama, dan sunce gobe zasuzo jere, ba wani taro zasuyi ba saboda halin da ake ciki, dan sunsan ko sunce zasuyi Hassan bazai taba zuwa ba, aure kawai za'a daura a kawota da daddare. Bangaren ya gyaru sosai, tura kofar Hassan tai dan tasan yana ciki. Jin kofar a rufe yasa ta dan yi knocking, Hassan ya mike ya bude kofar. Ummy ce ta kalleshi sannan ta shiga. Hassan ya maida kofar ya rufe sannan ya tako ya zauna abakin gado. Kallan d'akin tai tace "Hassan baka tunanin ya kamata mu canza gado?" Kallanta yai baice komai ba, tacigaba " wannan sofar ma ta tsufa ya kamata mu sa wani, sannan carpet din nan shima ya kamata mu canza shi, Hassan mai kake gani?" Hassan bai kalleta ba yace "Ummy Please ki bari." Tace "me? Bakaso a canza?" Yace "na rasa me yasa kike zumudin auran nan, Ummy bakya tsoron abinda zaije ya da
๐Ÿ