NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 39 of 172

mikar da ita tace "kiyi hakuri ki saka Jalila, dan tundazu akace ya taho." Haka ta hau saka kaya tana kuka, tana gamawa Mumy ta mata kwalliya da kanta, ta fesa mata turare sannan ta d'aura mata d'ankwali. Jalila tana zaune agaban madubi akai knocking, mai aikinsu ce tace mata wai yana falon baki. Mumy ta kalleta tace "Jalila!" Kallanta tai sannan tace "Mumy?" Mumy ta kara rungumeta tace "Jalila ki yafemin wahalar da na baki a da, ni kaina ina dana sanin yin hakan, kishi ne yasani yin komai." Da yake yarinyace mai kishiriwar nuna mata kulawa, jitai gaba daya jikinta yayi sanyi balle dataga Mumy na matse kwalla. Haka Jalila ta fito daga d'akin fa nufi falon bakin. ******** Sagir na zaune yana waya da Abba, yace "Abba nifa kasan bansan me ake cewa ba?" Abba yace "kai dai Sagir sai a hankali, to inkungaisa sai kai introducing din kanka, inkundan yi hira kadan sai ka bata kudin kace na kwalliya ne da wasu hidindimo, dama ai laifinkune da baku bata ba da wuri, sannan laifin yayanka ne da bashida aboki ko d'aya a duniyar nan." Sagir yai murmushi yace "Abba bye na fara jiyo kamshin Amaryar mu." Dariya sukai a tare ya juyo yana cewa "Abba sai.........." Kallan da yake mata ne yasa ya kasa karasawa, Abba ya kashe waya yana murmushi. A hankali ta shigo falon kanta a kasa, kusa dashi taje ta ajiye tiren dake hannunta. Sannan ta dago dan gaidashi. Sagir cikin mamaki yace "Jalila?" Da sauri ta karasa dago da fuskarta tace "Uncle?" Kallan juna sukai kawai sai sukai dariya a tare, yace "Jalila ta!" Kanta ta sunkuyar sannan ta kalleshi tana murmushi tace "Uncle kaine dama? Ya akai kasan gidanmu?" Yace "woah da alama we are made for each other, kinsan ban taba tunanin ganinki ba?" Samun kanta tai da zama a kasan gun, fuskarta dauke da tsantsar farinciki tace "Uncle ni kaina nayi mamakin ganinka." Yace "wai ina kika shiga ne? Ko fishin ne yasa aka kashemin waya?" Tace "Uncle wata matsala ce ta hanani magana dakai." Shiru yai yana kallanta, yanayin fuskarsa ne ya canza, ido ya kura mata wanda haryasata tsarguwa, tace " ka ganni kamar bani ba ko?" Idanunsa na kanta sai yanayin fuskarsa dake kara canzawa, a hankali yace "Jalila nan ina ne?" Tace "Gidanmu ne mana." Wani mugun faduwa gabansa yai ya kara kallanta, itama yanzu jikinta yayi wani irin sanyi a hankali tace "bakasani ba?" Bakinsa na rawa yace " ina Amar Amaryar?" Jalila gabanta ne yai wani faduwa hannu tasa tadan tura jikinta tai baya kadan sannan ta kalleshi idanunta sun ciciko. Sagir ya fara girgiza kai yana cewa "U are not the one ko? Na tabbatar ba ke bace ba ko?" Hawaye ne suka fara zubo mata, idanunta na kansa, gaba d'aya jiyai wani irin zufa na keto mai yace "will you please tell me?" Jalila ta runtse ido wasu hawaye suka zubo mata tace "Uncle i am sorry." Sauko wa yai ya zauna a kasa sannan ya sa hannayensa ya shafi fuskarsa, kallanta yai cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace "Jalila kinsan waye Angon?" Kai ta girgiza tana hawaye tace "bansashi ba kuma bana sha'awar saninsa Uncle, kai nake so kai kadai nakeso Uncle na rasa yanda zanyi, rayuwar........." Tana kokarin sanar dashi rayuwar Goggonta, sai jitai yace "Yayana ne fa." A firgice ta bude idanunta, tace "me kace?" Idanunsa ya rufe sannan ya bude yace "Jalila he is my brother." Mikewa tai tana kallansa tace "brother? Ha kana nufin yayanka ne gidanku d'aya? Kenan zuwanka gidan nan a matsayin kaninsa kazo?" Sagir ya rufe idanunsa cikin takaicin abinda ke faruwa? Meke faruwa? Yau me takeji haka? Mikewa tai da sauri zata fita. Jitai yace "He is someone whom i love alot." Tsayawa tai cak ba tare da ta juyo ba, idanunsa ne suka zubo da wasu kwalla yace "He is someone whom I respect alot." Yacigaba "He is someone whom I can't compare to anyone, i can sacrifice everything for his happiness." Jalila ta juyo da sauri tace "me kake so kace?" Idanu ya rufe wasu hawaye suka zubomai yace "Jalila bazan iya fad'a miko komai ba ayanzu, sai dai a hankali zaki fahimci abinda nake nufi ba sai dai bazan taba zama dalilin da zai zama silar bakincikin zuri'ar mu ba." Kallan mamaki Jalila takemai, sai hawaye dake ta gudu a idanunta tace " Kana san kaima kace inyi hakuri da auran kenan?" Sagir ya taso a hankali yazo inda take, kallanta ya shiga yi hakan yasa ta rufe idanunta tana hawaye. Jin batajin motsinsa ne yasa ta bude idanunta a hankali, me zata gani? Sagir ta gani gwiwowinsa a kasa. Da sauri ta ja baya tace "Uncle me kenan?" Sagir yace "That is how much he means to me." Jalila kallan tsoro ta fara mai, tama kasa magana sam, sai kai da take girgizawa a ranta tana cewa "banda kai Uncle, Please banda kai, ko kowa zai fada Please banda kai, Please ku tasheni daga baccin da nakeyi." Sagir a ransa yana hango abinda zai faru inhar ya nemi bin zuciyarsa, yanzu ma da ya ya yayan nasa ya yarda? Sannan inya tuno da tashin hankalin da iyayensa ke ciki da abinda
🏠