NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 36 of 172

kalinta ba'a kansu yake ba. Haka ta taho a hankali ta tura gate din gidan. Mumy ta ganina waje itada Dady suna magana, suna ganinta suka juyo suka zuba mata idanu. Dady a zuciye ya fara takowa, ganin haka yasata ta tsorata. Hannu ya daga zai shara mata mari, da sauri ta runtse idanunta, tsayawa yai sannan ya kalleta rai a bace, yatsa ya nuna mata yace "ni zaki cima mutumci?" Mumy ta matso ta sauke mai hannu tace "Dadyn Yasmeen meye hakan?" Kallanta yai yace "yanzu da badan shima dalili ya hanashi zuwa ba fa?sannan da kanin nasa bai fahimcemu ba fa?" Mumy ta kalleshi tace "tunda dai komai yazo da sauki ba shikenan ba?" Yace "in Inna taji fa? Me kike tunanin za'ace?" Mumy tace "sai muce mata ta ganshi sun gaisa harya tafi." Dady ya kalleta cikin jin dadi, wanda baisan a ranta ba wai damuwa da Jalilan tai ba balle tace batasan a mata fada ne, tayi hakan ne dan abin ya kara karfafa. Jalila ta kalla sannan tace "Hassan din wani uzuri mai karfi ya tasomai a hanya bayan sun fito, dole ne yasashi kin zuwa, shiyasa ya turo kaninsa. Jalila ta dan tabe baki kadan, dan itakam ba damuwarta bane. Mumy ta rike hannunta tace "muje ciki ko?" Jalila tace "A'a Mumy asibiti zan koma." Mumy ta jinjina kai tace "bari mu kaiki." Jalila fuskarta dama a daure take tai bangarensu. Kayan da Goggo tace ta dauko mata ta dauko sannan ta fito. Suna tsaye suna ta wani abu wai su a dole mata da miji, ita Mumy sai wani shagwabewa take, haushi ya kara kama Jalila a ranta tace "mutum ya girma amma jinsa yake kamar yaro." Ta gabansu tazo ta wuce, Mumt ta riko hannunta tace "Jalila tare zamu tafi." Jalila tai shiru tana kallan Dady. Mumy ta bude mata baya sannan ta shiga, ita kuma ta shiga kusa da Dady. A hanya tayi shiru tana kallan waje, wayarta ce ta fara ringing, da sauri ta zarota. Uncle? Da sauri ta daga tace "Uncle!" Jalila i am............ Bata gama jin mai zai fada ba, Dady yai wani irin parking, wanda ya tsoratata, sam ta mantada mutane a motar. Mumy ta fizgi wayar tana cewa "Jalila me kenan?" Jalila a tsorace ta kalleta, sunan da ke jiki ta kalla MINE? Nunawa Dady tai ya kashe wayar yace "uban wa ya sai miki waya?" Idanunta ne suka firfito tai shiru. Mumy tace "Jalila zance kike a bayan idanun mu?" Jalila ta kallesu sai dai ta kasa magana, cikin salo Mumy tace "shiyasa take neman bijerawa maganarka kenan? Lalai samarin zamani sun iya siyan zuciya, da har zasusa 'da ya bijirema mahaifinsa." Dady cikin takaici yace "Uncle? Malamin ku ne kenan? Dama abinda kike a makarantar kenan?" Jalila da hawaye suka fara zubo mata tai shiru tana kallan ikon Allah. Dady yace "wato ina miki magana ma kinfi karfin amsawa ko?" Jalila tace "ba haka bane Dady." Mumy tace " Jalila yaushe kika zama haka?" Jalila jitai hawaye suna gudu a idanunta, wannan shine a dakeka a kuma hanaka kuka. Haka tana kallo Dady ya zare sim din ya karyashi sannan ya cilar waje, sannan ya ajiye wayar cikin motar sa. Jalila tana kuka tana cewa "dan Allah dady ka barni ko magana daya muyi." Dady ko kallanta baiyi ba ya ja motar sukai gaba. Mumy tana cewa "lalai Jalila wato ya baki kima saurayinki magana?" Juyawa tai tana kallan window tana wani irin kukan takaici. #ONELUV💕 [08/10, 02:11] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 19* A kofar asibitin Dady yai parking sannan sukai shiru a cikin motar, Jalila tasa hannu. zata bude kofar Dady yace "Jalilah!" komawa tai ta zauna tana kallansa tare da amsawa. Dady ya juyo yace "Fatima dan bamu guri." kallansa tai kamar zatai magana sai naga ta fasa, kofar ta bude ta fita sannan ta nufi cikin asibitin. Jalila ta kalleshi sai dai gani take kamar shiryawa sukai, Dady ya kalleta sannan yace "Habiba, na tabbatar kina ganin kamar ban damu dake ba wanda a gaskiyar magana ba haka bane, a duk inda uba yake to lalai tabbas ne yaso abinda ya haifa, kallan mamaki tamai dan tabbas da ace Goggo ba ta bata labarin yanda tai rayuwa dashi ba tabbas zata yarda yana santa sannan zata iya tunanin wani abun akamai daya hanashi nuna mata so. Dady ya kara kallanta yace " kinajin haushi na ko?" kanta na kasa batace komai ba, yace " Jalila wannan auran da za'a miki ba wai rayuwar mahaifiyarki kadai zai taimaka ba, ni kaina kin ceci ni sannan kin taimaki rayuwar yan uwanki." Dagowa tai ta kalleshi cikin rashin fahimta tace " Dady ba aure ne tsakaninku da Goggo?" kallanta yai yace "me kike tunani?" Tace " amsar da zaka bani ita zata bani ikon ajiye komai dake raina." Shiru yai yana kallanta yace "Jalila yanzu ba zancen wani aure da rashinsa bane a gabanmu, inhar kinason Inna ta taimaki mahaifiyarki dolene sai kin amince da auran nan, sannan in fada miki gaskiya ko ki yarda ko karki yarda Inna sai ta aura miki yaran nan." Idanunta ne suka fara z
🏠