NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 33 of 172

nda tai maganar yasa ransa ya baci yace " me? Hakuri?" Ta daga kai, kallanta yai, harzai sake magana sai kuma naga ya fasa, motarsa ya koma ya shiga ya fizgeta da gudu. Jalila ta harari motar, ta cigaba da tafiyarta tana matsar kwallarta. Da alama yau gaba daya ranar bakin ciki ce a gareta. #ONELUV💕 [08/10, 02:08] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 17* A hankali ta tura kofar dakin, Tana kokarin shiga nurse din na kokarin fita, jiranta tai ta fito maimakon ta shiga sai tabi nurse din. Tana gaisheta, Nurse din ta tsaya ta amsa, Jalila ta matso tace " Aunty ya jikin Goggo?" Tace "da sauki, ya akai? Kina tsoro ne?" Jalila ta goge kwallarta tace " Aunty kina ganin kamar kwanaki nawa zamuyi kafin kafar Goggo ta samu sauki?" Tace "maybe 3 to 4weeks" Jalila ta zaro ido tace "da tsayi haka?" Tace "Umm." Jalila tai shiru, Nurse din tace " ba wata tambayar?" Jalila tace "in tabar asibitin fa?" Nurse din cikin mamaki tace " ta ya za'ai tabar asibitin tana cikin wannan state din? Ko asibitin kuke san canzawa?" Jalila ta runtse ido can tace " Aunty kudin ne......." Muryar Sultan taji yace "me kike anan?" Idanunta ta bude da sauri, Nurse din ta wuce ganin kamar bazata iya magana ba. Sultan ya karaso yana kallanta. Ya kara cewa "me kike anan?" Jalila bakinta ne ya shiga rawa ta kasa magana, Hannunta ya rike yace "meye hakan?" Kamar ya tabota kawai tasa kuka, mamaki ya kamashi can yace " Mumy ce?" Kai ta girgiza, yace "Dady ne?" Nan ma kai ta girgiza, sam bai kawo Inna ba saboda ba kasafai take shiga harkar rayuwar gidan ba, yace "Jikin Goggo?" Hawayenta ta share tace "Sultan ya zanyi?" Yace "name?" Tace "tsakanin rayuwata data mahaifiyata." Yace "wace irin tambaya ce wannan, sannan in amsa kike so ai ke yarinya ce mai kuma lafiya, ita kuwa Goggo ba lafiya ne da ita ba." Jalila ta shiga daga kai tana cewa "haka ne, Goggo itace gaba da komai." Kallan mamaki ya kara mata, ta kakaro murmushin takaici tace "nagode Sultan." Leda ya miko mata yace "gashi, Ni bari na wuce." Tace "kai kadai?" Yace " inada kudi a jikina, nan ya zaro dubu biyu yan dari biyar biyar, mika mata dubu daya da dari biyar yai ya maida dari biyar aljihunsa yace " gashi ko zaki sai wani abin." Ta amsa tamai godiya, juyawa yai ya fita, da kallo ta bishi sannan ta goge fuskarta ya tura kofar dakin. Goggo na zaune shiru ta shiga, Jalila ta karasa tana cewa "Goggo a zaune kike?" Goggo ta kalleta tace "kin dawo?" Tace "eh." Jakar hannunta ta kalla tace " baki daukon kaya ba?" Jalila ta bude baki tace "wayyo, wlh na sha'afa sam, ni fa dama jakar nan kawai naje daukowa." Goggo ta kalleta cikin zargi tace " me ya samu idanunki? Abubakar ya miki wata magana ne?" Ta zauna kusa da ita tace "Kai Goggo, ni ko ganinsa ma banyi ba." Goggo tai ajiyar zuciya tace " sai yaushe zamu bar asibitin nan?" Jalila tace "tab aima ki gyara zama goggo, dan wlh yanzu Nurse take cewa sati uku zuwa hudu." Goggo cikin mamaki tace "Wannan asibitin mai tsada? Kina tunanin zasu biya mana kudin?" Jalila tai murmushin takaici tace " karki damu da wannan, ke dai ki kwantar da hankalinki, kinji dai mai likita yace jiya." Goggo tai murmushi, Jalila ta bude ledar da Sultan ya miko mata, ruwa ne mai sanyi faru tace "ruwa kika aikeshi?" Tace "Allah sarki Sultan cewa nai ya bani ruwa in akwai, ashe wai babu shine naga ya fita." Jalila a ranta tace "dama sai a dinga kawo abinci ba ruwa." Haka tai ta kokarin boyema Goggo damuwarta. ********* Sagir na komawa gida ya hau sama dan dauko wayarsa, ganin irin kiran da Jalila tamai yasa hankalinsa ya tashi, nan ya shiga buga mata waya shima, sai dai duk yanda ya kira No Answer kawai ake rubutamai, Fitowa yai ya shiga mota ya tafi makarantar su, ba ta nan, ya akai baiyi tunanin amsar address din ta ba? Wai shi yana ganin yasai mata waya, kwatancen gidansu bazai zamarmai wahala ba. Kai ya shafa cikin takaici, ina ne gidansu? Haka ya dawo gida jiki a sanyaye. Abba ne bayan Magrib ya shiga d'akin Hassan, yana zaune rike da littafi a hannunsa yana karantawa, Jornal ne. Yana ganin Abba ya rufe littafin sai dai baiyi motsi ba daga inda yake bai kuma yi magana ba. Abba ya shiga ya zauna kusa dashi, Shiru ne yadan ratsa dakin, can Abba yace " Me zakayi gobe?" Hassan ya mai kallan mamaki, me zaiyi? Shi daka rayuwarsa ai kullum iri daya ce, Abba ya kalleshi yace "Gobe da yamma ko bayan magrib kuje kai da Sagir ku ga yarinyar." Kallan Mahaifinsa yai cikin mamaki yace " inje ince mata me?" Abba yace "kaje ku gaisa ta ganka, ka ganta." Hassan yai shiru can yace " Ai wannan tun a farko ya kamata kuce naje, Abba abinda ya kamata kuyi tun farko kenan, ta ya zaku sa rana ba tare da yarinya ta ganni ba?" Abba yace "Hassan bakasan me nai ba akan
🏠