Β  Β  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 3 of 172

Ya maida earphone dinsa, tare da kwantar da kansa kan kujera, Safeena tai kwafa tace " in munje gida kya maimaitawa Mumy na abinda kika fada a motar nan." Jalila a ranta tace " yauma a kwai wani sabon shan wahalar kenan, ai wahala bata kisa." Suna isa gida motar Dadynsu Safeena na parking, Safeena ta tashi kanwarta Yasmeen dake barci, tana ganin Dadynta ta ruga da gudu ta gunsa. Safeena ma tai gunsa tana murmushi, daga Yasmin yai yana cewa "Baby Yasmin an dawo?" Sultan ne ya karaso yace " sannu da zuwa Dady." Kallansa yai yana murmushi, Safeena kusa hannayenta ta zargo cikin nashi tare da cewa " Dady kace da safe zaka dawo." Yace " Naso dawowa da safe sai dai akwai wani meeting da nadan yi ne da suppliers dinmu. Karasa maganar yai yana kallan Jalila wacce kullum take jiya iyau, irin yar kibar nan ko dan murmurewar nan batayi, Jalila tace " Dady sannu da zuwa." Yace "Jalila an dawo?" Ya fada tare da juya kai zuwa gun Safeena wacce ke harar ta, yace " muje ko?" Nan suka nufi ciki Yasmin ma hannunsa ita kuma Safeena ta rikeshi. Murmushinnn takaici tai tace " happy family, wazai kalleni yace mahaifinane?" Wucewa tai can cikin gida inda aka dan musu dakinsu daya da bandaki a can karshen gidan aka katangesu kamar masu aikin gidan........ ************* A hankali ta tura kofar d’akin bayan ya amsa sallarmarta, zama tai daga gefen gadon inda yake a kwance, kallanta yai sannan ya fara kokarin mikewa zaune, a hankali cikin sanyin muryarta tace β€œ Hassan bazakai breakfast da mu bane?” Yace β€œUmmy banajin yunwa.” Idanunta ne suka canja yanayi cikin tsananin tausayama dan nata tace β€œ Hassan sai yaushe ne zakai yaki da wannan matsalar dake damunka? Mun kaika duk wani asibiti da ake ji dashi a duniya amma ba wani ci gaba, dole ance kaine zakai yaki da wannan matsalar da kanka ba wani bane zai maka.” Kallansa tai cikin tsananin tausayawa tace β€œ Hassan ka tausayamin ko dan halin da nake ciki.” Kallanta yai yace β€œ Sau nawa zan ce miki ki cireni aranki Ummy? Dazu da safe nagama nazari ina tunanin abu biyu ko dai na bar kasar nan na koma egypt da zama ko kuma na bar gidan nan, ina tunanin wannan shine abinda ya cancanta na muku dake da Abba.” Kallansa kawai takeyi cikin mamaki tace β€œ Kana tunanin in kabar kusa damu hankalinmu zai kwamta ne ko me?” Kafafunsa ya sauko ya saukesu a kasa yace β€œ To ya kuke so nai? β€œ Tace β€œ ka zo muje gun likita ya sanar dakai hanyar da zakabi danyin yaki da matsalarka.” Yace β€œ Ummy please ki fita.” Mikewa tai dan tasan in bata fita bama ba wani abu dazai biyo baya, in har kaji yace mutum ya fita to tabbas karshen maganarsa tazo kenan, daga nan duk wani abu na duniya da zaka fada ko mai zafinsa bazai taba tanka wa ba. Tana fita ta rufo kofar sannan ta sauka kasa, mai gidanta ta kalla jiki a sanyaye, yana ganin yanda tai yasan ba’a dace ba, kansa ga saukar kan dinning din sannan ya dago ya kalli yaransa biyu dababba mai bin Hassan sai kuma mai binsa mace, duk yaransu ukun sun girma, dan karamar mace wato Ameera a Ss2 take. Sagir yana ganin yanda sukai duk jiki a sanyaye yai saurin mikewa sannan ya jawo Ummy ya zaunar da ita kan kujera yace β€œ Ummy kinsan jiya naje gidan Auty Nana?” Ta kalleshi tace β€œDa yaushe?” Yace β€œ bayan mun tashi a makaranta, Aina tace ai zata zo mana hutu karshen satin nan.”” Ameera da sauri tace β€œYa Sagir da gaske?” Abba yai murmushi yace β€œAuta da alama kawa ta kusa zuwa.” Dukansu ne sukai murmushin. Suna cikin cin abinci ya fito rike da makulin mota, ko kallan inda suke baiyi ba yai waje, sam basu kula da wucewarsa ba dan falan babba ne sannan dining area din na bangaren kitchen. Mota kawai ya fada yai waje............ *Wattpad Ayushermohd* ( _please vote and Comment_😍) #Oneluv [08/10, 19:18] β€ͺ‬: πŸ—― *JALILAH* πŸ—― Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *AyusherMohd* *No 2* Gudu yai ta shararawa a mota sai dayaga har ya fita daga cikin gari sannan yaja motar ya tsaya sannan ya gangara gefen titi ya kashe motar, gani nai ya fito daga mazaunin driver ya koma baya ya kwanta tare da lumshe idanunsa. Bai dade da fara bacci ba yai wani irin zabura, a tsorace ya farka jikinsa ya fara karkarwa, jiyai numfashinsa na mai wahalar ja, jijiyoyin wuyansa ne suka firfito kamar wanda aka rikema hancinsa da bakinsa, zufa ce ta shiga keto masa da kyar ya jawo numfashi sannan ya mike ya zauna tare da hade kafafunsa, nan da nan idanunwansa suka canza. Wayarsa ce datai kara tasa ya dawo hankalinsa, kallan wayar yai sunan mahaifinsa ne a jiki, idanunsa ya runtse yana takaicin wannan rayuwar tasa, shi kadai ya hana iyalan gidansu samun farin cikin rayuwa. Lalai yana tunanin dolene ya bar kasar nan yaje inda ba wanda ya sanshi in ma rayuwar tasa a iya nan ta tsaya to shikam zai iya cewa Alhamdulila. Bai dau wayar ba har sai da ta katse. Fitowa yai daga motar ya hau samanta yana kallan bish
πŸ