NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 27 of 172

Uncle ya kalleta yace "wai anzo daukarki." Mamaki ya kamata tace "amma nace sai bayan azahar, gabanta ne ya fadi badai wani abun bane ya samu Goggon ta?" Kallan Uncle tai a tsorace tace "Uncle bari naje gida." Zahra na tsaye kusa da motarsu, wayarta ta mika mata ta bata jakarta, nan Jalila ta sa a cikin jakar ta shiga ciki sukai gaba, addu'a kawai take Allah yasa ba wani abun bane ya samu Goggonta. *£*£********* Goggo tana zaune wajen karfe 12 Yasmeen tazo da gudu wai tazo inji Inna. Tayi mamaki sosai dan tanaji tunda take a gidan Inna bata taba nemanta ba haka kawai. Samun kanta tai da faduwar gaba. Haka ta taso da kyar saboda ciwon kafa ta karasa. Tana shiga falon taga Inna, Dady da Mumy a zaune. Faduwar da gabanta ya shiga yi ne kawai ya sa ta shiga yin addu'a dan ta tabbatar ba lafiya ba, shiga tai a hankali. Mumy ta mata nuni da kujerar dake gefe tace "ki zauna anan." Goggo ta zauna sannan ta gaida Inna ta gaida Dady da Mumy. Bayan sun amsa ne falon yai dan shiru. Goggo tace "lafiya?" Inna tace "Gobe za'a kawo kayan lefen Jalila." Abin yazoma Goggo a ba zata wanda yasa tace "lefen Jalila kamar ya kenan? Dan banaji ta taba sanar dani tanada miji." Inna tace " ba sai ta sanar dake tana da saurayi ba, dan kuwa hakkin mahaifi ne ya zaba mata mijin da yaga ya dace da ita, sannan shi Abbakar ya fitar da nasa hakkin na yi mata miji yanzu hakkin 'ya ne tabi umarnin mahaifinta." Goggo ta kalli Dady da sauri tace " Abbakar me kenan?" Yace "hakan da kikaji shine." Cikin daga murya tace "da tunda aka haifeta bakasan da hakkin ta akanka ba sai yanzu? Dama wlh ni jikina yaban mutuncin da kuke mata da wani abin a kasa, ashe aurar da ita zakuyi? Mijin mahaukaci ne ko dan shaye shaye? Ko kuwa barawo ne? Ko kuma nakasasshe? Ko kuma dan fashi ne?" Mumy tace "ya zaki fadi haka, Abbakar fa ubanta ne ta ya za........." Goggo cikin tsawa tace "Ba dake nake ba." Yanda tai maganar ne yasa Mumy tsorata dan bata taba ganin Goggo na fada haka ba. Goggo cikin fada tacigaba " me ka mata a matsayinka na ubanta? Me ka mata?" Dady shim ya kasa magana dan bai taba ganin tana fada haka ba. Goggo fa mike da kyar idanunta sun canza tace " duk abinda kuke ma tunanin ku ajiye dan wlh ba wanda ya isa ya yima Jalila auren dole." Juyawar da zatai taji wani jiri na debanta, kan kace me tayi baya luuuu jikake tim ta fadi a kasa. Da sauri suka mike suna jijigata. Jalila wacce ta shiga bangarensu da gudu taga ba Goggo jakarta ta cilar a dakin sannani ta fito ta nufi bangarensu Mumy dan tambayarsu,ganin Goggo a kasa su Dady da Mumy na kanta yasa ta karasa da gudu jikinta na bari. #ONELUV💕 [08/10, 02:02] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 14* Dady a rikice ya nufi daki ya dauko key din mota ganin yanda Goggo take a kwance ga Jalila sai wani irin kuka takeyi. Jiyai ance "ABUBAKAR." Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalli Inna, kallansa tai tace "ina zaka?" Yace "Asibiti." Tace "dawo ka zauna." Tsayawa yai yana kallan Goggo sannan ya kalli Inna. Mumy ce ta kalli Inna tace "Inna kingafa......" Kallan data mata ne yasa ta yin shiru, Jalila a rikice ta jawo gwiwarta ta iso inda Inna take tace "Inna dan Allah ki bar Dady ya kai Goggo asibiti, duk da bansan me ya hadaku da Goggo ba har take nan bangaren sai dai na rokeki da ki yi hakuri." Hannunta ta hada guri daga tana ta murzasu tana kuka alamar tsantsar neman taimako. Ganin Inna batada niyyar kulata yasa ta ja gwiwa zuwa gun Dady ta rike kafaraa tace "Dady ka taimaka dan Allah, karka manta Goggo matarka ce, sannan mahaifiyatace." Gani tai Dady ya kalli Inna, hankalin Jalila ne ya kara tashi ta matso kusa da Mumy ta rike gwiwowinta tace "Mumy ki taimaka min, bazan sake yima Safeena laifi ba, sannan zan cigaba da yi muku aiki, dan Allah ku taimakeni ku kai Goggo Asibiti." Muryar Inna ce ta katseta da cewa " kinaso a ceci ran mahaifiyarki?" Jalila a rikice tana kuka shabe shabe ta shiga daga kai ba kakautawa, Inna tace " akwai hanya daya mafi sauki, wanda in kika amince da ita bama kaita asibiti ba hatta kula da ita zamu samo wanda zai dinga yi, sannan asibiti duk tsadarsa zamu kaita indai zata samu lafiya." Jalila a rikice tace "ko me kukeso ku fada zanyi dan Allah." Inna tace "ki amince da auran da Mahaifinki zai miki." Gabanta ne ya fadi ta kalli Dady idanunta jagab da hawaye, yana ganin sun hada ido ya juyar da kansa gefe. Jalila tace "ban gane ba Inna." Inna tace "in baki gane ba sai ki bar Goggon taki ta karasa rayuwarta anan." Wani irin fitar da numfashi da Goggo tai shi yasa Jalila rikicewa ta karasa gunta da gudu tana kuka. Inna tace "kina tunani ne akan maganar? Ashe baki dauki ran mahaifiyarki da daraja ba kenan tunda kina tunanin yanda zakiyi tsakanin lafiyart
🏠