NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 24 of 172

e komai ba. Sai daya dan kara yin shiru kafin yace "Hassan ke kake tunani game da aure?" "Aure? Aure kamar ya?" Abba yace "baka tunanin aure?" Cikin rashin fahimta yace "ban fahimci aure ga mara lafiya?" Abba ya danyi shiru kafin yace " Hassan mubar zancen lafiya da rashinsa, kafi kowa sanin halin da mahaifiyarka take ciki a kanka, ka kuma san yanda tasha wahala akan rashin dan uwan............" Kallan sa Hassan yai idanunsa har sun kada, bakinsa ne ya fara rawa, hannunsa ya sa a wuyansa yana dan kakari, cikin lokaci kankani Hassan ya rikede, hankalin Abba ya tashi sosai rungumeshi kawai yai dan ya rasa ma mai zai mai. Da kyar numfashinsa ya daidaita sai dai zufa da ta keto masa, Abba jikinsa ya kara yin sanyi tsananin tausayi dan nasa ya kara kamashi. Ya dade sosai kafin ya dawo daidai, Abba ya mike zai fita, Har yakai kofa Hassan yace "Wani abu ya samu Ummy ne?" Abba ya juyo daga inda yake a tsaye cikin raraunar murya yace " Hassan in har ka damu da halin da muke ciki ka amince ka auri yarinyar da mukesanka da ita." Mamaki me ya kara kamashi yace" tambayar abinda ya samu Ummy......." Yanzu Abba ya canza muryarsa daga alamar tausasawa zuwa dan bacin rai, yace " akwai wani abu dake damunta ne a duniya daya wuce matsalar da kake ciki? In har kanasan hankalinta da nawa ya kwanta ka yarda da auren da muke kokarin yi maka." Hassan shima cikin dan zafi abinda rabon da yai magana mai tsayi haka harya manta yace " Taya zaku nemi min aure bayan kunsan halin da nake ciki? Sannan ni a rayuwata kunfi kowa sanin banasan zama inba ni kadai ba, ya zakuyi kuyi tunanin hadani da wata? Bayan kunsan daga ita har ni hakkin mu zaku shiga?" Abba ya dan matso yace "wannan halin da kake ciki shine yasa muke tunanin ma auren kota wani hali, halin zama kai kadai, halin kin fadar in baka da lafiya, halin nunkufarci da rashin fadar matsalar ka, halin kin yima kowa magana, halin rashin kula da kanka, wannan kadan ne daga cikin dalilan dayasa mukesan ma aure." Hassan har zaiyi magana yaji kansa yayi gingirin gim dan gaba daya dama baya iya magana mai tsayi, mikewa yai ya shige cikin toilet ya rufo kofar. Abba ya juya ya fita, Ummy na tsaye a falo a kasa sai zagaye takeyi tana ganinsa ta matso tace ya kukai? Yace "kema kinsan bazai yarda ba daga bugu daya ba." Tace haka ne, yace "ke zaki mai magana gobe, dan inyaga kin damu kema kinsan zai yarda." Tace "amfani dani da tsauyi da kaunar da yakemin zamuyi?" Abba yace "ba haka nake nufina, hakan dai shi kadai ne haya." Shiru tai batace komai ba. Jalila kuwa tana zaune kusa da goggo suna dan cin abinci duk ta dameta da labarin film din India data kalla mai suna Vivah tana ta fada mata yanda saurayin ciki da budurwar ke san juna can tace "Goggo kinsan abin mamaki? Matarfa ranar auransu ta kone a jikinta amma saurayin nan dan tsabar san da yake mata ya nuna shi wannan ba komai bane, Goggo a asibitin fa ya aureta......" Goggo tace " nikan Jalila sai yaushe ne zaki kyalemu muci abinci shiru? Bafa asan mutum na cin abinci na magana, sannan ni na rasa me yasa baki da aiki sai zancen soyayya, wani irin so kikema Sagir din nan dayasa kika koma haka?" Jalila tai dariya tace "Goggo karki damu yanzu tunda muka gama makaranta zaki ganshi tunda kinga gobe za'ai taron yaye mu, kinga kuwa kila ma jibi ki ganshi dan bazai iya dadewa bai ganni ba." Goggo ta girgiza kai cikin mamaki tace "yaran zamani wato ba kunya, sannan ya san gidan nan ne?" Tace "gobe zan kwatantamai." Goggo ta tabe baki tace " da alama dai kinfi sanshi ma." Jalila tau dariya tace " tab Goggo ai ni bansan wayafi san wani a tsakanin mu ba." Ya isheni haka nan. Ta fada tare da tsame hannunta dan ta rasa me yasa takejin kirjinta na mata nauyi sosai sannan sai tafi kanta na sarawa. Jalila tace " Goggo ki bari kawai na kusa daukeki mu koma gidan aurena." Harararta Goggo tai tace " to sannu, nidai na fada miki ki kiyayi kanki karkije ba shine mijinki ba." Jalila tai dariya tace "tab lalai Goggo kina tunanin zan kara san wani bayan Uncle? Ai nni har mafarki nayi na auranmu." Goggo tace "to uwar surutu ya isheni haka nan, ba wanda yasan mijinki a duniya sai Allah sai dai a koda yaushe ina miki fatan miji na gari wanda zai soki kamar ransa ya kuma kula dake kulawar da baki samu ba a rayuwarki." Jalila batace komai ba sai cigaba da cin abincinta datai tana murmushi dan itakam tasan mai so da kula da ita ba kowa bane sai Uncle dinta. ******** Abba ne ya kira Sagir ya tambayeshi labarin jarabawa dan shi ba sanin abinda ake ciki yai ba, nan Sagir ya sanar mai ai an gama Neco. Yana kashe wa ya kira Inna, bayan sun gaisa ne yace mata "Inna yara sun gama jarabawa ko?" Tace "eh sun kammala nima dama ina jiran kiranka." Abba yace " sai mu hanzarta ko?" Tace "ba laifi ai ku muke jira." Yace " To Alhamdulila insha Allah jibi sai mata su kawo lefe." Tace "hakan yayi , Allah ya kaimu." Nan sukai sallama, ka
🏠