NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 23 of 172

in dana sani tace "Jalila kinsan yanda nake tsananin san Nasir ganin ransa ya baci dana tsaya ina tunani yasa na matso kusa dashi na sumbaceshi a kunci, shine yace shi sai na mai a baki, nan na kai bakina saitin bakinsa shine ya rikoni ya dinga tsotsar leb'ena bansan sanda na bude mai cikin bakina ba, Jalila bansan ya akai ba na kasa kwacewa sai bashi hadin kai danai, dakyar na kwavi zuciyata na fizge jikina da sauri na fito daga motar nai gida da gudu........." Kuka ne ya zo mata wanda yasa ta kasa karasa abinda takesan fada, Jalila kam sam tama kasa magana sai inalilahi kawai da take cewa........ Ganin yanda Zarah ke kuka yasa Jalila ta riko hannunta tace "Zarah it's okay! Kinyi laifi babba ma kuwa sai dai tunda harkin fahimci kinyi laifi sai ki nemi yafiya a gun Allah ki kuma kiyayi aikata makamancin abinda kika aikata." Zarah ta rungume Jalila tana kuka, Jalila tace "Sai dai magana daya zan fada miki gaskiya ki bincike san da Nasir yake miki, so ne ko sha'awa, in so ne sai ku tuba ga Allah ku nemi kariya daga shedan in kusa sha'awa ne sai kisan zaman da zakiyi dashi." (_Gareku 'yan mata da samari masu irin wannan soyayyar, sai kaga saurayi yazo gun budurwa in zai tafi sai yace sai ta mai kiss ko sai ya rungumeta, ko kuma ya nemi tamai abinda bai kamata ba, wanda ke da kike aikatawa kinsan haramun ne, sannan shi da yake saki shima yasan haramun ne._ _Dan Allah mu guji fadawa halaka saboda wani buri na zuciyar mu, Allah ya mana tsari ya kare mu daga sharrin zuciya_Ameen suma Ameen) Jalila na zaune itada Zarah tana kara mata fada aka aiko tazo inji Uncle Sagir. Kallan Zarah tai tace "Zarah ina zuwa." Zarah tace " Ba sai kin dawo ba dan na san ba ganinki zanyi yanzu ba." Jalila ta kalleta tace " har kin dago?" Zarah ta harareta tace " yanda kike nunawa ta ya ya zan kasa ganewa? Ba ni ba na tabbatar yawancin mutane sun sani." Jalila ta matso tace "da gaske? Ina nunawa a fili?" Zarah tai dariya tace gashi nan kin rubuta a goshinki da jan biro." Jalila ta dan daket tace "bansan iskanci." Zarah tace "daga ke har shi ai kun gama sanar ma mutane dan ni a bakin mutane ma na fara ji." Jalila ta dan shagwabe fuska tace " kice kowa kallona kawai yakeyi?" Zarah tace "ah to mu ai yan kallo ne." Jalila ta rufe fuskarta tace "bari in rufe fuska ta inje a haka." Zarah tai dariya tana cewa " u are so Naive." Jalila tana ta wani nuku nuku a haka har ta fita dan dama jiya ma a waje suka hadu gaban makarantarsu kadan, wani dan lungu. Sai data dan laleka kafin ta gangara wai ita a dole batasan a ganta. Sagir na kallanta yana murmushi har ta karaso, yace " me kike ta lekawa?" Tace "Uncle ya zamuyi? Duk fa ansan menene tsakanin mu." Yace "to sai akai ya?" Tace "qx Yace "nace sai akai ya?" Tace "hmm hmm" Murmushi yai yace " kin manta kin gama skul? Sannan ba yaudara ko wasa muke ba balle muce bamasan a sani, ya zakiyi in sukazo auranmu? Ko gidan mu?" Idanu ta zaro sai kuma ta rufe idanta da sauri, yace "oh ni wai sai yaushe ne za'a daina min kunyar nan?" Sauke hannu tai tace "ni in kai wata maganar ne sai naji kunya ta kamani." Yace "to da alama zan tattara maganganun dake cina sai munyi aure." Murmushi tai, sun dade tare kafin tace zata tafi, dan yau ita kadai za'azo dauka tunda Safeena tana gidan kanin Inner tun last week tacan take zuwa makaranta. ******** Abba ne ya kalli Ummy yace " ya kamata yau na sanar ma Hassan abinda ke faruwa." Ummy tace " ni kam tsoro nake kar abin nashi ya dawo." Abba yace " sai yaushe ne zaki bari a fadamai? Tun wancan satin kike sani nake jan lokaci ko so kike sai abin ya zo zai sani?" Tace"shikenan ka fadamai yau." Abba ya mike yai sama........... #ONELUV💕 [07/10, 21:30] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *NO 12* Hassan na sa kaya yaji Abba na knocking, da sauri ya karasa sa rigarsa sannan ya murda makullin ya bude dakin. Abba ya matsawa ya shiga cikin dakin, kallan dakin Abba ya shiga yi yana jinjina kai, gashi dau duk lalurar dake damun Hassan amma bazaka taba ganin dakinsa da datti ba, yadan murmusa dan tabbas bai manta lokacin yana yaro ba kafin abin nan ya sameshi Hassan mutum ne mai tsafta da tsantsani, sai dai dakin bai musu karami ba? Ko sagir zai maida kasa? Dan dama saboda Hassan ne ya dawo nan kusa da dakinsa. Ganin Abba na ta dubs dube yasa hassan ya koma kan sofa ya zauna. Abba ya kalleshi sannan ya koma kusa dashi shima ya zauna., Matsawa kadan Hassan yai dan Abba ya zauna daf dashi. Abba yai murmushi yace " Hassan yada matsawa?" Bai tanka ba dan dama Abban yasan ba tankawar zaiyi ba. Sunyi shiru sai karar fanka dake kadawa a cikin dakin, sai sanyin A.C, Abba ya rasa ta ina zai fara, can ya daure ya maida hankalinsa kan Hassan yace "Hassan!" Kallansa yadanyi baic
🏠