NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 21 of 172

tace "ba komai Mumy sannan ni bakumin komai ba, Goggo itace za'a ba hakuri, ni dama 'yace a gunku kome kuka min dama hakkinane na 'ya inyi abinda kuka sa ni." A ran mumy tace 'Ya? Amma a fili tace "Nagode Jalila, sannan zan ba Goggon hakuri itama, inaso ki cigaba da nuna matsayinki na babba a gidan nan, karki nunama kowa ke din ba 'yata bace, da ke da Safeena duk daya kuke a gurina." Jalila tace "nagode Mumy." Haka suka isa gida cikin farin ciki. Goggo kuwa bayan sun fita ta fito da kanta ta kwankwasa kofar falon cikin gida, Yasmeen ce ta bude kofar. Goggo tana dan dingisa kafarta da take mata ciwo, tace "Yasmeen Dadynku na nan?" Tace eh, sannan tai ciki da gudu tana kwallamai kira, dady ne yadan fito ba da dadewa ba. Goggo ta kalleshi sannan ta gaisheshi. Mamaki tai dataga ya amsa, tace magana nakesan muyi. Yace ina jinki. Sai datai dan shiru kafin tace "meke faruwa?" Yace "name fa?" Tace "na canzama Jalila da kukai kai da zuri'arka, nasanka nasan bazaka taba canzawa dan kanka ba sai dai in dakwai abinda kake nufi damu, domin kai da kanka kasanar dani hakan." Yace "ban ganeba?" Tace "ka manta da bakinka kacemi kai a rayuwarka ba so, in har kuwa naga kanasan abu to lalai akwai abinda zai kareka ne." Dady yace " kema kinsan wannan zancene na da, sannan me ya kawo wannan maganar da yar cikina?" Kallan zargi tamai tace" tuni nazo na maka dan baxan taba tafema ba in har ka cutarmin da 'ya ta." Ta juya ba tare da ta nemi amsarsa ba, ko ajikinsa ya juyawarsa ciki. ******** Yau tun safe ake hidima a cikin gida,Mumy ta aika aka kira mata Jalila, tare dukansu suka hadu a kitchen sukai ta aiki, Safeena kuwa tana gidan Kanin Inna a cikin gari, suna gamawa Mumy tace ma Jalila tace tai wanka a toilet din Safeena. Wani had'ad'en material ta dauko mata ta saka, Jalila kam yau tayi mamakin kyan da tai, dan tayi kyau sosai, Mumy da kanta ta daura mata dankwali sannan ta sa mata turare. Wajen azahar motar Taura tai parking a gida. Ummy ce ta fara futowa sannan shikuma ya kashe motar ya fito. Kallo d'aya zakama Ummy kasan macece mai class ba wani shigar karya tai ba sai dai kana ganinta kasan matar manya ce. Taura ya matso sannan ya nuna mata hanyar. Dady ne ya fito ya shigar dasu falon baki, sai wani washe baki yakeyi, Inna ta sauko suka gaisa, nan suka dan tattaba magana akan harkar business, Mumy ta mike ta shigo dakin Safeena inda Jalila take a zaune,tace "Jalila zo ki kai musu abinsha." Jalila ta mike tana cewa "Mumy kunya nake." Mumy ta yafa mata mayafi tana cewa "abokana Dadynki ne gaisawa kawai zakuyi." Haka ta fito ta amshi tiren ta nufi falon, ta rasa me yasa gabanta ke faduwa, yaye labulen tai ta shiga da sallama. Ummy tana shigowa ta kura mata ido, haka kawai taji yarinyar ta shiga ranta, yanayin nutsuwarta ne ya kara burgeta, Jalila ta ajiye tiren kanta na kasa dan ji take kamar kallanta akeyi. Kanta na kasa ta gaishesu, Ummy ta fara amsawa sannan Taura ya amsa ya daura da cewa " Ya karatu?" Tace "Alhamdulila." Yace "ance kun kusa fara jarabawa sai a dage ko?" Tace "insha Allah." Ganin yanda take tsugunne a gun yasa Ummy tace "tashi kije." Nan Jalila ta mike ta fita. Inna ta kalli Ummy tace "kun ganta?" Ummy tace " Mun ganta sai fatan Allah ya kaimu lokacin, sannan muna fatan bazaku mata maganar auren ba har sai ta gama karatunta kamar yanda aka tsara." Inna tace "dama hakan shine daidai." Ummy tai shiru kafin can tace "sai dai ni banasan auren dole, a matsayina na mace banasan tauye hakkin mace yar uwata, kar muje akwai wanda takeso." Mumy tace "in dai wannan ne ba matsala dan Jalila ba ruwanta da kula kowa, ita kunya ma bazata barta ta kula saurayi ba." Ummy ta jinjina kai na gamsuwa, haka suka sa hannu a takarda na yarjejeniya....... Sannan sukai sallama. Nace uhm hmm.......... [07/10, 21:28] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *NO 11* Ummy har ta sa hannu zata kwankwasa kofar Hassan sai kuma naga ta sauke hannunta sannan ta bi kofar da kallo, juyawa tai jiki a sanyaye tana neman sauka. Sagir ne ya fito daga dakinsa, kallan Ummy yai sannan ya matso gunta, yace "Ummy menene?" Tace " Sagir ashe kana ciki?" Ya kalli shima kofar Hassan sannan yace "Ummy in koma dakin yaya ta karfi?" Harararsa tai na wasa tace "kana tunanin zai barka ne?" Yace "sai in zauna ta karfi ince bazan fita ba." Ummy tai murmushi tace "karka damu insha Allah na kusa samun mai tayashi kwana." Cikin zumudi yace "haba?wanene?" Ummy ta fara sauka daga matatakalar tana cewa " watace." Sagir cikin mamaki yace " Aure?" Nan ta shiga bashi labarin abinda ke faruwa sannan ta daura da cewa " Sagir ni na rasa me yasa tunda na ga yarinyar nan nakeji kamar akwai alamun tauye hakki acikin wannan lamarin." Sagir yace "ba wan
🏠