NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 2 of 172

sannan ta ja wani tsaki juyawa tai baya taga duk yawanci mutanen baya motar suke bi da harara da alama kowa yaji haushin yanda motar ta kunno da gudu cikin layinsu, Jalila ta kara kallan motar wacce ta riga ta kule tare da kara tsaki tace " wasu dai ba kai sai na daukar kaya" Cigaba da tafiyarta tai duk ta gaji, har sai da ta kusa isa makarantar sannan ta tsaya tare da ciro safarta ta tsaya a gefe ta saka sannan ta dan karkade jikinta, ita nufi makarantar, mamaki tai da taga kamar motar da gani dazu. Motar ta gani tayi gaba, baki tadan tabe sannan ta karasa gate din makarantar. Sabon Malaminsu ta gani tsaye a bakin gate da alamar shine yake tarar late comers, kanta ta sunkuyar har ta isa gun. Shikuwa tunda ta taho yake kallanta fuskarsa a dan hade tana matsowa yace " Habiba Auwal me kenan?" Kallansa tai da sauri tare da cewa " Good Afternoon Sir!" Yace "Afternoon?now?" Da sauri tace" Oh sorry sir Good Mor......." Katseta yai yace "Dama bakya zuwa school da wuri?" Kallansa tai tace " No sir wlh yau ma tsaytsayi ne." Fuska ya kara had'ewa yace " Tsautsayi a ranar farko dana fara tsayawa a gate?" Kasa tai da kanta tana wasa da yatsun hannunta, yace "sai ki dau dustbin kiyi picking." Kallansa tai dan ta dauka dukkanta zaiyi, murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace "Thank you sir" Shima murmushin yai yace "Last warning in har kinaso mu shirya kenan." Da sauri ta daga kai sannan ta dau dustbin tai gaba ta fara picking, kallansa ta juyo tai ta baya, ba shakka bata taba ganin wanda kayan Nysc sukama kyau ba irin Uncle Sagir. Jalila na gamawa ta wuce ajinsu, ganin ba kowa a cikin ajin yasa tai saurin juyawa ta nufi lap. Suna lap din chemistry ana musu practical, da sauri ta wuce gun groups dinsu, Zarah ta kalleta tace "Jalila kinga yarda idanunmu suka firfito muna tsoron kar a ce ya akai aka ganmu mu shida. Tace "Kedai bari nima na dauka zai ganni." Haka sukai ta karatu har sai da aka tashi break sannan ta samu tasai biscuit na naira goma taci ta sha ruwan fanfo sannan ta ajiye naira goman. Ana tashi suka fito ita da Zarah suna hira, Zarah tace " Jalila kinsan jiya sai ga Ya Amud da takardar jamb!" Jalila ta kalleta cikin jin dadi tace "Haba? Kice hankalinki ya kwanta dama kina ta tsoron kar ace za'a miki aure." Tace " ke dai bari jiya ai baccin dadi nai, dan banaji zan iya rabuwa da Nasir dina, kuma kinga shi level 3 yake a Buk." Jalila ta tabe baki tace " su soyayya manya, da alama kema makarantarsu zaki nema. Tace "sai ma kin tambaya...." Dariya sukai, Zarah tace " ni nayi gida ke nasan sai kin jira ko?" Tace eh Dayake gidansu Zarah ba nisa da makaranta nan ta kwana, Jalila taja gefe ta tsaya kamar yanda suka saba, minti 30 ne tsakanin lokacin tashinsu dasu Safeena, abinda zai baka mamaki shine su in har suka shirya zasu taho to fa ba ruwansu da jiranta sai dai ita bata isa a tashi ta tafi ba sai ta jirasu. Tana nan a tsaye taji ance "baki tafi ba? Juyowa tai ta kalli malamin nasu wanda yanzu su yan aji shida kusan dukansu matan nan in suka zauna gulmarsa sukeyi, tace " eh sir." Ya dan daga littafin dake hannunsa kamar zai kwada mata, da sauri ta runtse idanunta, jin shiru bai dake taba yasa ta bude idanunta a hankali, kallansa tai ya harde hannayensa kawai yana kallanta cikin mamaki tace "ba dukana zakai ba?" Yace "me kikamin da zam dakeki? Dazu da kikai laifi ban dakeki ba sai yanzu?" Cikin mamaki tace amma naga ka daga...... Yace "sato ke bakya zuwa school da wuri sannan in an tashi kece karshe a tafiya, me hakan yake nufi?" A ranta tace "ni kaina wannan amsar nemanta nakeyi." A fili tace " hmmm, ai......" Wayar da aka mai ne ta katsesu ya dau waya tare da fara tafiya, alama ya mata da hannu akan ya wuce. Tace " Okay Sir." Bin bayansa tai da kallo, sannan tai ajiyar zuciya, nan ta cigaba da tsayuwa har suka iso, 2017 toyota sienna ce tai parkin a kusa da ita, tura kofar motar tai ta shiga. Sannan ta rufe kofar, Safeena ce wacce kana kallanta kasan bata wuce sa'ar Jalilan ba tace " Ashe kuma yau da kafa kika taho." Jalila ta kalleta tace " Amma Safeena dazu tsakani da Allah baku ganni ba, sannan Malam Auwal ma bai ganni ba?" Safeena tace " Ta ina zamu ganki? Sannan in ma munganki menene damuwarmu? Uban wa ya hanaki yin sauri?" Jalila ta juyo ta kalleta tace "Uban wa ya hanani yin sauri? Kwata kwata fitowata daga bangarenku minti nawa ne har kuka taho?" Tace "wannan damuwarki ce, naga kina wani hararata ni na saki aikin? Sannan in kinsan bakyasan kiyi late me zai hana ki dinga tashi karfe hudu?" Jalila ranta ya baci ta juyo gaba dayanta tace " karfe hudu? Ku karfe nawa kuke tashi, ni daga na tashi sallar asuba me nakeyi? Bangarenku nake shigowa sai na gama muku komai har abinci sannan nake tafiya na shirya, sannan hakan ma ba birgewa nake ba har zakice indinga tashi karfe hudu?" Sultan kanin Safeena ne ya zare earphone din dake kunnensa yace " will you please keep quiet, duk kun cika mana kunne da wani musunku."
🏠