NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 171 of 172

'yan uku ma likita yace zaki haifa, ya gano wani daga nan, wani anan sannan wani a kwance tanan." Ya fada yana wani taba cikinta. Gabanta ne ya fadi tace "yan uku?" Yace "eh shiyasa banasan ki sani dan nasan hankalinki tashi zaiyi, kinga Amira kadai mana kadan sai mun hada da Aina'u." Kallansa tai ta hade rai tace "abinda yafi Aina'u." Yadan saki fuska yace "yanzu Jalila ya zamuyi? Ga karatu?" Idanunta ne suka fara rau rau, dariya ya sa harda kyakyatawa yana nunata, tana ganin haka tasan tsokanarsa ce ta motsa. Kafa tasa ta tureshi daga kan hadon ya fadi a kasa, amma duk da haka dariya yake, ta hade rai tace "Allah zan rama." Yace "a yaushe kenan? Bayan kullum haka ake cewa?" Ta turo baki, yace "tashi kiyi wanka Baba Ghali zaizo gaida 'yarsa." Da sauri tace "haba?" Yace "kin manta Goggo ta fada miki yau zasu zo dashi? Dasu Nabila? Kafin mums muje?" Tace "inalilahi nikam naga ta kaina wallahi na manta." Ta mike da sauri tai toilet ya bita da kallo yana Murmushi. Tana shiryawa yana taimaka mata tasa kaya da sauri dan tana fitowa daga wanka akace sun iso Nan suka fito mayafinta a hannu. Neman gudu takeyi gun sauka daga kan steps, Hassan yasa hannu ya rik kugunta, kallansa tai tace "yaya karfa suga mun dade." Yace "gwara suga laifina na basu hhskuri akan kijin asara." Dariya tai sannan ta sauko a hankali. Nabila na zaune yarinya yar shekara 12, tana ganin Jalila ta saki fuska dan sun hadu a biki. Dr na ganinta yace "masha Allah ana ganinki anganta." Ummy tace "ah haba? Anya ba san kai kuwa?" Dr yace "inafa sankai? Sai dai inkece kike sanyi." Abba yai dariya, nan ta karasa kusa da Ummy ta tsugunna ta gaishesu, fuska a sake ya amsa sannan ta gaida Goggo, dasu Ummy da Abba. Nabila ta dawo kusa da ita ta zauna. Hira suke sosai har lokacin yingirki yai, Jalila, Amira suka shiga kitchen Nabila ma tabi bayan Jalila dan ko ina Jalila tai binta take. Bayan sun gama cin abinci akai sallah sannan aka karasa wani hira. Can yanma wajen magrib suka fito dan tafiya, dukansu suka fita harabar gidan ana karayin hira. Mai gadi ne yazo ya sanar dasu zuwan Dady. Jalila naji gabanta ya fadi,Hassan ta kalla da sauri. Hassan yace "abarshi ya shigo. Yana shigowa ya tsaya turus, ganin mutane, sai daiduk da haka ya gano Jalila. Cire kunyarsa yai ya nufosu. Dr ya kalli Goggo yace "shine baban nata?" Tace "eh." Dady ya karaso jiki a sanyaye, hannu ya mika musu suka gaisa dukansu, sai dayazo kan Dr sannan ma yaga Goggo ce ashe dan da sam bai gaje taba. Dr yace "barka da haduwarmu, nine mahaifin Jalila na yanzu, mijin mamanta kenan." Dady ya kalli Goggo yaga yanda ta canza, ya kalli motar da suke jin gine agun dan alama ce ta motarsa ce. Jiki a sanyaye ya kalli Jalila da Goggo, kamar zaiyi magana sai sukaga yasa gwiwowinsa a kasa, da sauri Hassan yaje ya sa hannu ya dagashi. Dady ya kasa magana kawai sai kuka.......... Gaba daya tausayinsa ya kamasu, dan kam Dady yaga rayuwa adan lokacin nan. Idanun Jalila ne suma suka ciciko. Gaba daya Dady yama kasa magana kawai sai kuka......... ********** Gidan ya cika sosai anata shirye shirye, Jalila na zaune a daki tayi rau rau da ido kamar zatai kuka, Hassan yace "wai da zafi sosai?" Tace "nidai wallahi da zafi." Bude kofar da akai bayan an kwankwasa ne yasa Hassan juyowa. Goggo ta kalleshi tace "Hassan jeka gidan Sadiq ankai muku abincinku can." Yace "Goggo har gidan Sadiq cin abincin? In tafi in barta?" Mumy tace "ai kuwa dai tafiya zakai, dan na kula Jalila neman raki takeyi dan taga yau ka dawo, ai sanda tana nakudar bata dinga zabga mana raki haka ba, amma yau dan ta ganka shine takesan fanshewa, dama ai suna na mata ne, kaje kaci abincin amarya." Jalila ya kalla wacce ta shagwave, haka ya fita. Goggo tana zuwa ta dungurema Jalila goshi tace "ko kunya? Shayarwar akema raki haka?" Jalila ta turo baki, tace sai fa yau yazo? Basu san Ummy tazo ba sai ji sukai tace "abarta tai abinta wayace kar ya dawo da wuri? Wai shi a sole yanajin haushin na daukota da cikinta yakai wata tara? Itama ku barta ta fanshe." Mumy tace "dama dai Ummy ke shagwabata." Sukasa dariya, Safeena ce ta shigo da kaya tace "gashi inji Wata tace dole dole wannan za'a sama jariri." Ummy ta girgiza kai tace "Aunty Nana kenan, sam ba dama." Nan Ummy ta dauki yaran wanda yake jin yunwa tace "Jalila bashi yasha asamai kaya." Dan nasan mijin nan naki dakyar zai bari ki kara sati biyu anan. Sukasa dariya. Ameera ce ta shigo da flask na ruwan zafi ta ajiye kusa da Jalila. Jalila ta daga mata gira, Ameera ta hade fuska tace "bamu shirya ba." Jalila ta jawota tace "badai ruwana in naji kina lalabashi a waya cikin dare. Ummy tace " gulmar ce?" Jalila tai dariya...... A kasa kuwa falon Abba, dady na zaune daga dan gefe yana ta kallan yanda aketa hira tsakanin Dr da Abba. Shikam sai dai hmm ko um
🏠