NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 17 of 172

gayyacen ta shiryamin abinci, sannan ba dadi taga naje banci ba, kuma kinsan halina inhar naci abinci yanzu 11 banaji akwai abinda zan iya ci nan da awa d’aya.” Tace “Hakane, kai kadai zaka ne?” Yace “a’a da ina tunanin tafiya da Sagir to kuma ina tunanin kar taji nauyin fadar bukatun ta a gabansa, shiyasa zan tafi daga ni sai Ibrahim.” Tace “to sai kun dawo.” Ya dau hularsa ya saka sannan suka fito tare. Sagir na falo ana masu Ameera tsiya akan sun gaji da jiran abincin safe ya hangosu, mikewa yai yana dariya yace “Ummy zaku fita yawon shakatawa ne?” Harararsa tai tace “a haka ake fita ba ko mayafi?” Yace “ai ba komai tunda mota zaki shiga.” Abba ya kalleshi yace “Wato Sagir in baka zolayi mahaifiyarka ba na kula sam bakajin dadi.” Keyarsa ya sosa yana murmushi yace “Abba kasan nafisan kullum naga tana murmushi ne.” Ummy ta kalleshi tace “ Muje muga masu abinci tunda Abbanka ya mana yajin aiki yau.” A tare suka fara takawa suna hira, Abba ya bisu da kalli cikin jin dadi sannan ya juya ya fita. ************ Jalila anci uban aiki duk tai wujiga wujiga ga ko abinci ba wanda ya damu taci, sai data gama jera komai sannan ta fito, bangarensu ta nufa cikin tsantsar gajiya. Goggo na zaune hankalinta duk yana kofa tana jiran yar tata ta shigo, ko abincin ma ta kasa ci, Jalila na shigo ta zube tare da kwanciya akan cinyarta. Goggo tace “zauna ki danci abinci.” Da kyar ta mike ta sha shayi da bread sannan ta fara kokarin kwanciya, Goggo tace “Jalila kidan jira ya tsirga miki.” Tace “Goggo wlh nikadai nasan me nakeji.” Tafada tare da kwantawa. Abba ya iso batare da shan wahala ba, saboda kowa yasan Hajiya, Sun shiga babban falo inda ake sauke manyan baki. Dady ne ya fara tarbarsu, ya zauna suka gaisa, sannan mumy ta shigo. Bayan sun gaisa ne sai Hajiya ta shigo. Taura yana ganinta ya mike, sai data zauna sannan ya gaidata. Mumy ta mike ta fito, d’akin Safeena ta shiga taga bata nan, na ta fito ta bude dakin Sultan, yana zaune akan computer da alama game yakeyi. Tace “Safeena fa?” Yace “Safeena? Ba jiya take cewa akwai inda zasuba yau da friends dinta? Inaji sun tafi ai.” Mumy tace “dama yau ne? Ni na dauka sai gobe ai, to kai taso ku gaisa da bakon.” Mikewa yai ya fito, yana gaishesu ya koma d’aki. Mumy tace “Inna bata nan kinsan tace yau akwai inda zasuje.” Inna ta kalli Taura tace” babbar yarinyar bata nan sun fita.” Yace “bakomai Hajiya,ni ai ban masan kinada jika babba haka ba.” Yana nufin Sultan. Tai murmushi tace “Sultan ai na biyu ne, babbar mace ce ajinta shida a secondary.” Yace “Masha Allah, Allah ya raya.” Tace “Ameen. Sun d’an bar musu falon na sama da minti talatin saboda su ci abinci. Sai da suka gama sannan Inna da Dady suka shiga. Sun d’anyi shiru kafin Inna tace “Taura kayi hakuri rashin nemanka danai har sai damatsala ta tasomin.” Yace” bakomai Hajiya.” Tace “Taura muna cikin matsala wanda company dinku ke neman fuskantar durkushewa...........” Nan ta zayyane masa duk yanda matsalolin ke faruwa,shima Dady na kara mai jawabi. Sai da sukka gama, Ta daura da cewa “shine nake neman taimakon ka.” Taura yai shiru kafin can yace “ba matsala indai, sai dai nima sai kun bani zuwa gobe na duba yanayin abin sannan sai musan yanda za’ai. Taji dadi sosai, dady yace “mungode kwarai.” Taura ya dau takardar ya shiga kara dubawa, yana nazari, kudi sukeso sosai dole dai ya nutsu kafin yasan abinyi, dan business ne.” Inna ta kara godiya, Dady ma haka. Bayan sun gama ne suka mike dan tafiya. Jalila bayan tayi wanka Goggo ta bata mafici dan takai makotansu akwai wata tsohuwa agidan da ta sa a mata. A gun ajiye motoci ta hango su a tsaye, da alama bakon ne, ta gabansu dole zata wuce shiyasa tana zuwa inda suke ta tsugunna har kasa ta gaishesu. Kallanta Taura yai ya kura mata ido, har ibrahim ya amsa gaisuwar shi bai ce komai ba. Ta kara kallan Taura wanda kallan da yake mata yasata yin kasa dakai tace “Ina wuni?” Taura yace”lafiya kalau, kece babbar yarinyar gidan?” Cikin halin ko in kula tace “Eh!” Yace “Masha Allah, aji shida akace kike ko?” Takara cewa eh. Yace “Alhamdulila.” Mikewa tai tace “Sai anjima.” Taura yasa hannu a aljihu ya zaro dubu biyar, yace “gashi!” Idanu ta zaro tai saurin cewa “A’a kabarshi nagode.” Kallanta yai sannan yai murmushi yace “kyauta na miki fa?” Tace “wlh ka barshi, na gode.” Kai ya daga sannan ya bita da kallo, Ibrahim ya kalla bayan sun shiga mota, yace “me zakace game da yarinyar nan?” Ibrahim yace “ban fahimceka ba.” Taura yai murmushi sannan yace a ransa Alhamdulila ala kuli hal...... #Oneluv💕 ‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *AyusherMohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert
🏠