ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 168 of 172

nan abinda kake yi ba karamar tauye mata hakkin rayuwa kakeyi ba, ayanzu ma danaji baka dauketa a matsayin mata ba, in na sanar da ita auranku ya rabu sai dai nafisan ka rubuta saboda abinda zai iya faruwa nan gaba." Dady yace "amma ni.:......." Abba ya katseshi "akwai sauran cin zarafi ne dakake kokarin yi mata?" Dady yai shiru yana tuno irin wulakancin dayama Goggo, Abba yace "akwai mai santa inhar kanaso wani ya gyara abinda ka bata sai ka rubuta min yanzu ka bani." Dady ya kara goge kwallar data zubomai sannan yace "to zan rubuta yanzu, dan na tabbatarban camcanci zama mijinta ba." Abba ya wuce mota Dady ya biyoshi, paper ya dauko da biro ya mikamai, Dady ya rubuta saki daya yaba Abba. Gaba daya sai ya kara ba Abba tausayi, Abba ya koma cikin mota yana tunanin ya taimaka mai ne? Sai dai in ya tuno abubuwa marasa kyau da Dady ya aikata sai yaji inaa bazai iya ba gwara ya kara sanin duniya ta garashi tukunna, wallet dinsa ya dauko ya duba ciki, dubu takwas ne a ciki, yasa hannu a aljihunsa yaji dubu biyu ya mikamai yace "gashi kai kudin mota sannan ka nemi na abinci." Dady ya fara godiya, Abba ya shige ciki da sauri. Yana parking ya fito jiki a sanyaye.......... #OneLove๐Ÿ’•[1/11, 10:17 PM] El-hajj: ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ *80* ************* Bayan wata takwas. Jalila ce ta turo kofar falon, tana shigowa ta zube a kasan carpet din falon ta kwanta. Hassan na kitchen yana jinta ya fito falo yana cewa "Hajiya an dawo?" Harararsa tai tace "wallahi daga yanzu na daina yarda da wannan wayan ace wai ni kadai xan dinga zuwa siyayya." Kusa da inda take kwance yazo ya kwanta shima yace "kefa kikace ayi game, wanda ya zabi zuwa siyayya shizai dinga zuwa cefani." Tace "amma ai wayau kamin, kasan wanda ka rubuta hakan, tunda kana dauka ka zabi abinda kake so." Juyowa yai ya kalleta tare da jawota kafadarsa yace "baby ba wayau, ya zakiyi? Tunda kin zaba ai ba yanda zakiyi." Ta turo baki tace "ni gaskiya a sake." Yace "inaaa ban yarda ba." Tace "Allah ga yunwa, na dawo daga makaranta ansani wucewa cefani." Ya dan bubugata alamar lalashi yace "karki damu wannan ur Hubby ya shirya miki sai dai kawai kici." Da sauri ta kalleshi tace "Allah?" Ya mike yana daga mata gira alamar yes, da sauri ta bishi kitchen ta bude tukunya tana murna, hade ran datai ta juyo ta kalleshi ne yasashi yin dariya yace "Surprise!" Kallan Indomien dake cikin tukunyar tai tace "Yaya Allah ni nagaji dacin indomie." Yace "ah haba? Ta kalleshi tace "nisaidai kamin dan wake." Dan wake? Tayaya akeyi? Badani ba." Tace "Allah yau inbanci ba banaji zan iya bacci." Yace"baban magana, sai ki dafa mana muci." Nanta shigayindan wake, sai dai tana gamawa sunzo ci ta kasa, da sauri ta mike tai toilet ta shiga kela amai, Hassan cikin mamaki ya kalleta tare da dafa goshinga yace "Baby stress ne ya miki yawa? " Ta kalleshi tace "bakai bane ka sani?" Mikar da ita yai yace "muje gari ki duba wani abin kichi." Ta kalleshi kamar zatai magana sannan sai yaga kuma ta tsaya, yace "ya akai?" Kallansa tai tace "Yaya yaushe rabon nai period?" Yace "period? Na manta, badai shi bane? Ahh nikam gaskiya....." Yanda yaga tana irge da hannunta ne yasa ya kalleta yace "oh gaskiyarki fa kin dade bakiyi ba." Ta kalleshi tare da saurin rikimai hannu tace "muna ta fama da skul ga murnar zani nigeria bikin Ya Sageer next month inaji shiyasa sam ban kula ba." Yace "da matsala ne?" Tace "a'a sai dai inaji......" Sai kuma tai shiru, yace "me?" Ta kalleshi ta nunamai yatsa guda biyu, yace "baby?" Tace "maybe." Da sauri ya sureta sama yana wani irin farinciki, Jalila ta hade rai tace "yaya murna ma kakeyi? Karatu na fa?" Ya sauketa yace "menene aciki? Sai muje mu taho da ko Amira tunda ta gama secondary tazo ta zauna mana." Ta kalleshi cikin gamsuwa tace "amma saifa munje anyi test karka sa rai dayawa." Hannunta ya rike kawai yanata tsalle kamar wani yaro, dariya kawai ya shiga bata..... ************ Yanda aketa shirye shirye a gidan ne zai kayatar dakai, Goggo da Ummy na kitchen suna ta shirya abinci kala kala, Ameera da Aina'u suna gefe suna aiki suma, Goggo ta kalli Ummy tace "Oh na tabbatar jiya Jalila batai bacci ba." Ummy tai dariya tace "inafa zatai zata zo taga na gida, malam Hassan dai na tabbatar ya shari baccinsa." Goggo tai dariya, Ummy ta kalleta tace "Dr dai yau zai bar mana ke ki kwana ko?" Goggo tai dariya tace " bazan bar Nabila da Muftahu ba a gidan, shima cemin yai in kwanab amma nikam badani za'ai wannan abin kunyar ba, anjiman nan zan koma, suna zuwa zamu tafi." Ummy tai dariya tace "ya labarin su Mumy kuwa?" Goggo tace "suna nan, ai kun gama musu komai, tunda kukace su dawo gidan danake ciki inyaso su sa dayan haya." Ummy tai murmushi tace "kinsan da ke naso a dinga ba ma rabin kudin hayar dazasu dinga samu,
๐Ÿ