NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 164 of 172

kenan ya zama babba wanda ba wanda ya isa ya rainashi, sai dai duk a cikin san kudinsa banda ta hanyar zina, in yaransa suka ganshi fa?" Da sauri ya juya yai waje tare da yarda makullin( ina duniya zaki damu? Ace wai yanzu mace itace ke neman namiji kuma ita ke biyanshi saboda rashin hakuri da san kai da san zuciya? Allah ya mana tsari ameen) Dady ya koma cikin dakin nan wanda yanzu gaba daya haushi yake bashi...... Haka ya gama kwanansa ya fito daga hotel din, ina zai je? Shi ba abokai ba ba wasu yan uwa ba, haka yaje ya nemi karamin hotel ya kara biyan wani kudin ya shiga, yanzu kam gaba daya ba komai a account dinsa sai dubu talatin, wanda haka yake zara yana siyan abinci. Gaba daya a dan kankanin lokacin nan har Dady ya canza. Duk yanda ya kira Jalila kuwa bata dauka dan itakam tasan magana daya ce tsakaninsu, itakuma bazata taba taimaka mai ya kara lalacewa ba. ****** Yanda aka bude kofar kitchen din ne yasa Ummy da Jalila suka juya da sauri dan ganin meke faruwa, Hassan kam idanunsa sun rufe da farinciki, kusa da Ummy yazo ya rike hannunta yace "Ummy na ta fito." Tace "Visa din?" Da sauri ya daga kai yana dariya ya kalli Jalila wacce ta juya da sauri tare da cigaba da wanke wanken da takeyi. Ummy ta mintsine hannunsa tace "Shine kake murna haka gaba daya kamar dama ka gaji da mu?" Kansa yadan sosa yana dariya yace "kema Ummyna kinsan ba haka bane, murna kawai nake dai abinda ake nema an samu ba wani abu ba." Tace "ba wani nan, bayan ga fuskarka nan ta nuna min a fili." Yai dariya yace "dagaske?" Ya fada yana shafa fuskarsa, Ummy ta girgiza kai tace "oh ashe ni kadai ce nake tunanin rashinku." Ta juya itama tana karasa abinda takeyi. Hassan ya matso yace "Kai Ummy na." Tace "Ah bari na dauko wayata." Ta juya ta fita. Hassan na gani ta rufe kofa ya matso ya rungume Jalila yana dariya. Tace "Oh ni yaya, dan Allah ka daina farin cikin nan haka nan, kar Ummy taji ba dadi." Yace " to wai ni yazanyi na daina? Nikam ki gama wannan aikin kizo mu fara hada kaya." Jalila ta dan tureshi tace "ni dai kar Unmy ta shigo." Ya saketa yace "ni yau ma zan sai ticket dan jibi sai tafiya, gobe na kaiki gidan Goggo sallama." Baki ta bude tana kallansa tace "oh ni yaya." Yace "harna fadawa Abba ma nasan yanzu shima ya fadama Ummy, kallan mamaki kawai takemai, shikam juyawa yai ya fita. Haka kuwa tana fitowa taji a bakin Ummy wai jibi zasu tafi, haka ya sata a daki sukahau hada kaya, itakam duk kunya ta isheta. Washegari ya kaita gidab Goggo acan ta wuni, sunsha hira da Sultan, Goggo itakanta tayi mamakin wannan tafiyar da wuri haka, rasa mai zatace tai kawai sai dariya tai. Ya sallami Goggo kudi mai kauri dan yasan Ummy da Abba zasu dinga kula dasu, sai dai shima yana san yai wani abin. Wajen magrib yazo ya dauketa ya kaita gidan Mumy wai tanasan tayima su Safeena sallama. Gida ne karami amma agunsu wadanda suka taso daga katan guri, dakuna biyu ne da falo da kitchen. Mumy na ganin Jalila ga saki fara'a cikin jin dadi, Safeena ma tana toilet tanajin Mumy na kira. Sunan Jalila tai sauri ta fito tana murna, Jalila na zaune kusa da Mumy, Yasmeen na zaune a cinyarta tana bude alawoyin da Jalila ta bata, Safeena ta taho da sauri, ta rungumeta. Mumy tace "nikam har abin yazo haka?" Tace "wallahi gashi har mun kusa tafiya." Jalila ta kalli Safeena tace "kin fara neman skul ne?" Tace "wallahi maganar da muke da Mumy kenan kullum amma jiya na dameta ta kira Sani yace sai nayi Jamb. Jalila tace "haka ne amma wacce kikeso?" Tace "F.U.D." Jalila tace "Allah ya taimaka ya bada Sa'a." Tace "Ameen." Jalila ta kalli kasan carpet wanda da alama Yasmeen abinci ta gama ci, shinkafa da wanke sukai damai da yaji, Jalila ta kurama kasan ido tana tuno lokacin da agida ake sata yin abinci kusan kala uku, kuma ko za'ai me basa cin mai da yaji sai anyi miya da nama kachha kacha. Kallan Mumy tai tace "Mumy ya kuke da kayan abinci?" Tace "kudin da Hassan ya bamu muke cancanawa kafin mu samu a saida filin Da Inna tabarmin, sannan tanada wasu kudi a bank, sai dai su sai anyi cike ciken takardu kafin a bamu." Jalila tace "To Allah ya taimaka, amma Mumy tunda kinyi karatu ba gwara ki fara aiki ba ko a company din Inna ne? Inkika fara kamar abin zai kara sauki." Cikin mamaki ta kalli Jalila tace "Oh ya akai wannan tunanin baizo min ba?" Jalila tai dariya, Mumy tace "aikam zanyima Kanin Hassan magana, sannan ai inama da Shares din Inna." Jalila ta kura mata ido tana kallo, shiyasa Dady ke cutanta sam bata tsayawa tai tunani mai zurfi. Jalila ta kalleta tace "bari na baki numbersa sai ki kirashi." Sundanyi hira kafin Hassan ya kirata ya sanar da ita dawowarsa, fitowa tai ta shiga mota, a hanya tana bashi labarin yanda sukai. Ya riko hannunta yace "Umm wannan babyn daga inna aka samota ne haka?" Tai dariya tace "daga ina kuwa?" Yai dariya zaiyi magana wayarta ta
🏠