NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 161 of 172

ada Safeena da Yasmeen, Mumy kuma ta shiga motar su itada Sultan. Tana shiga ta baza tagumi. Jalila kam tana shiga ya kalleta sam bai kula da Safeena ba yadaiga Yasmeen a hannunta ya wani saki murmushi zaiyi magana tai saurin nunamai baya da idanta, Safeena yaga ta shigo sannan ta gaisheshi, Hassan ya kalleta ya amsa, sannan ya kalli Jalila ya dan matso saboda abin na cinsa yace “kiyi maza nima ki gaifarmin yar baby.” Harararsa tadanyi tace “zaka fara ko?” Gyara zama yai tare da gyaran murya sannan yace “me zan fara?” Jalila tace “Yasmeen ga Uncle.” Yasmeen tace “ Uncle ina wuni?” Hassan yadan ja kumatunta yace “Yasmeen ko?” Kai ta daga tana murmushi, ya mika mata hannu yace “nice to meet u.” Hannu ta mikamai dan ta fahimci gaisawa zasuyi, tana dariya. Hassan ya kalleta yace “yanzu ina zamuyi Ranki ya dade?” Murmushi tai kafin tace“zamu fara zuwa gidan Mumy ne ta debo kaya sai mukai Sultan gidan Goggo mu wuce gida.” Ya kalleta yace “To angama Hajiya.” Dariya tasa tace “Yaya?” Yace “ me? Ohhh na manta ashefa ba’a zama Hajiyar ba tukunna, to ko mu fara zuwa Hajj ki zama Hajiya kafin mu tafi Qatar din?” Tace “Nayi recording zan fadawa Ummy.” Safeena tai shiru tana kallansu abin sha’awa, jitai idanunta na neman tara ruwa, da sauri ta maida idanunta jikin window tana kallan titi. Yasmeen kuwa sai zolayarta yake tana dariya, Safeena kuwa tundaga gaisuwa bai kara ce mata komai ba, har suka isa gidan. Dady na falo suka shigo, Jalila ce ta fara shiga rike da Yasmeen. Mikewa tsaye yai yana kallanta, zaiyi magana yaga Mumy ta shigo itada Safeena. Komawa yai ya zauna yai shiru, Jalila ta kalli gidan gaba daya ya canza a dan wannan lokacin, shikanshi dadyn duk ya wani canza, Mumy ta zuba mai ido ya kalli Yasmeen datazo gunsa da gudu ta rungumeshi, har a jikinsa sai dayaji yace “Yasmeen ya gida?” Tace “Dady ina kaje? Baka siyomin ice cream ba?” Ya dagata yana murmushi, shigowar Hassan da Sultan ne yasashi sauketa, yana kallan Hassan. Hassan ya kalleshi sannan yace “Barka dai.” Dady ya hade fuska yace “Barka dai? Wace gaisuwa ce hakan?” Hassan ya kalli Jalila ba tare da ya kara mai magans ba yace “kuyi sauri ina mota.” Ya fada tare da juyawa. Dady ya bishi da kallan takaici, ba yanda baiyi ba akan Sageer ya barshi ya cigaba da aikinsa amma yaki, ya kuma tabbatar wannam mara mutuncin ne ya hana. Shiga su Mumy sukai, Safeena gaisheshi kawai tai ta wuce, Sultan kam ko kallanshi baiyi ba ya wuce dakinsa, Dady ya kalleshi dan duk a yaransa yafi san Sultan. Mumy ta shiga dakinsu, gaba daya dakin yai kacha kacha, Dady ne ya shigo ciki ya kalleta yace “yanzu ina zaku koma?” Tace “ko ina zamu koma ai ba kada ta cewa tunda ka koremu daga gidan da yake halak dinmu.” Dady yace “ku kwashe kayanku duka dan saida gidan zanyi.” Cikin mamaki ta kalleshi tace “siyarwa?” Yace “sosai, ina zan kai katan gida haka?” Haushi ya kamata tace “dan Allah Abakar ka sanar dani menene ribarka na abinda kake aikatawa?” Yai shiru yana kallanta tace “yanzu ka tabbatar min ilimi bai ratsa kaba, sannan ka tabbatarmun kai bagidaje ne, na dauka daka wulakantamu zan ganka kana rayuwa yanda ya kamata, sai dai menene hakan? Kalleka, kalli gidanka? Sannan siyarwa zakai?” Zaiyi magana tace “basai kace komai ba, tunda har mahaifiyata ta mutu baka tako ka min gaisuwa ba, ai a tunani na ko zaman kiyayya mukai dakai kaminn gaisuwar mutuwar mahaifiyata balle, ni ai yanzu ka nunamin tabbas ko da wasa baka taba sona ba.” Ta share kwallarta tana cigaba da kwashe kayanta, zuru yai ya tsaya yana kallanta fitowa tai zata dakin Safeena dan tattara kayan Yasmeen, har ta wuceshi ta tsaya tace “Ahh Sultan zai zauna a gidan Goggo saboda makarantarsa, naga kamar ya kamata ka sani.” Ta juya zata tafi, da sauri ya fizgota yace “Goggon har gida gareta?” Tace “eh sirikanta sun siya mata.” Yace “me?” Tace “sakeni dan Allah.” Yace “amma shi Sultan din bazai zauna anan ba har ya gama?” Tace “ya zauna a ina? Gidan mutumin da bai kaunarsa bai kaunar mahaifiyarsa? Ta ina ma zai zauna a wannan gidan?” Dady ya fara hucci, fizge hannunta tai ta fita, Dady yai shiru gaba daya yama rasa abinyi. ****** Jalila kuwa tana ganin sun shiga kwaso kaya ta fito inda Hassan yake, tace “Yaya muje kaga dakinmu.” Fitowa yai ya riko hannunta yace “ahh yau zanga muhallin Baby.” Tai murmushi tace “Yaya daka dan sake hannuna kar a ganmu.” Yace “to wai ni in an ganmu menene a ciki? Ahhh dana sani London nace a nemarmana dan su nasan ko me kai ba ruwann wani dakai ko a ina ne.” Jalila tace “Lalai, wato kai abu ma kake so ka dingayi a ko ina? Oh ni yays ba kunya sam.” Zaiyi magana tace “Yaya zaka saima Sultan keke?” Yace “keke?” Ta kalleshi
🏠