NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 160 of 172

n kuwa ita kadai taje, wanda shine yau ranar bakwai, su Mumy sun shirya dan yau zasu koma can gidan, dan dama itace tadanyi rashin lafiya shiyasa basu koma da wuri ba, jiya tasa Sultan yaje ya ga gidan shida Driver dinsu wanda sun san yanzu suna tattarawa zasu sallameshi, ga gidan da nisa sosai ga kuma jarabawar Sultan ta matso, jarabawar karshe waec, Mumy tai shiru tana tunani, Jalila ta kalli Sultan tace “yakai minti nawa daga can zuwa makarantar taku?” Sultan yace “tab gidan fa a can wajen gaba da gida dubu yake, wasu sababbin gidaje agun.” Cikin mamaki Jalila tace “kai!” Safeena ta kalleta tace “da nisa sosai ko?” Jalila tace “nima bansan gun ba nadai taba wucewa sai dai gaskiya da nisa sosai.” Sultan yai ajiyar zuciya yana cijen lebensa yanda ya saba in ransa ya baci. Mumy tace “sai dai ka hakura da jarabawar, dan kaga kawunka tafiya zasuyi, dan dama mutuwar goggo ce ta tsayar dasu, ga kuma itama datai rashin lafiya, sannan a yanda suke nuna mana suma yanzu kamar sun gaji da zamanmu ne, kaga ban isa in kara daura musu wani nauyin ba.” Jalila ta kalli Yasmeen dake jikinta a kishingede sannan ta kalli Mumy, tace “ko zai zauna a gidan Goggo?” Gaba daya kallanta sukai, Jalila tai murmushi tace “ban tambayeta ba sai dai nasan Goggo bazata taba hanashi ba, mai zai hana ya zauna a can inyaso sai mu nemarmai keken hawa kawai ya dinga zuwa?” Idanun Mumy ne suka ciciko, tai shiru tana kallan Jalila, Sultan ma kallanta yake kafin yace “Akan me zaki taimakamin Jalila?” Tace “ban gane ba?” Muryarsa ta fara rawa yace “kin manta cin kashin da aka miki a gidan mu? Kin manta wahalar da Mumy, Inna, Dady da wannan Safeenar suka miki? Taya zaki........” Kunnenta ta toshe tace “ya isheni haka nan, oh ni Sultan yaushe ka fara magana haka? Sannan kome ya faru ai dane, sannan ka manta kai wanene a gareni?” Mumy batasan hawaye sun zubo mata ba sai da Safeena ta kamo hannunta, Mumy ta share kwallarta tace “Jalila nagode, ko ince Mun gode, kin nuna mana yanda ake saka sharri da alkairi, butulci da hallaci, mungode.....” Jalila tai murmushi tace “bari na kira Goggo na sanar mata inyaso sai mu fara kaishi kafin kuwuce.” Mumy tace “Jalila dan Allah wata alfarma.” Kallanta tai tace “tame?” Mumy tace “ki taimaka kima mahaifinki magana munaso mu kwashi kayan sawar mu.” Tace “Safeena ta kirashi ta fadamai ko ke mana, ai kayanku ne dole ya baku.” Mumy tai murmushin takaici tace “tun shekaran jiya muke kiranshi bai dauka ba.” Jalila ta mike tare da yin sallama saboda muryar Goggo dataji, tace “Goggona!” Ta fada tare dayin ciki, bayan ta gaisheta ne ta sanar da ita abinda ke faruwa, Goggo ta tausaya musu kafin tace menene a ciki, yazo ya zauna ai duk daya ne.” Jalila tace “Lanta ga?” Goggo tace “dama tare muke kwana da ita, shimfida takeyi a kasa, nace ta hau kan gado mu kwanta taki wai ita tafi san kwanciyar kasa, dama dakin a rufe kawai yake.” Jalila tace “shikenan ma.” Sun danyi hira kadan kafin suyi sallama, harzata fita daga dakin sai ta kira wayar Dady, yana ganin numberta ne ya dauka da sauri yace “Jalila.” Tace “Dady kana ina?” Yace “ba gaisuwa bakomai haba Jalila?” Ta daure tace “Ina wuni?” Yace “lafiya ina gida, ya akai?” Tace “zamuzo dasu Mumy su debi kayansu ne dama shine nake so naji inda kake.” Yai tsaki yace “sabodasu kika kirani? Wai Jalila baki da wayau ne? Kin manta mai mutanen nan suka miki?” Tace “sai munzo, kawai ta kashe, tare da zama akan gado tana rike da wayar.” Mikewa tai sannan tace musu ta fadamai, sannan Goggo ta amince, murna agun Mumy kamar me, Sultan kam shiru kawai yai yana kallanta, duniya kenan. Text tama Hassan tace “Yayana ka dawo?” Da yake dama ajiye tayai akan zai leka gun Abba ya dawo, ganin reply tai akan saura 2mins ya iso. Murmushi tai sannan ta kalli Mumy tace “Mumy nima tafiya zamuyi da Yaya.” Cikin mamaki Mumy ta kalleta alamar rashin fahimta, Safeena cikin zumudi tace “ina zaku? Umara?” Jalila tace “a’a zamu tafi Qatar ne munyi visa shekaranjiya amma bata fito ba tukunna.” Mumy jiki a sanyaye tace “me zakuje yi?” Tace “karatu zamu.” Sultan yace “haba? Kai congrats, kun samu admission ne?” Tace “wlh a’a tukunna, mun dai cike, sai dai dama zamu samu, ko muna can zata fito.” Safeena tai shiru tana kallanta yanzu fa da itace take wannan rayuwar?” Jalila tai murmushi tace “bansan sanda zamu tafi ba, amma daga visa ta fito nasan ba jira.” Mumy ta jinjina kai tace “masha Allah, Allah ya bada sa’a, ya karo ci gaba.” Jalila tace “ameen...” Sakon Hassan ne ya shigo, “Baby am back, ko nazo na kinkimoki?” Murmushi tai bayan ta gama karantawa sannan tace “Mumy muje.” Mumy ta mike suma suka mike suka fito, motarsa suka mufa it
🏠