NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 172

pple and coconut juice sai ki yanka ragowar kiyi fruit salad. Tashin hankali, kallanta Jalila tai, Inna tace " ki tabbatar kinayi kina kara gyara gidan, sannan kisa turaren wuta sosai, bakon dazanyi mai mahimmanci ne a garemu. Ki tabbatar kin kammala komai kafin lokacin. Ta juya ta fita, Jalila ta kara kallan kayan girki sannan ta kalli agoggon dake kitchen d'in, karfe 6:40am idanunta ne suka ciciko da kwalla yanzu ia kadai akw tunanin tayi wannan uban aiki sannan ta hada da aikin gida? Jitai ance "me kikeyi banji kin fara ba?" Lekowa tai ta ga Inna a digirgire a zaune a falon kusa da kitchen. Nan ta bude fridge ta d'auko kayan cikin da Mumy tace farfesunshi zata musu da soyayyiyar doya dakwai. Yau kam gun gajiya ba'a cewa komai a gun Jalila, dan dama tun datashiga Ss1 aka sakar mata girkin gida gaba d'aya, a da tare sukeyi da Mumy, ashe batasan training ake mata ba, data shiga Ss1 kuwa sai dai ta zauna a kitchen din tana cewa tai kaza tai kaza, wanda a yanzu indai abinci ne ko snacks ko abinsha sai dai in wanda bai fito ba, amma ba wanda ba'a sata yi ba. Haka ta shiga aiki kamar mahaukaciya, duk mai tausayi inya ganta saiya tausaya mata. ************* A hankali Ummy ta tura kofar d’akin, a kwance taganshi a kasan d’akin daga can gefen gado, yana kwance akan sallaya yana bacci, takan rasa inda zata sa kanta a koda yaushe in taganshi a kwance akasa, abinda ke damunta shine inhar bacci dare zaiyi bazaki taba ganinsa akan gado ba, sannan a kasan ma kwanciya kawai yake, amma in gari ya waye sai kiga ya kwanta akan gado. Kusa dashi ta karasa ta dauko karamin bedsheets a gefen gadonsa sannan ta lulubamai, jiki a sanyaye ta juya ta fita. Tana rufe kofar yana bude idanunsa, kofar ya kalla dan tun da ta shigo ya farka, idanunsa ne suka canza launi a hankali ya maidasu ya rufe saboda tsananin tausayin da yakeji na mahaifiyarsa. Mikewa yai ya hau kan gado yai wata kwanciya a dukunkune, a hankali idanunsa suka zubo da wasu zafaffan hawaye. Ummy tana fita ta sauka kasa, kitchen ta shiga inda Ameera da Aina’u suke girkin abincin safe. Tace “wannan jagwalgwalo har mun gaji da jiransa, sai kace wanda ake mana abincin arziki.” Ameera tace “Ummy kin dage sai munyi girki da weekend kinga kuwa kome muka dafa sai kuyi hakuri kuci.” Ummy tace “ai na gama kula dake sam bakyasan yin girki, yanzu kuwa kinjama kanki duk asabar da lahadi ke zaki dinga yin girkin safe.” Ameera tace “Shikenan Ummy sai mudingacin Indomie.” Aina tai dariya tace “Lalai Ameera, Abban zaki ba indomie?” Ummy ta juya tana murmushi, falo ta zauna sannan ta d’au waya ta kira Aunty Nana. Bayan sun gama gaisawa tace “muna nan da Aina’u munatashan hutu.” Aunty Nana tace “ ai gwara datazo dan nasan yanzu Ameera tafi kowa jin dadi.” Ummy tai murmushi. Aunty Nana tace “ Ya jikin Hassan?” Tace “dama saboda shi na kiraki” Aunty Nana tai shiru tana sauraranta. Ummy tace “ Me kike tunanin akan yi masa aure?” Aunty Nana tace “Aure? Wace irin magana kike yi Hafsa? Wa kike tunanin zai aureshi? Karfa san kanku ya muku yawa.” Ummy mamaki ya kamata tace “ban gane san kai ba? Sai kace wani mahaukaci ko mai lalura mara warkewa ko fa nakasar jiki?” Aunty Nana tace “ Ni dai dan bakwasan gaskiya ne, amma na tabbatar Hassan nada matsalar kwakwalwa, kardai ku aura masa yarinya yazo yana neman kasheta.” Mikewa Ummy tai idanunta suka canza tace “mene?” Aunty Nana tace “ Hafsa......” Kashe wayarta Ummy tai sannan tai shiru tana kara maimaita kalaman Aunty Nana a ranta. Aunty Nana irin matan nan ne da duk abinda ya fito musu a baki fada suke ba tare da sunyi nazari. Da yaya zaka fuskanci kalamansu ba. Ummy ta shiga d’aki jiki a sanyaye, Abba ya gama shiryawa yana fesa turare ta shigo, yanda yaga ta zauna akan gado yasa ya juyo yace “Lafiya?” Kallansa tai tace “ Alhaji ya zamuyi da Hassan?” Ajiye kwalbar turaren yai yace “keda Yaya Nana ce?” Kallansa tai cikin mamaki tace “ya akai ka sani?” Yace “ me yasa haryanzu bakisan kanki ba? In dai har naganki a wannan yanayi to nasan matsalar Hassan ne ke damunki, to in har naga yanayin ya hada da dan baccin rai to inba Aunty Nana ba waye? Ni dai nasan ba ni bane, sannan Sagir banaji ya taba bata miki ran da har zaki shiga cikin wani hali, ita kuwa Ameera yarinta ce a kanta.” Ummy ta kalleshi tace “jiya naji yanda kukai da Dr Ahmad, shiyasa......” Yace “kike tunanin hadashi da Aina’u?” Tai shiru, kusa da ita ya zauna yace “Hafsa!” Kallansa tai yace “ shi aure da kike gani nufine na Allah, sannan wani baya auran matar wani, Allah ne kadai yasan abinda ya shirya akan rayuwar yaran nan, mudai abinda zamumai kawai shine mu dinga mai addu’a kamar yanda muka saba.” Kai ta jinjina alamar gamsuws sannan tace “yanzu zaka wuce ne? Naga bakai break ba.” Yace “ In naje naci acan, dan nasan thnda dai gida ta
🏠