NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 159 of 172

"ka manta wahalar dakaba baiwar Allahn nan? Kasa ta rabu da iyayenta, ta rabu da 'yan uwanta, sannan kai baka bata farin ciki ba sai kunzuga mata dakai, yar data haifa baka taba tausaya mata ba, baka taba nuna mata ko kula da ita kamar yanda Uba ya kamata ya kula da dansa ba, dan Allah dady a tsawon rayuwarka mai ka taba yima baiwar Allahn nan? Wannan wani irin san.........." Kukan daya kubce mata ne yasa ta kasa magana, dady yai shiru shikansa yanzu jikinsa yayi sanyi dajin kalamanta, da sauri ya kashe wayar sannan ya kwanta rigingine a kan gado. Hassan na jin kukanta, sai dai baisan me zai ce mata ba, bakin cikin mahaifi ne wanda ba wanda ya isa cire mata shi. Idanu kawai ya runtse yanajin kukan har ransa, mikewa tai ta bude kofar tana share hawayenta, kusa dashi tazo kawai ta rungumeshi tsam, shafa mata baya ya shiga yi, ta dago ta kalleshi tace "bari nasa abincin a microwave nasan yanzu duk ya huce." Kai kawai ya daga mata ta dau abincin ta fita dan dama a plate kawai ta zubo mai. Tana sauka su Ummy na shigowa ta musu sannu da zuwa sannan tai kitchen, Ummy ta kalli Abba tace "Jalila akwai sansanyan hali, yanzu kaga wai matar data mutu fa tayima kuka haka idanta ya canza haka?! Abba yace "matar data wahalar da ita, gaskiya mu gode Allah." Nan sukai ciki suna hirarta, komawa tai sama ta taraddashi a zaune yanda tabarshi, kusa dashi taje ta zauna tace "tunanin me kake?" Yace "ba komai." Amma a ransa yace a satin nan zamu muyi visa. Haka ta zauna ta bashi abincin har ya koshi, ta bashi ruwa yasha, zata mike ya riko rigarta, kallansa tai yace "wanka nake sanyi." Cikin mamaki tace "yanzun? Ya zamuyi?" Yace " ya zakiyi kuwa tunda ke kika jimin ciwo kika karyani, haka nan zaki zo kimin." Idanunta taxaro tace " ni?" Yace "sosai." Haka ta taimaka mai ya cire kaya yasa towel itakam duk kunya ta isheta, sai rokonshi take ya bari yayi wankan gobe amma yaki, haka ta jashi sukai toilet. Bayata juya saboda kunya shikam ya sa hannu ya jawota cikin bath hub din, kallansa tai da sauri zatai magana ya saki shower gaba daya ta jike, kallansa tai sannan ta kalli hannun daya riketa dashi tace "Yaya?" Ta fada tana kallan hannunsa. Zata sake magana ya jawota tare da kai bakinshi cikin nata......... ^********** Ganin magrib ta kawo kai yasa Mumy ta kalli wayarta sannan ta kira Safeena. Da sauri Safeena ta daga tace "Mumy ina hanyya" Ahankali Mumy tace "kin dauko takardun?" Tace "eh Mumy sa'a nai Dady bayanan." Mumy ta kashe wayar tare da jinginar dakanta jikin kujera. Matar kawunta ce ta kalleta tace "Fatima ki taimaka kisa abinci abakinki." Mumy ta girgiza kai alamar a'a sannan tace "karki damu dani, ko nasa abincin ma banaji zan iya taunawa." #OneLuv💕🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *76* Safeena na shigowa ta shige daki, Mumy ta mike ta bita. Hijab dinta ta cire sannan ta mikama Mumy katuwar enveloped din dake boye a hijab dinta, Mumy ta amsa sannan ta bude, kamar yanda Inna ta fada takardar gida ne da kuma fili, sai kuma takardar bankinta wanda ke dauke da kudi da dan dama, sannan sai takardun shares dinta na company dinta.” Kurama takardun ido tai wasu zafaffan hawaye na zubo mata, kuka ne ya kwace mata tanayi tanA cewa Inna ki yafemin...” Safeena ce ta rungumeta Itama tana kuka, sun dade a haka kafin Mumy tace “in anyi uku ma sanar ma Sultan abinda ake ciki.” Safeena tace “ai Mumy inaji ma yasan abinda ke faruwa, nasan dai bai san duka ba amma na tabbatar yasan rabi daga ciki, dan ko tambaya ta dady baiyi ba.” Mumy tai shiru kafin ta share hawayenta tace “Rayuwa ce, nasan mun cuci su Jalila amma ko da wasa banida hakkin mahainfinku, dda zuciya daya nake zaune dashi....” Safeena ta share nata kwallar tace “Mumy dan Allah ki daina kuka hakanan, sannan kisa tawakalli a ranki.” Mumy tai shiru tana kallanta, kafin tace “Safeena ban taba tunanin wannan abin bazai shafeki haka ba, ban taba tunanin kece zaki zama mai lalashina ba.” Safeena tace “Mumy baki san halin dana shiga ba bayan tafiyata, da yanda gaba daya rayuwata ta nemi hargitsewa a lokaci daya, na tabbatar addu’arki ce ta kareni, tun a lokacin na shiga hankalina ganin irin abubuwan dake neman faruwa dani.” Mumy ta jawota jikinta tace “Safeena nagode sosai, Allah shine ke shiryar da bawansa na tabbatar da irin tarbiya da nuna komai dole ne ki samu da muka nuna miki shi kikai amfani dashi, da yanzu bansan abinda zai faru ba, Allah mungode ma.” Haka suka kwana cikin wani irin yanayi da su kadai sukasan irinshi, dan Mumy kam bata ko rintsa ba, dan tana matukar san Abakar, ta kuma yarda dashi dari bisa dari... *********** Yau kwana goma sha hudu kenan da mutuwar Inna, zuwan Jalila uku gidan gaisuwa, a duk sanda zata je kuma sai Hassan ya hada kayan abinci sun kai, sau biyu sukaje da Goggo daya
🏠