NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 158 of 172

ncikeshi hakan yasa dady ya fadi kasa, board director din ya nunashi da yatsa yace "kai wanene? Mtsw ni zaka maida karamin mutum? Ko ni nace ma ka kwaso kudi dayawa? Ni dai nasan cema nai kawai ka kawo kudi a basu, ko nace ma ga yawon kudin da zaka ciro? Shashashan banza kawai, har kai ka isa ka maidani karamin mutum? Ashe da babban kuskure na kusa tafkawa. Yai tsaki sannan ya koma cikin gida, Dady ya mike da kyar ya shiga mota yai shiru, can ya dauko wayarsa ya duba dan yaga balance dinshi. Dubu dari shida ya gani kwata kwata, dan dama miliyan bakwai ne dashi a ciki, wai saboda ya birgesu sai yabada miliyan shida wai a raba musu dan su zabeshi, sannan ya kama katan hotel inda yake ciki, tsaki yai kafin ya sa hannunsa a saman kansa, yanzu gashi ance dole ya kawo takardar ajiye aikinsa gobe, nausan sityarin motar yai kafin yai wata ajiyar zuciya, tun farko ya riga ya bata kansa agaban mijin Jalila yazu gashinan hanyar daya bi bata billemai ba. Kwafa yai kafin yaja mota yai gaba, hotel dinsa ya shiga ya wuce ya kwanta yana lissafi, can ya dau waya ya kira Jalila, dolene ya kira ta ya lallabata ta samu tasa mijinta ko aikinsa ne a barshi dashi in har baza'a bashi matsayinsa ba. Hassan na kwance yana jiranta ta kawo mai abinci yaji wayarta na kara, ganin number ne yasa ya ko daukan wayar, kiran bai dade da katsewa ba ta turo kofar, da sauri ya gyara kwanciyarsa. Ta shigo ta ajiye abincin ta matso inda yake, tace "yaya tashi kaci abincin." Kallanta yai tare da kara ragwancewa yace "Jalila hannuna kamar zai cire." A tsorace tace "nikam yaya ka taimakamin muje asibiti zanba Ummy hakuri." Yace "dagani naci abinci." Dagashi tai sannan ta kalleshi rike da spoon din, dan a hannun dama ne ta ina zaici? Kallanta yai sannan ya bude bakinsa, haka ta debo zata samai wayarta tai kara, kallan wayar tai sannan tasamai sannan ta matso gefensa tasa hannu ta dauko wayar, dauka tai tare da yin sallama. Jalila! Sunanta da aka kirane yasa gabanta faduwa dan ta gane mai muryar, dady yace "Jalila magana zamuyi in kina kusa da mijinki dan Allah kidan matsa." Jalila ta kalli Hassan wanda shima kallanta yakeyi, tace "me zakacemin da har sai na matsa?" Dady yace "Jalila wai yaushe kika zama mai musu ne? Nine mahaifinki wanda fa duk duniya baki da kamarshi." Shiru tai sannan ta ajiye abincin a side bed sannan tamike, Hassan kam bai mata magana ba yana kallo ta fita falo ta rufo kofar. Jalila tace "inajinka yanzu ba kowa, Dady yadan ja numfashi yace "Jalila tunani nakeyi, mai zai hana in dawo da mahaifiyarki? Na tabbatar ke kanki babban burinki ne hakan, yanzu tunda nasamu gurin zamazan kula da ita yandaya dace, ke kanki kinsan bawai santa bane banayi, ba dai yanda zanyi ne." Jalila tai Shiru tanajin wannan sabon salon wulakancin, cikin takaici taji Yana cewa "Jalila kinsan abinda mijinki yamin kuwa? Kinsan wulakancin da sukamin shida kaninsa? Amatsayina na mahaifinki ai banaji ko mai nai ya kamata yaran nan yaci mutuncina, sai dai bayansa zanyi nima nasan ban kyauta ba dana nausheshi, dan Allag Jalila ki bashi hakuri kinji? Ni mahaifinkine ya kamata yasan darajata kinji?" Bakin Hassan ta tuno a ranar dama jikinta ya bata Dady ne sai dai batasan zargi shiyasa. Dady zaiyi magana tace "kaje gaisuwar Inna?" Yace "wani gaisuwa bayan na rabu da matar sannan ko kin manta ne? Yanzu nake miki zancen komo da mamanki." Jalila cikin takaici tace "Dan Allah dady kai wani irin mutum ne? Wanda zuciyarsa da kansa kawai ya sani? Taya mutum magidanci mai iyalai kamarka za'ace bakasan komai ba sai kanka? Baka tausayin mu? Baka tunanin yanda muke kallanka? In har ni da Goggo bazaka faranta mana ba taya za'ace wadanda ka moresu a iya tsawon rayuwarkasuma bazakaji tausayinsu ka faranta musu ba? Wannan wani irin tsabar san kai ne? Sannan maganar Goggo ma ka dainata dan alama ce ta kaidinba mutumin da zai iya rike wani bane, kanka kawai zaka iya rikewa, sai ka cigaba da zama kai kadai har karshen rayuwarka dauke da alhakin 'ya'yanka wadanda Allah ya daura maka hakkinsu, sannan magana ta karshe, Karkayi tunanin Goggo har yanzu a wacce ka sani ne, yanzu tanada gatan da ya wuce tunaninka, dan tanada gidan zama sannan bata rasa komai na duniya ba, insha Allahu kuma Allah zai bata wani mijin ta aura, hakan yasa dama nake neman taimako a gurinka akan in da auranka a kanta ka taimaka ka sauwake mata, ko dan........." "Jalila ni Abubakar kike fadawa haka? Har yaushe aka haifeki da zaki nemi yimin wa'azi?" Jalila ta maida numfashi tace "ba wa'azi nake ma ba rokonka nake." Roko? A banza? Inhar kinasan na saki mahaifiyarki sai kin sa mijinki ya barmin aikina ya kuma barmin company din dana sha wahala gun kula dashi." Mamaki ya kara kama Jalila idanunta suka ciciko cikin takaici tace "Dady yaushe ka zama haka? Nasan dama can kanada san kanka sai dai bansan abin naka yakai haka ba? Dady wace irin rayuwa ka daura kanka a ciki?" Dady yai shiru, Jalila tana kuka tace
🏠