NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 156 of 172

bin kuka tace "Jalila Allah yayima Inna rasuwa." Gaban Jalila ne ya fadi, ta mike tsaye daga jikinshi jikinta duk ya fara rawa tace "Inalilahi wa Ina Ilaihi Raji'un, yaushe?" Safeena tana kuka tace "dazun nan, yanzu muna hanyar kaita gida ne za'a mata wanka." Jalila hawaye ne ya zubo mata tace "bari nima ganinan zuwa." Safeena tace "Gidan kawu zamu kaita, acan za'ayi zaman makoki, dan Dady ya koremu." Jalila jitai kanta yayi dum kafin tace "ya koreku kamar ya?" Safeena tana kuka tace " sai kinzo." Dan batasan me zatace ba acikin wannan yanayin, gaba daya Jalila ta juyo tace "Yaya? Inna ta rasu." Hassan wanda tundayaji yanda take magana jikinshi ya bashi Inna ce ya matso ya rike hannunta wanda keta rawa yace " Jalilah?" Kallansa tai tana zare ido tace "yaya ina Dady yake?" Yace "wallahi bansani ba, menene?" Tace "Yaya meke damun Dady? Taya zai kori mutane daga gidansu?" Hassan yace " bangane kora ba?" Tace "nima bansani ba amma kome ya faru wannan abinda dan adam ya kamata ya aikata ne? Gidansu ne fa?" Ta fada a rikice, Hassan yace "yanzu kizo muje in kaiki gidan gaisuwa komai ya biyo daga baya, sannan mutanen nan sumafa sun cutar dake." Hawaye ya sake zubo mata tace "sun cutar dani amma ba kamar shi wanda ya haifeni ba, ya banzatar dani da mahaifiyata duk abinda ya faru damu ba ruwansa........." Rungumentan dayai ne yasa tai shiru, yace "ya isa haka nan, ki kira Goggo ki sanar mata sai mu biyo mu dauketa." Ta daga kai alamat to. Nan ta kira ta sanar mata, Hankalin Goggo ya tsahi tsantsa dan gaba daya ma kasa magana tai, Jalila ta koma ta shirya suka fito suka shiga mota, gaba daya haryanzu hankalinta ya kasa kwanciya dajin abubuwan nan biyu. Gidan Goggo suka wuce suka daukota suka fito, Hassan yace "kamar ya kamata asai wani abun ko?" Jalila tace "abu kamar me?" Yace "bari na tambayi Abba." Shiru tai ya kira Abba sukai magana, itakam sai cewa take "Goggo nikam dama Inna batada lfy ne? Ni gaba daya na kasa gane abinda ke........" Tabota da Hassan yai ne yasa ta kalleshi, magana yai mara sauti yace "Karki kauce hanya." Shiru tai itakam gaba daya.... Goggo kam dama tundaga gaisuwa batasake magana ba, gaba daya mutuwar tazo mata a ba zata. ********** Kallan kansa yai a madubi "me ya kawoshi nan?" Hannu yasa yana shafa kirjinsa yace "Sageer da alama ziyara zaka gidan Aunty Nana." Wata zuciyar tace "kaine kake zuwa gidan haka kawai?" Can yai sauri ya kara cewa "ai yanzu haka na koma." Kallan layin da yake yai yace "ai dubata zanyi a musulunci kuma ziyarar mara lafiya akwai lada mai yawan gaske." Kara tada motar yai yana dan hango gidan shikam yaje yace me? Inaa bada shi ba, gaba yai kadan ya juya kan motar, yana neman yin gaba mai adaidaiti na parking, fitowa tai daga ciki sanye da kayan makaranta na health school, kudi ta mikamai ta juya, hartayi gaba sai kuma ta tsaya ta juyo ta kalli motar, girman idanta ta rage dan ganin mutumin dake ciki. Kunya ta kara kama Sageer ya daure ya fito tare da dan daga mata hannu kadan, yana yake. Maimuna ta dan fara takowa shima yana takowa, sai da suka matso kusa da juna sannan tace "Ina yini?" Yadan sosa keya kadan yace "lafiya, nazo wucewa ne sai na hango gidanku, naji kamar ya kamata na tambayi jikinki." Kallansa tai dan taga sanda ake juya motar tana hanya, tace "na gane shine kake neman juyawa?" Yace "hmm daga bayane nai tunani kamar kuma na tafi, kar kiji abin banbarakwai." Murmushi tai tace "yanzu fa?" "Yanzu kam tunda naga kingani naga kuma kamar dai kamar dai." Tace "to yanzu nagode zance?" "Ba nagode kadai ba kinga saboda kar asani tunani dawowa inaji number kawai za'a bani yanda zan kira." Batai mamaki ba, dan yanda fuskarsa take da idanunsa yasa ta fahimceshi, tadai gane ta baya yakesan biyo mata. Murmushi tai kafin ta mikamai hannunta, wayarsa yamika mata yana murmushi. Amsa tai ta saka mai, nan suka danyi hira kadan kafin ta shiga ciki. Tana shiga ya washe baki yace "ahhh Malam Sageer da alama kaima......" ************* Kayan abincin da ake ta shigowa dashi ne yasa mutanen dake zaune suka mike suna cewa "daga ina??" Jalila ce ta shigo itada Goggo bayan masu ajiye abincin sun ajiye, Safeena na hango Jalila ta mike da gudu tazo ta rungumeta tare da fashewa da kuka.... Itama Jalila hawaye ne ya zubo mata, Yasmeen dake kwance jikin Mumy ce itama ta mike da gudu ta taho gun Jalila. Hawaye ne ya kara zuboma Mumy aranta tsantsar nadama ce fal, Goggo Safeena ta kalla tana kuka tace "Goggo sannu da zuwa." Dan da bata ganeta ba saboda canzawar datai. Mumy ta mike tacema "Goggo tazo ta zauna." Mutanen gun kuwa mamakin kayan da aka shigo dashi da kuma sunan Jalilah da suka jine yasa kuwa ya kunshe gulmar dake ransa, dan tabbas sunsan sunan wasu kuma sunsanta. (Balle dama a wannan lokacin da gidan mutuwa ya zama gidan gulma, gidan sa ido, gidan h
🏠